Connect with us

MANYAN LABARAI

Dalilina Na Kin Ayyana Yiwuwar Yin Takara A 2019 –Buhari

Published

on


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yanzu lokaci yayi kusa ya ayyana yiwwuwar yin takararsa a babban zaben 2019.

Shugaban Kasan ya bayyana cewa, ayyana aniyarsa ta takara a yanzun zai ba ‘yan adawa dama su shigo da wasu abubuwan da basu dace ba a siyasance, tattalin arziki da kuma tsarin rayuwa.

Buhari ya bayyana haka ne ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a karshen makon da ya gabata. ya ce, Shugaban Kasan ya bar wa kanshi masaniyar yiwuwar tsayawa takara ko akasin haka.

kakakin Shugaban Kasan ya ce, Buhari zai bayyana yiwuwar yin takararsa ko akasin haka ne a daidai lokacin da ya dace.

Yayin da yake amsa tambaya dangane da lokacin da Buhari zai ayyana yiwuwar tsayawa takara a zaben shekarar 2019, Adesina ya ce; “Ka san irin yanayin da Nijeriya ke ciki, musamman ma a yanzu. Idan Shugaban Kasa yayi magana da wuri, zai zama matsala. Akwai masu son haifar da rudani sosai a kasar.

“Kun ji ai yadda da yawansu ke yekuwar kar yayi takara. Saboda suna sane da cewa matukar Shugaban Kasan ya yi takara, sai dai su yi hakuri, domin basu da karkon da za su iya bugawa da shi. Don haka, so suke yi su kashe masa gwiwan yin takara.

“Yanzun idan har ya ce, zai yi takara, yayin da sauran kusan shekara guda kafin babban zabe, zai ba ‘yan adawa damar ci gaba da yin kulle-kulle har na tsawon shekara daya. za su jefe shi da komi don dai su iya hana shi takarar.” inji shi

Idan dai ba a manta ba, yayin wani taro a fadar shugaban kasa a watan da ya gabata ne Buhari ya bayyanawa Gwamnonin Jam’iyyar APC cewa su ba shi isasshen lokaci domin ya yi nazarin yiwuwar yin takararsa ko akasin haka.

Sai dai a wurin taron, gwamnonin sun bukace shi da ya sake yin takara kawai.


Advertisement
Click to comment

labarai