Connect with us

RA'AYINMU

Annobar Shaye-Shaye A Tsakankanin Matasa

Published

on


A farkon wannan watan ne kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta baci a kan matsalar yawaitan shaye-shayen kayan maye a cikin kasarnan. Sun kuma yanke wannan shawarar ne, a bisa ganin yadda matsalar ta shaye-shayen kayan mayen ke ta kara yaduwa a tsakanin matasa, musamman ma a nan Arewacin kasar da ma kasar bakidayanta.

Gwamnonin na Arewa, sun yi wannan kiran ga gwamnatin na tarayya ne, jim kadan da fitowarsu daga wani taro da suka yi a Kaduna, inda suka nu na matukar damuwarsu a kan yadda matsalar ta shaye-shayen kayan mayen ke kara tambatsa tana zama tamkar wani abin ado ga matasan duk da irin illa da kuma cutuka gami da nakasan da kayan mayen ke haddasa wa matasan, lamarin sai kara tabarbara yake yi a tsakanin matasan, duk da matakan da gwamnatocin yankin ke dauka na dakile matsalar shaye-shayen.

Gwamnonin sun nu na matukar damuwarsu da ganin yadda tu’ammuli da muggan kwayoyin da matasan ke yi yake saurin lalata rayuwar matasan bakidayanta. Kwankwadar ababen sa maye kamar su, ‘amphetamine’ da sauran ababen da ke haddasa jirkitar da hankali idan an sha su ba bisa ka’ida ba, na narcotic, irin su, codeine, tramadol da ire-iren su, hanya ce kai tsaye mai saurin lalata hanta, sanya hauhawan jini, ciwon daji da sauran cututtukan jiki wadanda ke haddasa gaggautowan mutuwa.

Rahotannin da aka samu a wannan shekarar kadai, masu nu ni da yadda matasa suka rika shekawa lahira tun da kuruciyarsu a sabili da matsalar ta shaye-shayen kayan mayen abin akwai ban tsoro saboda yawaitan su. Kwanan baya kadan aka shelanta mutuwar wani matashin da ya sha kayan mayen har su ka yi ma shi karo ya kuma sheka lahira tun da sauran kwanansa a garin Abraka, da ke {aramar Hukumar Ethiope ta gabas, a Jihar Delta. A dai Jihar ta Delta, wani matashi dan makarantar Sakandare ta, ‘Army Day Secondary School,’ da ke garin, Effurun, ta {aramar Hukumar Ubwie, shi ma hakanan kawai aka gan shi yana tangal-tangal a cikin aji, nan take kuma sai aka ga ya fadi kasa matacce ba rai. Ko da aka kai gawarsa dakin bincike, sai aka taras ya kwashi Tramadol ne har ya yi ma shi karo ya mutu.

Mista Akindele Akingbade, Kwamandan Hukumar yaki da shan muggan kwayoyi ta Jihar Abiya, a kwanakin baya ne ya shelanta mutuwar wani dalibin karamar Sakandare a {aramar Hukumar Ohafia, ta Jihar ta Abiya, wanda shi ma ya sheka lahira babu shiri bayan da ya hadiyi kwayar ta tramadol har guda 10, wanda aka ce wai ya sha ne domin ya sami karin kwazo a gasar wasanni da ake yi a makarantar na su.

Ainihin ita wannan kwaya ta, tramadol, an kirkirota ne domin ta kasance maganin da ke rage radadin ciwo ko kuma ya rage zafin jikin da ya tsananta. Amma a sabanin hakan, sai matasan suka samo wata hanyar yin amfani da shi ta daban wacce ta kauce wa ka’idar amfani da shi din, ta hanyar shan sa da yawa fiye da ka’ida. Matasan, sun ma yi ikirarin cewa wai shan kwayar ba bisa ka’ida ba, yana kara ma su karfi, musamman a wajen jima’i. Duk da cewa, akwai dokoki a kasarnan wadanda suka yi hani da yin tu’ammali da shigen wadannan kwayoyin kamar kwayar ta tramadol, da amphetamine, sai dai abin da aka rasa shi ne, tabbatar da yin aiki da dokokin.

Kasantuwan yanda ake yawan shan ababen sa mayen, a yanzun haka, diloli da masu sayar da kayan mayen sun zama hanshakan ‘yan kasuwa. A wannan satin kadai, hukumar ta hana yin tu’ammali da kayan mayen, NDLEA, ta bayyana cewa, ta kwace kwayoyin na tramadol har milyan 159 a tashar jiragen ruwa ta Apapa, da ke Legas. Daraktan hukumar ne ta, NDLEA,  mai gudanar da bincike, Mista Femi Oluruntoba, ya bayyana hakan, a wani zama na musamman da Majalisar Dattawa ta gayyace shi domin ya yi bayani kan illoli da kuma rawar da hukumar na shi ke takawa wajen hana shan muggan kwayoyin. Ya ma kara da bayyana cewa, a kwanan nan a Kano kadai, hukumar na shi ta lalata sama da Tan 50 na kwayar ta tramadol. Ya kuma yi nu ni da cewa, baya ga kwayar ta tramadol, akwai sama da ababen sa maye 31 da ake hadiya ko kwankwada domin jirkitar da hankali tun daga shekarar 2016.

Matsalolin kan iyakan kasarmu, da kuma zafafan dokokin da suka haramtawa hukumar lura da lafiyar abinci da magunguna, NAFDAC, gudanar da ayyukansu a tashoshin jiragen ruwan kasarnan, sun kara taimakawa wajen yaduwar haramtattun kayan maye a cikin kasarnan. Wani bincike da kamfanin nan na, NoI Polls Limited, ya gudanar a ranar 1 ga watan Yuli 2013, ya yi nu ni da yadda karuwan tu’ammuli da kayan mayen a cikin kasarnan ke kara janyo mana mugun talauci da rashin aikin yi.

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a wani zama na musamman da Majalisar ta Dattawa ta yi kan matsalar shaye-shayen kayan mayen, ya yi nu ni da cewa, shaye-shayen, su ke haddasa yawaitan ayyukan masha’a, kamar su, fashi da makami, garkuwa da mutane, ta’addanci da saura ayyukan laifuka makamantan su, da suke barazana da sha’anin tsaro na cikin kasarnan. Sannan kuma abin takaicin, in ji Shugaban Majalisar ta Dattawa, da yawa daga cikin matasanmu, wadanda ake sa ran su zama shugabannin gobe duk sun rungumi wannan muguwar dabi’ar ta shaye-shayen na kayan maye. Wanda hakan a cewar shi, barazana ne ga lafiyarsu da rayuwar su ma bakidayanta, sannan kuma barazana ce ga iyalansu, don haka tilas ne mu tashi tsaye haikan wajen yakar wannan dabi’ar ta shaye-shayen na kayan maye, in ji Saraki.

Matsalar ta shaye-shayen kayan maye a tsakanin matasan namu, da suka hada da, shakan sholisho da dangogin ta, da kuma ababen da ake sha daban-daban, da suka hada da tabar wiwi, shakan masai da makamantan su, wadanda suka zama ruwan dare musamman a nan arewacin Nijeriya.

{warraru sun tabbatar da cewa, iyaye suna da mahimmiyar rawar da ya kamata su taka wajen duba halayyar ‘ya’yayen na su dangane da matsalar ta shaye-shaye. Kan haka, suka bayar da shawarar cewa, ya kamata iyaye su rika duba ‘ya’yayen na su, musamman wadanda suka fara tasowa, ta hanyar duba idanuwansu a kai a kai, numfashinsu da ma yanayin warin jikinsu, gami da lura sosai a kan yanayin dabi’o’in su, na maganganu, huldansu da kuma yadda halayyarsu ke canzawa. Da zaran an lura da wani bakon abu kan wadanda muka lissafta din nan, sai a gaggauta daukan mataki.

Dangane da hukuma kuma, kungiyar masu hada magunguna ta kasa, (PSN), ta kawo shawarar da a sanya dokar rubuta magunguna a kasarnan, wacce za ta baiwa kungiyar ta PSN, damar sanin ko wa da wane ne ke yin abu kaza a kowane waje, da ya shafi bayar da magungunan. Sannan kuma gwamnonin arewa, sun bayar da shawarar dukkanin gwamnatocin Jihohi su kafa wani kwamiti na musamman da zai tabbatar da ana aiki da dokokin hana safara da shan kayan mayen, a karkashin ko dai mataimakin gwamna ko kuma Sakataren Jiha.

Sun kuma bukaci Ma’aikatun kula da harkokin mata da matasa da su kara kaimi wajen shirye-shiryen wayar da kai kan hadarin da ke tattare da shan kayan mayen. A nan arewa kuma, gwamnonin sun shawarta kafa wata doka ta musamman da za ta yaki safara da shan kayan mayen a yankin na su na arewa.


Advertisement
Click to comment

labarai