Connect with us

WASANNI

Duk Duniya Babu Dan Wasa Kamar Ronaldo, Inji Zidane

Published

on


Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya bayyana cewa duk duniya babu dan wasan dayakai Ronaldo sanin yadda ake zura kwallo a raga a kowanne yanayi da ake ciki na wasa.

Real Madrid dai  ta ci kungiyar Girona daci 6-3 a Gasar Cin Kofin La Liga wasan mako na 29 da suka kara a ranar Lahadi a filin wasa na Santiago Bernabeu dake birnin Madrid

Real Madrid  ta ci kwallon farko ta hannun Cristiano Ronaldo minti 10 da fara wasa, yayin da minti 19 tsakani Girona ta farke ta hannun Cristhian Stuani.

Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Cristiano Ronaldo ya kara ta biyu, sannan Lucas Bazkuez ya kara ta uku, sai Cristiano Ronaldo y ci ta hudu kuma ta uku da ya ci a karawar. Cristhian Stuani ne ya kara farkewa Girona kwallo ta biyu, inda Real Madrid  ta kara ta biyar ta hannun dan wasa Gareth Bale, dan kasar Wales.

Girona ta ci kwallo ta uku ta hannun Juanpe, sai dai kuma Real Madrid ta ci ta shida ta hannun Cristiano Ronaldo kuma na hudu a wasan.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma mataki  na uku a kan teburi da maki 60 yayinda kuma zata kara da Jubentus a wasan zakarun turai a wata mai kamawa.


Advertisement
Click to comment

labarai