Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Neja Za Ta Sa Ido KanShigowar Baki

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya bayyana cewa gwamnatin za ta ci gaba das a ido wajen shigowar baki cikin jihar nusamman bakin da ke zuwa daga kkasashen waje ta barauniyar hanya. Saboda haka sai ya yi kira ga jami’an Hukumar kula da shigi da fici ta kasa da su kara sa ido domin kama irin wadannan mutane masu shigo wa kasa ba izini,

Daga nan sai shugabar Hukumar ta NIS Misis Amadih Honby ta mai kula da yankin ta  bayyana wa gwamnan cewa za su hada kai da gwamnatin jihar wajen ganin sun kawo karshen wannan matsala ta kwararowar baki cikin jihar, musamman wadanda ke shigo wa ta barauniyar hanya.

Gwamnan ya yaba da kokarin da Hukumar ke yi wajen gudanar da ayyukanta saboda haka shi ma sai ya lashi takobin taimaka musu da dukkan abin da suke bukata wanda zai taimake su wajen aikinsu. Sannan sai ya kara tuanatar da jami’an Hukumar bisa gagarumin aikin da ke gabansu a kan iyakokin jihohin kasar nan musamman jihohi irin su  Neja da Kebbi da kuma Zamfara.

“Muna da hanyoyi masu yawa a wadannan jihohi wanda tan an mutane na iya shigo wa a kowa ne lokaci suka bukata. “Yanzu haka na samu rahoton cewa bakin haure na shigo wa kasar nan musammam ta kan iyakarmu da Nijar, saboda haka ya kamata jami’ar wannanhukuma su kara kaimi wajen sa ido a kan masu shigo wa cikin wannan kasa”.

“Ina tabbatar muku da cewa zan ba ku dukkan taimakon da kuke bukata wajen gudanar da ayyukanku kamr yadda muke bai wa sauran ma’aikatun gwamnatin tarayya gudummawa yadda za su samu nasarar aiwatar da ayyukansu.”


Advertisement
Click to comment

labarai