Connect with us

LABARAI

Sabon Turakin Rano: Nadin Sarauta Ya Rikide Gangamin Taron Siyasa A Kano

Published

on


Daga  Mustapha Ibrahim Kano

 

A jiya Asabar 24 ga Maris, 2018 aka gabatar da wani gagarumin taro a garin Rano da ke jihar Kano karkashi jagorancin Dakta Tafida Abubakar Ila Sarkin Rano Garin Autan Bawo, inda aka nada Turakin Rano tsohon kakakin majalisar dokoki na tihar Kano, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, sarautar Turakin Rano a wannan yammaci na ranar Asabar.

Taro, wanda gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zama babban bako, ya samu rakiyar daukacin mukarraban gwamnati da sauran mahimman mutane a Kano da kasa bakidaya, inda su ka hada da kwamishinoni da sauran yan majalisa a matakai daban-daban daga jahohin kasar.

Hakan ta sa gurin taron ya rikide ya zama kamar taron gangamin siyasa ta yadda matasa su rika daga hotunan ’yan siyasa masu mukami da masu neman mukamai daban-daban a cikin fadar mai girma Sarkin Rano yayin da sauran matasa ke rike da makamai daban-daban musamman ma kungiyoyin mafarauta da su ka hallaci wannan nadin sarautar, wanda hakan ya sa a ka rika tambaya a gurin taron na cewa taron nadin sarauta ne ko taron siyasa ne a ke yi yau a Rano?

Sai dai kuma wani fitacce a dan garin, Alhaji Ubale Adda’u Rano, shugaban sashen kula da lafiya matakin farko a karamar Hukumar Tofa kuma shugaban kula da ilimin firamare, yabawa Sarkin Ranon ya yi da kuma sabon Turakin nasa kan kyakykyawar mu’amala da jama’a.

Shi kuwa mai neman zama dan majalisa mai wakiltar Rano a majalisar dokokin Kano, Alhaji Bellon Liman, ya bayyana Turakin a matsayin shugaba abin koyi.

Jagoran matasa kuma, Mukhtaru Musa Rano ya ce, Hon. Bellon Liman shi su ke so ya gaji kujerar mukamin Turakin Rano, Turaki kuma ya tafi majalisar tarayya.


Advertisement
Click to comment

labarai