Connect with us

NISHADI

Diyar Hadiza Kabara Ta Sauke Alkur’ani

Published

on


A kwanakin baya ne diyar Hadiza Kabara, Bilkisu Muhammad ta yi saukar karatun Alkur’ani maigirma. ‘Yan fim musamman mata sun mata kara inda suka yi dandazo wurin halartar walimar saukar a gidan Hadiza a Unguwar Fanshekara da ke Kano.

Hadiza Kabara ta tofa albarkacin bakinta ga LEADERSHIP A Yau Juma’a kamar haka: “Assalamu alaikum,  wanan yarinya dai Sunanta Bilkisu Muhammad Kabara, an  haife ta a shekarar 2005. A yanzu tana da shekara goma sha uku kenan. Allah cikin ikonsa ya sa ta sauke Alkur’ani maigirma a ranara 11 ga Maris din 2018. Wadanda suka zo ‘yan fim dinmu duk na gode, Allah ya saka da alheri. Jama’a duk sun yi min kara kuma ina yi wa kowa da kowa fatan alheri, na gode”.

 


Advertisement
Click to comment

labarai