Connect with us

AL'AJABI

Abin Da Ya Sa A Ke Bankare Wa Budurwa Lebe A Kabilar Kibishi

Published

on


Yau filin namu zai sada ku da mutanen ‘Suri’ da ke Kasar Habasha (Ethiopia).

Su dai wadannan bayin Allah suna rayuwa ne a yammacin kogin ‘Omo’ da ke kudu-maso-yammacin Habasha, ana kiransu da “Kibishi”.

Bincike ya nuna cewa su dai wadannan mutane makiyayane, sannan a kan gane yawan dukiyar kowane gida ta hanyar la’akari da yawan dabbobin da suka mallaka.

  • Addini

Wadannan mutane suna da abin bauta wanda suke yi masa lakabi da “Tuma”. Sun yi imani Cewar shi dai wannan Tuma ya kasancene a cikin sararin samaniya, bugu da kari mutanen sun yi imani da almatsutsai da kuma ifiritai, sun kuma yi imani da cewar su din a karan kansu na iya sanya ruwan sama ya sauka a lokacin da suke bukata.

  • Al’ada

Inda ranka kasha kallo! Wani abin ban al’ajabi da wadannan al’umamma shi ne dabi’arsu ta fafake leben baki, sannan a sanya masa faifayin katako, yanda suke yi kuwa shi ne duk inda yarinya mace ta kai munzalin shekara “goma sha biyar” zuwa “goma sha shida” za a yanka leben bakinta na kasa sannan a fafake shi sosai ta yanda zai zamto ya rabu da ainihin mahadinsa da habarti.

Ba kowa nauyin yin haka ya rataya a wuyanta ba sai mahaifiyarta, bayan an fafe bakin sai a sami dan madaidaicin faifayi na katako a sanya mata a leben yayin da zai tokare leben. Haka za a bar shi har sai lokacin da aka tabbatar wannan ciwo da ke wajen ya warke tas, daga bisani sai a cire wannan a sake sanya wanda ya fi wanda aka cire din girma. Haka dai za a yi ta canza su bisa yanayin girmansu, ma’ana idan aka cire wani sai a sami wanda ya fi shi girma a saka. Za a yi ta canzawa har na tsawon wadansu watanni, sannan daga karshe sai a saka kanda ake ganin iya bakin girmansa ake bukata ya kasance a wajen.

‘Tirkashi! Allah daya gari banban.

A yanzu dai wannan dabi’a ta danganta da ra’ayin ita yarinyar da za a yi wa, ma’ana idan tan aso za a yi mata idan kuwa ba ta so, to falillahil hamdu sai a barta ba lallai ba tilas, sai dai har yanzu al’ummar sun yi imani cewar wannan huda na baki alama ce da ke nuni da cewar yarinya ta kai munzali sannan kuma yakan kara mata wani daraja da daukaka ta musamman a idon samari.

A cikin al’adunsu akwai horas da matasa ta hanyar koya musu fada, har su zamto gawurtattun jarumai, wannan ya samo asali ne sakamakon yawan tashe-tashen hankula da ke wanzuwa tsakanin su makiyaya da kuma makotansu mutanen “Nyangatom” a kan filaye da kuma gonaki.

  • Auratayya

Su dai wadannan mutane sukan gwada jarumtar saurayi da ke neman aure ta hanyar shirya gasa ta musamman wanda da shi a ke tantance samarin ta hanyar duba jaruntakar kowa a gasa. Gumurzun fada a ake yi kashirbin a tsakanin maneman auren budurwar, inda taron yakan sami halartar gangamin samari da ‘yanmata domin su shaida abin da zai wakana. Akan shirya yin wannan gasa a lokacin da aka yi ruwa ya dauke, matasan daga kauyukan ‘Suri’ za su halarci taron, ana fara fadan da mutum “ashirin “ zuwa “ talatin” daga kowanne bangare sannan a fara karawa na gaba daya. A wannan lokacin za a wakilta masu alhakin kula da wannan gasa, wato alkalan gasar domin lura da yanda gasar ke gudana

Ba a nan gizo ke sakar ba, domin kuwa wannan wasa yana kunshe da tarin hadarurruka wanda yakan zamto barazana, a wasu lokutan ma ya zamto sanadin rasa rayuka misali: a ce an yi wa wani mummunan duka a ciki, ko a kai, ko dai a wani muhimmin waje da zai iya cutarwa, sannan kuma kasancewar wannan gasa takan kunshi ko ya sami halartar mutane daban-daban, fada na iya barkewa tsakanin ‘yan kallo, ko kuma wadanda dama can suna da ‘yar kullaliyar gabarsu a kasa, don haka ana haduwa sai daukar fansa.

A dayan bangaren kuma duk saurayin da ke neman aure zai bata jikinsa tas a cikin laka, tun daga fuska har kafafu sannan ya dingi yawo tumbur, yana kewaye mutane dauke da katuwar itace. Wannan al’ada suna kiransa “Dongo”.

Bayan an kammala gasar, to a nan ne kuma ‘yanmata za su fito suyi ta zaben samarin da suke so a cikin wadanda suka yi nasara a matsayin mazajen aurensu.

  • Abinci

Duk da yawan dabbobin da suke kiwatawa, wadannan mutane ba sa cin nama daga cikin dabbobinsu har sai idan ya kasance akwai wani gagarumin biki ko taro.

Abincin nasu dai sukan sarrafa shi ne ta hanyar tatsar madara daga cikin dabbobin ko kuma jinin dabbobin wanda suke samu ta hanyar yiwa dabbobin rauni. Sannan bayan an tari iya adadin jinin da ake bukata sai kuma a yi wa dabbar maganin raunin da aka yi ma ta ta hanyar manna karfe mai zafin gaske a jikin ciwon. Masu iya magana dama sun ce “abincin wani gubar wani”.

Wannan kabila ta Suri har gobe tana rike da al’adunta da ta gada tun iyaye da kakanni ba ta canja ba, duk da sauye-sauyen zamani da ake fuskanta. Allah daya gari bamban.

 


Advertisement
Click to comment

labarai