Connect with us

ADABI

Marubuci Da Jigo

Published

on


A ranar Lahadin karshen makon da ya gabata ne 25/03/2018, kungiyar marubutan Hausa zalla ta HAUSA AUTHORS FORUM ta gabatar da taronta na al’ada da ta saba a ranar Lahadin karshen watan mai jan kunne, a KURNA SPECIAL PRIMARY dake kan titin Katsina, Kano. Taron dai ya tara manyan marubuta da suke ‘ya’yan kungiyar, da shugabanni na da da kuma na yanzu.

Makasudin yin taron dai shi ne, don tattauna lamuran da suka shafi kungiyar, tsefe littattafan ‘ya’yan kungiyar da kuma karawa juna sani. To a wannan watan Malam Lawan Muhammad Prp, marubucin littafin GIDAN HAYA, KWANAN GIDA, BAKIN DARE da dai sauransu, shi ne ya gabatar da makala mai taken MARUBUCI DA JIGO makalar da ta sha yabo saboda tarin ma’anoninta da yadda aka fayyace komai daki-daki, kuma ta sha ragargaza ta wani bangaren.

Ga dai makalar tsaraba ga mabiya wannan shafi da wakilin ADABI A YAU ya zo mana da ita. A sha karatu lafiya.

 

Kafin mu yi magana akan jigo yana da kyau mu fara sanin wane ne Marubuci.

Marubuci shi ne mutumin dake zama ya kirkiri labari ya rubuta da nufin fadakarwa, nishadantarwa, gami da ilmantarwa akan abin da ya shafi rayuwar yau da kullum. Haka kuma ana kallon marubutan al’amuran yau da kullum a jarida ko mujalla a matsayin Marubuta.

Rabe-raben Marubuta

– Marubutan litattafan addini (na shari’a)

– Marubutan Alkur’ani

– Marubutan Kimiyya

– Marubutan kirkira

Da duk wani marubucin wani abu da ya shafi rayuwamu ta zahiri. Duka wadannan ana yi musu kallon Marubuta.

A takaice dai duk wani mutum da zai yi rubutu ya yada a cikin al’umma don amfanin al’ummar sunansa Marubuci.

Wannan shi ne ma’anar Marubuci a takaice.

Amma za mu tattauna ne akan rubutun kirkira, sauran nau’ikan rubuce-rubucen kuwa bincike da ilmi ne ke samar da su. Duk da cewa shi ma rubutun kirkirar na bukatar bincike.

 

Yaya Ake Samar Da kirkirarren Labari?

Ana samar da labari ne ta hanyar tunani akan rayuwar wasu mutane da ake son yin rubutu a kansu, ko kuma yin duba da sashen wasu mutane a rayuwarmu ta zahiri wanki rayuwarsu a mayar da ita labari cikin sauki. Irin wannan labarin shi ake cewa ‘true life story’ (wato labarin da ya faru a gaske) duk da masana sun tabbatar babu ta yadda za a yi ka dauki labarin gaskiya ba tare da ka cudanya shi da tunaninka (na kirkira) ba. Irin wannan karin gishiri shi ke kara armasa labari, ta yadda za a samu rike mai karatu ta hanyar kyautata rukunan gina labari, wato Jigo, Salo da Sarrafa harshe, Zubi da tsari.

Wadannan rukunan suna da matukar muhimmanci wajen samar da labari, ta yadda idan babu daya a cikinsu ko kuma ba a yi shi yadda ya kamata ba labarin zai zama lami (miyar da ba gishiri ko shayin da ba sukari).

Akwai muhimman abubuwa da suke jinginuwa da wadannan rukunan, amma dai za mu fara daukar wadannan rukunan daya bayan daya domin saukakawa ga masu bibiyar filin.

 

Jigo

Jigo shi ne gundarin abin da labari ya kunsa, kuma shi ne tushen gina kowanne labari. Duk labarin da ba shi da jigo aka ce za a samar da shi, to kamar a yi gini ne babu tushe (foundation).

Dole ne kowanne labari ya samu jigo kafin rubuta shi.

 

Misalan Jigo:

Jigo yana da yawa, kuma ya danganta da yadda Marubucin ya shirya rubuta labarin ko aka sa shi ya rubuta.

Misali, akwai jigon sata, daukar fansa, karuwanci, talauci, tattalin arziki, jarumtaka, fashi, zamba cikin aminci, soyayya, kiyayya, zaman banza, da sauransu.

Jigo yakan kunshi abu mai kyau da mummuna. Misali, a labarin da ya kunshi karuwanci ko sata ko fashi da makami ko zamba cikin aminci. Marubucin zai nuna hanyoyin da masu wadannan harkoki ke rayuwarsu kafin a karshe ya nuna yadda suka kare ba da kyau ba, wato dai Marubuci zai nuna illar wadannan abubuwa a karshen labarinsa.

Misali, littafin ‘’Yar tsana’ na Malam Ibrahim Sheme ya nuna illar karuwanci ne, yayin da littafin ‘Karshen alewa kasa’ yake nuna illar daukar fansa ta mummunar hanya.

 

Ire-Iren Jigo

Jigo ya rabu iri biyu kuma ana samun su a kusan kowanne labari.

Su ne, karamin jigo da babban jigo.

Babban jigo shi ne abin da aka gina labarin a kansa, wanda kai tsaye ya shafi babban tauraron labarin, misali, Zainab (Asabe) a littafin ‘’ Yar tsana’ da kuma Mailoma a littafin ‘Karshen Alewa Kasa’

Karamin jigo kuwa yana shafar kananan taurarin labarin walau kai tsaye ko kuma a hikimance.

 

Jigo Tahakiki Da Jigo Jimla

Dukkanin wadannan jigogi guda biyu suna jinginuwa i zuwa sunan labari. Ma’ana daga sunan labarin za a fahimci jigo tah’ki’ki ne ko jigo jimla.

Shi jigo tah’ki’ki shi ne sunan labarin da ba za a taba gane me labarin ya kunsa ba (kai tsaye) daga jin sunansa, har sai mai karatu ya karanta labarin gaba daya.

Misalin irin wannan labari shi ne, Zuciya Da Kwanji na Maimuna Idris Sani Beli. Mafi yawan sunan labari mai kunshe da jigo tah’ki’ki kalmominsa ba su da tsawo kamar na jigo jimla, wato wata ‘yar kalma ce ko guntayen kalmomi da aka kirkiri jigon labarin da ita.

Jigo Jimla kuma shi ne sunan labarin da daga jin sa mai karatu zai gane ina ya dosa.

Misali, littafin Tsallake Rijiya Da Baya na Jamilu Haruna Jibeka.

Mafi yawan jigo jimla an fi amfani da karin magana ko kirari ko suna wajen gina shi.

Misalin masu kirari ko suna:

Sihirtacce – Bala Anas Babinlata

Kulu – Bala Anas Babinlata

Rayya – Kabiru Yusuf Fagge

In Da So Da Kauna – Ado Ahmad Gidan Dabino

Tarzoma – Aminu Ladan Abubakar (Ala)

Da sauransu.

Misalin masu karin magana:

– Sara Da Sassaka… – Bala Anas Babinlata

– Idan Bera Da Sata… – Dan azumi Baba Cediyar ‘Yan Gurasa

– Dan Kuka… – Rabi’at Adamu Shitu

– Karshen Alewa Kasa – Bature Gagare

Da sauransu.

An karanta wannan takarda a taron Marubuta na kungiyar marubuta litattafan Hausa ta Hausa Authors Forum (HAF) ranar Lahadi 25 ga watan Maris, 2018.


Advertisement
Click to comment

labarai