Connect with us

BIDIYO

Dutsen Dala Da Na Gwaron Dutse Ma Film Village Ne  –Shehu Kano

Published

on


SHEHU HASSAN KANO na daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood na farko-farko kuma jarumi ne wanda duniyar finafinan Hausa ta yarda da kwarewarsa tunda daga wancan lokaci har zuwa wannan zamani. Masu bibiyar tarihin masana’antar shirin finafinan Hausa sun ce, Shehu Kano ya fi kowane jarumi karko a Kannywood, saboda shi kadai ne a cikin mashahuran jaruman Hausa wanda bai taba shirya kansa fim ba, amma duk da haka ba a taba daina yi da shi ba, saboda tsabar kwarewarsa. To, amma duk da wannan nasara da ya samu, shi a wajensa ya na da sauran tafiya. To, da ma haka hazikan mutane su ke kasancewa; wato kullum a tsaye su ke cak!

Wakiliyar LEADERSHIP A YAU LAHADI, BILKISU YUSUF ALI, ta samu zanta wa da wannan kwararren jarumi, inda ya tabo batutuwa da dama ciki har da batun badakalar Alkaryar Finafinai da gwamnatin tarayya ta taba yunkurin yi a jihar Kano. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Mene ne tarihin rayuwarka?

An haife ni a 1967 a unguwar Fagge. Bayan karatu da na yi na makarantar allo an saka ni a makarantar Islamiyya Haido Islamiyya. Na yi makarantar Firamare ta Fagge daga nan na tafi makarantar sakandire ta Gwammaja 2 na kammala a shekarar 1986. Na yi koyarwar shekara daya daga nan na tafi makarantar share fagen shiga jami’a CAS inda na yi remedial studies daga nan na kama aiki da kamfanin Dantata Organization daga nan na fara aiki da ministry of local gobernment ( ma’aikatar kananan hukumomi) inda nake  tare da su har yanzu. Na yi kungiyoyi da dama ciki akwai kungiyar sukawut inda na taka mukamai har na kai babban mukami a jaha a wancan lokacin. Ina da aure kuma da yara.

 

Yaushe ka fara wasan kwaikwayo?

Ni tun tasowata na ke wasan kwaikwayo tun Ina makarantar firamare har lokacin da na ke aiki da ma’aikatar kananan hukumomi Ina hadawa da wasannin kwaikwayo na dabe tunda akwai kungiyoyi daban-daban wadanda mu ka yi tun kama daga matsayi na unguwa har aka zo ‘home’ bidiyo.

 

Me ya ja ra’ayinka har ka fara yin wasan kwaikwayo?

Wannan yana da nasaba da kallo, domin lokacin da mu ke firamare akwai wani shiri da ake yi a gidan talabijin na kasa NTA akwai kakanni kamar yadda ni nake kallonsu a wannan harkar misali a Kaduna akwai su Alhaji Kasimu Yaro anan Kano akwai irin su Danhaki a Sokoto irin su Baba Soja Bauchi irin su Gaude da dai sauransu.ire-iren wasanninsu yana ba ni sha’awa sai nake da burin da na girma ni ma wasan kwaikwayon zan yi.Wannan sai ya sa daga firamare in aka kai mu filin maraba da yara na NTA ni ba wani abin da na fi so irin sashen da za a ce mu yi wasan kwaikwayo daga haka aka fara har zuwa inda ake a yau.

 

Ya ka ji a ranka lokacin da ka fara wasan kwaikwayo?

Har yanzu Ina jin ban kai gaci ba, saboda har yanzu Ina da buri, amma dai Ina jin mafarkina ya na ta tabbata, don a farkon lokacin da mu ka fara ba a daukar wasan kwaikwayo, sai ranar Asabar da Lahadi, saboda ma’aikata kuma kyauta mu ke yi mu. Mu ke ma biya, amma yanzu alhamdilillah a cikin irin cikar burin abin ya zama sana’a ingantacciya.

 

Ya ka ke hada ayyuka guda biyu; aikin fim da aikinka na gwamnati?

To, ba yadda za a yi sai na je ayyukan guda biyu. Don haka sai muke yin tsari tunda su masu shirya fim din su na la’akari da irina; sai su raba abin kashi uku; mu mu na yin namu daga rana zuwa dare; in kuma za a bar gari ne mu na neman izini wajen aikinmu in an yarda mu je.

 

Wacce irin gudunmawa masana’antar ke bayarwa?

Gudunmawar ai ba za ta musaltu ba. Amma ana samun wannan gudmmawar in har mai kallon fim din yana da ilimin kallon fim din. Don haka ana gane gudunmawar in har ka cire wani bangaranci ka kalla da zuciya daya. Amma fim ya taba duk bangarorin rayuwa amma wasu daga talla suke farma ‘yan fim ba ma za su tsaya su kalli fim din ba. Fim ya tabo rayuwa gaba dayanta addini kamar wani fim wani gari wanda jigonsa rabon gado a muslunci. Ana tabo al’ada da zamantakewa da tattalin arziki. Akwai fim din Sandar Kiwo sai da wasu Turawa, ya da kanwa, suka musulunta, saboda an yi shi ne kan ’yancin mata a Musulunci. A fim din sai suka lura hoton da aka ba su na yadda mata suke a baya a Musulunci da suka kalli fim din sai suka lura farfaganda ce ashe. Ire-iren wannan darasin ba  su da adadi; ga su nan birjik kan darussan fina-finai.

 

Ya a ka fara gwagwarmayar kungiya?

A 1984 akwai kungiya da muka kafa a Fagge sunan kungiyar Fagge Dramatic Society har aka zo aka yi fagge so dangi dramatic society ko ma a lokacin da muke tamun akwai kungiyoyi da muke kallonsu iyayen tamu ce kamar anan Kano an yi kungiya kwaya daya wadda ita ta haifi tumbin giwa ta haifar da kungiyar Dabo ta haifar da kungiyar tauraruwa ta haifar da jan zaki wadannan kungiyoyi an yi su ne karkashin Kano State art council wannan su suka ja ragamar zuwa gidan talabijin na ctb inda aka din ga yin wata drama gani ga wane inda ake bin yan kungiyoyi suna taka rawa. Haka marigayi malam Abdullahi Sani Makarantar lungu yana gabatar da wani wasan kwaikwayo Duniyar nan tamu suma sun din ga dauko ‘yan kungiyoyin can ana yi da su wanda ni ma ina ciki. A lokacin kishi ne ya kai mu don kowa ki ka gani yana taka wata rawa a kungiya da aljihunsa yake yin ta.

 

Wanne tasiri kungiya ta yi ma ka?

Tasirin kungiya da ta yi min shi ne wanda ake kallo a shekarar 1999 aka kafa kungiyar Kanywood lokacin ba Kanywood ake kiranta ba, an ace mata Kano State Producers Association wadannan daraktocin su suka hadu suka ce za su fara yin fim a kaset, don suna ganin tasirin abin da suka koya a kungiyoyi zai fito a ciki mutane za su amfana. A lokacin samari da dama sun sami aiki da a dabe kawai ake yi amma yanzu dole a nemi mai daukar hoto dole a sami mai kwalliya ana bukatar wanda zai kawo kayan saw a da direba mai dafa abinci da sauransu. Wannan ta sa sai aka ga wadannan mutane da ke cikin wadannan kungiyoyi wa zai dauki wannan layi da wancan sai aka karkasa. Abin sai ya tasirantu ya koma sana’a.A kungiyoyin nan mun sami ilimi hatta a labarai a cikinmu akwai malaman islamiyya da za su zo su kawo wata kissa ko tarihi a zauna a yi bitarsa a mayar wasan kwaikwayo don jama’a su amfana a lokacin wannan kungiyoyi makaranta ce babba nan z aka goge tun kana yi  da sigar koyo. Su kuma na yanzu da suka shigo bas u sami wannan horon ba  sai abin ya zama da nakasu saboda ba gogewa. Shi ya kai ga har a dauki fina-finan indiya a wanka.

 

Ana kuka da finafinai marasa inganci a yau. Ina matsalar ta ke?

Ai laifin masu kallo ne ya haifar da wadannan. A yau mutum zai yi fim mai inganci ya shiga kasuwa sai a kyale a ki saye, amma idan fim din da aka kwafi Indiya ya shiga kasuwa sai a yi rububinsa ya za a yi wanda ya yi marar ingancin zai fahimci abu ya yi marar kyau?  Amma a ‘yan shekarun nan an sami ci gaba inda ake ta karatu ake ta tarurrukan sanin makamar aiki a yanzu su da kansu masu irin wannan halin da suke wankar fim sai suka fahimci ashe ka dau fim ka wanka matsala ne ba ma ya birgewa.

 

Batun Film Billage da aka yi  caaa! Sai aka ga kamar gwiwarku ta yi sanyi a harkar bakidaya.

Ai mu Fim Billage bai sa mun yi sanyi ba; ba dai mun kara bi ta kanta ba ne. Ai idan ma ban da Nura Husaini da wasu daidaikun mutane ba, wadanda ya ma tsaya ya yi wani jawabi kai. Saboda ai ma mutane ba su fahimci mene ne fim billage din ba, mu kuma abin da muke gani kasuwar Jakara ma Fim Billage ce, Kofar Nasarawa da su Dutsen Dala da Goron Dutse duka shi ne tunda gurare ne da gwamnati ta sahale mana mu je mu yi fim dinmu; ba mu matsawa kowa ba, hankali kwance. Wancan babba da aka hana mun yi la’akari da ma mutane ba su ma fahimta ba sai an wayar musu da kai a hankali, don sun dauka manyan gidaje za a bude a ba mu mu shiga. Don mutumin da yake yin yawo ya je kasashe irin su Egypt su Marocco ya san me ye fim billage don in ya je aka ce ma ya koma ba zai koma ba, don daga inda ya sauka zuwa inda fim billage din yake kudin da zai kasha ba kadan ba ne, sannan kuma in ya isa wajen fili zai gani fetal don dajin Allah aka yanka aka yi kuma kome na wajen daga katako sai roba in an kammla amfani da shi nadewa ake a ajiye sai kuma wani amfanin ya taso.Fim billage wajen adana tarihi ne. Ai da ma an yi fim billage ci gaban ya kai iyaka watakil ma mu sai dai mu zama ‘yan kallo swatakilma muna zaune daga saudiyya ko ingila za a zo a yi tarihin Kano ko wata al’ada saboda kudi za a kasha masu yawa kuma kudi za a nema daga haya zuwa masu yin sai ka ji ana batun miliyan dari a hada kaya kawai.

 

Fim din kara’i fim ne da ya zo da sabanin yadda ka saba fitowa ya ka ji da ka ji ka ga script din?

Lokacin da aka kawo min script din kara’i aka fada min ga abin da za a yi a jikiin shirin sai nake jin ina ma a yanzu da aka kawo min a yanzu za fara daukar shirin har shi furodusan mamaki ya kama shi ya ce chairman ya daga kawo w aka ce ko yanzu a fara sai y ace me ne dalilinka? Sai na ce a kasar Hausa akwai mutanen da kulba na barna amma ana cewa jaba ce akwai mutanen da ga shekaru sun cimma su kuma sun sami kudi amma bas a tunanin taimakon ‘ya’yansu da al’umma ko dai su ba da tallafin ilimi ko sana’a ko wani muhimmin bangare illa su burinsu su sheke aya tunda sun ga wasu na yi kuma a tunaninsu suna jin dadi za su sa kananan kaya su yi bariki.

 

Ya zama da iyali yake da sana’ar Fim b aka samun matsala da uwar gida?

Gaskiya ina cikin wadanda suka yi sa’a tsakaninmu da iyalanmu matata mun fahimci juna sannan ita ma ‘yar wasan kwaikwayo ce lokacin tana sakandire ta Kabo ta yi Hausa cultural group ta karanta wani abu kadan game da wasan kwaikwayo don haka da Allah ya hadamu da ita sai ya zama wani lokaci mukan jarraba yi acting ni da ita a cikin gida in zan tafi wani shiri musamman kamar shirin da nake gani zai wahalar da ni misali a ce na zo a kwarto y azan yin a shiga falon gidan kuma in na zo wacce irin Magana zan yi wa matar in na zauna wanne irin sakin jiki zan yi wani lokcin nakan jarraba irin wannan da me dakina daga nan sai na sami kwaringwiwar fita.

 

Ka na fatan magaji a cikin iyalinka?

Ai ‘ya’yana sun fara fim ni na dan dakataar da su saboda ina son su yi karatu saboda sana’ar fim sana’a ce da idan ba ka da ilimi ko na arabiyya ko na boko idan b aka da ilimi z aka zama dan kallo ne wadanda ke shura a sana’ar duk ‘yayan makaranta ne. Babban dana Abdallah ni na dauke shi aka yi wani fim da shi Uwar gida. Baba Hassan mai bin sa shi ma ya yi wani fim ga koshi ga kwanan yunwa.

 

Akwa wani kalubale ku da kuke masana’antar ba kwa auren abokanan sana’arku me ya sa?

Ey to haka dai mutane ke fada amma ba haka ba ne misali bari na dauko miki daga can nesa akwai wani tsohon jarumi Ibrahim Buba matarsa da ya aura Rabi Musa acting ne ya hada sun a fim akwai Sani Mu’azu daga Jos matarsa da ya aura acting ne ga Sani musa ya aur Faty Muhammad mansura sun yi aure da Sani Danja da Muhibbat da mijinta Gigs ga Abida Muhammad da Danzaki mutuwa ta raba su

 

To, akwai kuma batun in matan sun yi auren ba sa zama.

Laifin daga gun mazan da suke aurensu ne . dalili yarinya ce aka yi mata kwalliya ta shiga gida me tsada aka ba ta mota mai tsada daga ganin haka tsaf da ita sai y ace sai ya aureta zai kasha kudi har ta zo gida to kuma bayan ta zo sai zama ya garara saboda aure ne na son zuciya ba don  Allah ba. Sannan akwai  kaddara mutuwar aure a yau ta zama gidan kowa akwai amma gas u nan dayan gaske suna zamansu. Ina su Zahara’u Shata da Maijidda Abdulkadir da Aishan ki yarda da ni su Hindatu Bashir duk suna gidajensu da yaransu lafiya. Ai ma wadanda ke gidajensu sun fi wadannda suka fito yawa.

 

Ya ka ke ji in an s aka a sarki ko wani mai mulki musamman in an daura ma kamara?

(Dariya) Na taba ji sau daya da dadewa a wani shiri a Kaduna na fito a shugaban kasa ga masu tsaro ga motoci na alfarma amma ni a lokacin motata bitil ce aka yi komai aka yi kade-kade aka ba ni filawar nan da aka tare ni na biyo red carfet ga jiniya ina ta daga hannu. Lokacin da aka gama shiri sai nag a mutane na darewa n ace yay a haka? Suka cee y to y aba za a yi haka ba. Nan dai aka bar ni ‘yar bitil din tawa ma aka ce ba me shiga sai ni kadai.Sai da na ji abin a raina anan na kara gano ashe masu mulki in aka ce su sauka bas a jin dadi.

 

Yadda aka bar addini da al’adunmu a fina-finai a yau ci gaba ne ko ci baya?

Gaskiya ci baya ne don duk a sha’anin fim kowane yanki ko kasa ko nahiya kokari suke su tallata hajarsu wato zamantakewarsu da addininsu da al’adunsu

 

Bayan kasancewarka dan wasa kai ma ka rikide ka zama mai shirya fim ko bayar da umarni?

Tun da nake ban taba rubuta fim ba ko shiryawa ko bayar da umarni ni jarumi ne kawai sai dai a dauko ni na taka rawa. Saboda ni shin a zaba. Ni na yarda da ka dauki bangare guda ka ginu a wajen saboda in k ace z aka raba kafa to a karshe z aka yi biyu babu tsalle-tsallen bay a kawo ci gaba.

 

Wanne Kira Gare ka Ga ‘Yan Fim Musamman Masu Tasowa?

Kirana kullum gare su shi ne su nemi ilimi. Ilimin nan shi ne kashin bayan kome a yau. Wanda ke sha’awar shiga harkar akalla ko diploma ce ya kawo sannan ya daure ya zamana yana da ido a addini. Saboda harkar Fim hark ace ta ilimi.

 

Wanne Kalubale ne ke Ci Ma Tuwo a Kwarya a Harkar Fim?

Gaskiya kalubalen da nake samu shi ne irin mutanen da wani zai tare ni saboda na taka wata rawa a fim ba zai bari na yi masa bayani ba ko ya bari ya fahimci me yasa na taka rawar kawai sai yah au ni da fada da hayaniya wani har da zage-zage wannan abu na ci min tuwo na taba cin karo da irin wannan ma lokacin da na taka rawa a wani fim Adon gari. Labarin na kalla don na zo a matsayin dan daudu har masoyana suka ga wannan rawar bai dace ba duk da a karshe na zama malami na shiryu. Amma fa na sha kalubale.

 

Malam Shehu Hasan Kano, mun gode kwarai.

Ni ma na gode.


Advertisement
Click to comment

labarai