Connect with us

SIYASA

Zaben 2019: Gwamnoni Da Sanatoci Masu Goyon Bayan Buhari Sun Yi Wa Saraki Taron Dangi

Published

on


Daga Abdullahi Usman, Abuja

Sanatocin da ke goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari na taruwa don yin fada da Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, wanda suke ganin ya bullo da fada da shugaba Muhammadu Buhari, fadan da suka kira na yi-wa-kai.

Wannan kungiya da Sanatocin suka kafa, sun kafa ta ne don hana majalisar dattawa zartar da kudurin dokar da shugaba Buhari ya ki sanyawa hannu ta canza jaddawalin zabe.

Wani daga cikin Sanatocin da suka kafa wannan kungiya da suka kira da ‘Parliament Support Group’ a turance, ya shaida wa wakilinmu cewa suna nan suna kara karfi don ganin sun yaki Saraki.

Wannan kungiya ta PSG, wadda Sanata Abdullahi Adamu, wanda aka cire daga shugabancin kungiyar Sanatocin arewa kwanakin baya ke wa jagoranci.

Ita dai wannan dokar da majalisun kasa suka yi wa gyaran fuska wadda gyaran ya hada da canza yadda ake gudanar da zabe, wasu na gani da gangan majalisar ta yi haka don ta cutar da shugaba Buhari,

A watan fabrairu, wasu Sanatoci sun fice daga zaman majalisar saboda sun kasa hana majalisar amincewa da wannan canji da ta yi.

Daga baya kuma majalisar wakilai ta tarayya ta amince da irin wannan canjin gudanar da zabe da ‘yan uwarta majalisar dattawa ta yi. Sai kuma daga bayan majalisun biyu suka hadu suka amince da wannan doka gaba dayansu.

Amma shugaba Muhammadu Buhari da aka mika wa wannan doka ya ki sanya mata hannu, in da ya aikewa da majalisun wasika cewa ba zai sanya wa wannan doka hannu ba.

Amma tsoron da ake da shi cewa majalisun na iya bijirewa shugaba Buhari su yi amfani da ikon da tsarin mulki ya basu su amince da dokar ya sanya wasu ‘yan majalisar ke kokarin hana yin hakan.

Daya daga cikin shugabannin PSG, wanda ya ce bai son a ambaci sunansa, ya bayyana wa wakilinmu cewa yanzu hana sun sami amincewar Sanatoci 46.

Ya ce adadin da suka samu ya zarce abin da suke bukata don hana zartar da wannan doka. Ya ce suna neman Sanatoci 36 ne kawai. Wato kashi daya cikin uku na ‘yan majalisar dattawa din. Su kuma masu kokarin ganin wannan doka an zartar da ita suna neman a kalla Sanatoci 73, wanda shine kashi biyu cikin uku na Sanatocin.

Sanatan ya ce sun kuma sami mafi yawan ‘yan majalisar wakilai, wadanda ke tare da su. Wadanda suka masu goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ne.

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa wannan kungiya ta PSG ta nemi goyon bayan Gwamnonin da ke tare da shugaba Muhammadu Buhari don ganin sun cimma wannan buri na su.

Don haka Sanatan ya ce “Gwamnoni 20 daga cikin 24 na jam’iyyar APC na tare da mu. Kuma sun kafa kwamiti a karkashin gwamnan jihar Jigawa, don magance wannan matsala ta majalisa.” In ji shi.

Ya ci gaba da cewa har wasu Gwamnonin ba sun baiwa ‘yan majalisat da suka fito daga jihohinsu umarnin su tabbatar sun shigo cikin wannan kungiya ta PSG. Saboda haka ya ce har yanzu suna tsammanin karin samun wasu ‘yan majalisun.

“Muna fatan samun wasu ‘yan PDP su shigo cikinmu. PDP na da Sanatoci 45 ne. 25 na tare da su, muna fatan sauran 20 din da ba su bayyana inda suke ba za su shigo cikinmu.” In ji Sanatan.

Ya ce abin da suka fata shine su tabbatar wannan doka majalisar ba ta zartar da ita ba.

Wani Sanatan da ke cikin wannan kungiya, ya bayyana cewa abin da ke gabansu ba wai kawai su hana zartar da wannan doka ba.

Ya ce sun atakaicin ganin cewa sune ke mulki, amma wasu daga cikin su sun zama ‘yan adawa ba tare da wani dalili ba.

Ya ba da misali da yadda majalisar ta ki amincewa da wasu daga cikin wadanda shugaba Buhari ya aike mata don nadasu wasu mukamai.

Ya ce Ibrahim Magu majalisar dattawa har yau ta ki amincewa da shi a matsayin shugaban hukumar yaki da cin nhanci da rashawa ta EFCC.

“Sanatocin da ke da matsala da EFCC ba su wuce su 20 ba, amma al’umma na kallon wannan kin amincewa da Magu a matsayin mu duka ‘yan majalisa ne muka yi hakan. Saboda haka wannan abin da wasu daga cikinmu suke yi yana shafarmu sosai. Saboda haka kanmu ya waye yanzu, ba za mu bari wasu su yi amfani da mu ba don biyan bukatar kansu.” In ji Sanatan.

Wata majiya da ke kusa da wannan kungiya ta PSG ta shaida wa wakilinmu cewa cikin daren yau kungiyar za ta gana da Gwamnoni da kuma wasu mukarraban Gwamnatin tarayya don tsara matakan da za su dauka nan gaba.


labarai