Connect with us

RA'AYINMU

Yaushe Za A Gyara Tsarin Samar Wa Nijeriya Da Kudaden Shiga?

Published

on


Samar da tabbatacce kuma kyakyawan tsarin tara kudaden shiga abu ne mai mahimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kowace kasa, domin kuwa shi ne babbar hanyar samun kudin ayyukan da duk wata gwamnati za ta gudanarwa al’ummanta. A mafiya yawan kasashen da suka ci gaba ta fuskacin tattalin arziki, duk ta hanyar sanya haraji ne gwamnatocin ke samun kudaden da suke bukata domin aiwatar da manyan ayyukan su, wadanda da hakan ne kuma suke samarwa da mutanan su ayyukan yi.

A wannan kasa tamu Nijeriya, yawancin gwamnatocin da suka gabata, ba su mayar da hankulan su ba wajen tara kudaden shigan su ta hanyar sanya haraji. Kila hakan, domin kasantuwan makudan Dalolin da ake samu ne ta hanyar Man Fetur, wanda ya kasance kashin bayan tattalin arzikinmu. To sai dai, kasantuwar abin da ya bayyana a halin yanzun na yadda kasuwar Man Fetur din ke kara fuskantar barazana, wasu gwamnatocin sun fara yunkurowa da zimmar tara kudaden shigan su ta hanyar harajin da ma kara fadada hanyoyin tara kudaden na haraji.

Tabbas a yanzun ne lokacin da ya kamata Nijeriya ta inganta tare da bullo da sabbin hanyoyin tara kudaden haraji. A bisa kididdigan Bankin duniya, kudaden shigan da Nijeriya ke Tarawa ta hanyar haraji, yana daya daga cikin mafiya karanci a duk duniyar nan tamu, domin kuwa abin da ke shigowa Nijeriya din ta fuskacin haraji, bai wuce kashi shida a cikin 100 ba na kudaden shigar da Nijeriyan ke Tarawa. Hatta a wannan nahiyar tamu ta Afrika, shi ne mafi karanta, in an kwatanta da yadda kasar Ghana ke tara kashi 15.9, na daukacin kudaden shigarta daga haraji, kasar Afrika ta kudu kuwa, tana tara kashi 27 ne na kudaden shigarta daga kudaden harajin da take azawa. Hakanan yawancin kasashen da suka ci gaba, jimillan kudaden shigan su, kashi 32 zuwa 35 duk daga kudaden harajin da suke Tarawa ne yake zuwan masu.

Mu a nan lamarin ba haka yake ba, a lokacin da ya zame wa masu arzikinmu dabi’a, su rika gujewa biyan harajin bakidayansa, su kuma ma matalautan kasar namu a duk lokacin da aka yi masu zancen cire masu harajin daga dan albashin da suke samu, sai ka ga suna fusata. Da haka ne ‘Yan Nijeriya suka saba da dabi’ar kin biyan haraji, domin kuwa in ka cire dan abin da ake debewa na dole daga albashin ma’aikatan kasarnan, to kadan daga cikin ‘yan Nijeriyan ne suke zuwa su biya harajin da ke kansu a bisa radin kan na su.

A halin yanzun, gwamnatin tarayya ta nu na aniyarta na yin amfani da tilas a kan masu kin biyan harajin, walau masu kudi ko ma talakawa ne su. Wannan yunkuri na gwamnatin tarayya a kan tilasta biyan harajin abin a yaba ne. ya kuma kamata a sake yin dubi ga dokan nan da ta tanadi bayyana kadara da kuma kudin shigan da kan shigowa masu biyan harajin, wacce ta baiwa kowa dama a bisa radin kansa da ya bayyana abin da ya mallakan a cikin watanni tara. Wannan shi ma muhimmin tsari ne wanda ya kamata da a yaba mashi, domin ya bayar da dama kai tsaye ga kowa da ya biya harajin kadarorinsa wadanda a baya baya biyan masu harajin.

Hakan kuma ya sake bayar da daman karin wayar da kai a kan mahimmancin biyan kudaden na haraji da kuma amfaninsu. Kasantuwan nasarar da wannan tsarin ya fara samu, inda har ta kai ya zuwa yanzun gwamnatin tarayya ta iya tara sama da Naira bilyan 17 ta wannan hanyar tun daga lokacin da aka kirkiro shi. Wannan wani shirin yin rangwame ne na musamman, wanda ya baiwa mutane daman biyan harajin da ke kansu ba tare da an dora masu wani ruwa ba, ba kuma tare da an yi masu wani hukunci ba. Don haka, muna yin kira ga gwamnati da ta bi ka’idojin wannan shirin da kyau wajen aiwatar da shi.

Bukatar bunkasa hanyar tara kudaden haraji, ta wajabta samar da karin guraben ayyuka sama da 7,500, na jami’an da za su yi aikin tara kudaden harajin a cikin al’ummu, ta yadda za a cimma kyakyawan manufa. Hakanan gwamnati ta bayyana cewa, za ta sanya ido sosai a kan dukkanin kamfanonin da suke yin harkokin cin riba a wannan kasa tamu, amma kuma sai su koma ainihin kasashen da suka fito suna biyan haraji a can, mu kuma a nan sai su rika biyan mu abu dan kadan, a wasu lokutan ma ba wani abin da suke biyan mu.

Matukar ana son cimma manufa mai kyau na tara kudaden haraji, to ya wajaba ayi komai a bisa yadda ya dace. Muna kuma kira ga masu biyan harajin da su baiwa wannan yunkuri na gwamnati cikakken goyon baya, kamar kuma yadda muke yin kira ga gwamnati da ta kiyaye bin tsari da doka wajen tara wadannan kudaden ba tare da cin zarafin kowa ba. Wajen cimma wannan manufa akwai bukatar gwamnati ta samar da sabuwar hanyar tara kudaden. A yi amfani da hanyoyin zamani wajen cire kudaden daga asusun ‘yan kasuwa da sauran al’umma.

Ya wajaba gwamnati ta mayar da hankali sosai wajen samar da hanyoyin da suka dace sosai na tara kudaden harajin, domin ta hakan ne kadai za a sami isassun kudaden da gwamnatocin za su yi wa mutanan kasa aikin da ya kamata. Hakan kuma zai sanya ‘yan kasa bakidaya su kasance suna bayar da gudummawarsu wajen gina kasan su, wanda da hakan ne kuma za a iya samun cikakken da’a da biyayya ga ita kasar kanta.

Sannan kuma wadannan kudade da za a tara ta hanyar biyan haraji sun fi zama tabbas ga tattalin arzikinmu, sabanin kudaden da ake samu ta hanyar sayar da danyan man Fetur wanda a kullum kasuwarsa tana sama ne tana kasa ba wani abin da ke da tabbas a cikin sa. Da wannan ne zamu iya yin tanadi mai zurfi da kuma shirye-shirye masu tsawo, na aiwatar da manyan ayyuka a wannan kasa tamu.


Advertisement
Click to comment

labarai