Connect with us

LABARAI

Kungiyar Engender Health Ta Gana Da ’Yan Jarida A Ilesha Kan Yoyon Fitsari

Published

on


Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Kungiyar Engender Health mai samun tallafin kungiyar ci gaban kasashen ta America wato USAID a karkashin shirin kawo karshen lalurar yoyon fitsari na Fistula Care Plus, ta jaddada yin kiri da  babbar murya ga masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a ta hanyar amfani da kafafen yada labarai da shugabannin al’umma domin ganin an samu kai wa ga shawo kan matsalar cutar yoyon fitsari da ta fi addabar mata a yankunan karkarar Nijeriya.

Shugaban kungiyar ta Engender Health a Nijeriya Dokta Iyeme Efem shine ya bayyana haka a wajen taron kungiyar da manema labarai a garin Ilesha da ke Jihar Oshun a jiya. Taron wanda ya gayyato manema labarai daga dukkan kafafen da suke aiki tare a Nijeriya, an gudanar da shi na kwanaki uku daga ranar alhamis zuwa lahadi, inda aka tattauna game da yadda za a ci gaba da wayar da kan mazauna yankunan karkara don ganin sun kare mata daga kamuwa da lalurar ta yoyon fitsari ta hanyar bin dokokin da suka dace a lokacin da mata ke da juna biyu don su aihu lafiya ta hanyar zuwa awu da karbar alluran rigakafi da sauran shawarwari.

Dokta Iyeme Efem lokacin da ya ke jawabi a yayin bude taron na Ilesha a jiya ya ja hankalin shugabannin al’umma da su ci gaba da tabbatar da wayar da kan jama’a don su rika tura mata zuwa awu a kan lokaci da zarar sun samu juna biyu domin a tabbatar za su iya aihuwa da kan su ko sai sun samu temakon kwararru kan kiwon lafiya. Bayan haka kuma ya bukaci mata masu juna biyu da su rika zuwa awu tare da aihuwa a asibiti.

Idan kuma an samu matsala musamman ta yoyon fitsari a tafi zuwa ga cibiyoyin da wannan kungiya ke aiki da su domin bayar da shawarin da suka dace ko yin aiki cikin gaggawa don raba mata da wannan matsala tun bata habaka ba. Saboda ba wata hanyar warkewa da yoyon fitsari sai an yi wa mata aiki tare kuma da bata duk wata kulawa da ta dace, bayan haka kuma ana wannan aiki kyauta a irin wadannan cibiyoyi da ke jihohi dabam dabam a Nijeriya.

Daya daga cikin likitoci masu wannan aiki na tiyatar yoyon fitsari  a yayin wannan taro na Ilesha, Dokta Abiodun Amodu ya ja hankalin masu ruwa da tsaki kan wayar da kai game da wannan matsala da su kara himma don zakulo matan da suke tare da wannan matsala saboda a musu aiki.

Kuma ya yaba game da kokarin ma’aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya na sanar da cibiyoyin da asibitocin kiwon lafiya mallakar gwamnatin tarayya domin su bude dakunan majinyata masu yoyon fitsari don su rika samun kular da ta dace kyauta, saboda yawancin masu kamuwa da wannan matsala marasa galihu ne.

Harwa yau shugaban Engender Health a Nijeriya Dokta Iyeme Efem ya bayyana cewa kungiyar za ta sake horas da likitoci goma don su ci gaba da taimakawa wajen tiyata ga mata masu yoyon fitsari a Nijeriya domin a samu dorewar lura da dimbin matan da ke dauke da wannan matsala a Nijeriya.

Don haka ya shawarci ‘yan Nijeriya da su gujewa dabi’u irin na gargajiya game da wannan matsala musamman irin su yankan angurya da yankan gishiri da kari wa mata yayin aihuwa daga ungorzoman gargajiya lamarin da shi ne ke haifar da irin wadannan matsaloli na karuwar yawan masu dauke da lalurar ta yoyon fitsari.

Ita ma babbar jami’a kan ci gaban shirin na Engender Health Ebere Diokpo ta ja hankalin ‘yan jaridun da su kara himma wajen ganin sun wayar da kan jama’a game da yadda za a yaki matsalar ta yoyon fitsari musamman ganin akwai dubban mata da ke fama da wannan lalura amma har yanzu basu fito don zuwa cibiyoyin da za a taimaka musu ba. Don haka ta bukaci jama’a su bi hanyoyin kare kai daga kamuwa da wannan matsala don ci gaba da samun tallafin wannan kungiya kafin lokacin da za ta kawo karshen aikin ta a Nijeriya nan da watan Satumba.


Advertisement
Click to comment

labarai