Connect with us

NAZARI

HANGEN NESA: Talakawa Na Cikin Kunci, Yayin Da ‘Yan Majalisa Ke Wawushe Lalitar Gwamnati

Published

on


Babu wanda ke musunta yanda rayuwa ta yi zafi ga talakawan kasar nan, yanda talauci ya kara tsanani da dimuwa, fargaba da tashin hankali duk akan talakawan kasar nan suka kare, bayan irin gumurzun da suke lokacin zabe, don kawai su nuna soyayyar su da bada ‘yancin su ga ‘yan siyasar kasar nan, amma kullum talakawan sune cikin halin kakanikayi da fargaba, fatara da zazzafar rayuwa atare dasu.

Dukkan wannan abun bafa wai muna zaune kasar Somaliya bane, ko kuma Afrika ta tsakiya, inda tashin hankula kadai ya isa mutum ya kasa sanya abinci abakin sa, ba kuma wai muna zaune a kasar Nijar bane, wacce ake temaka mata da kayan abinci saboda talauci, sannan ba muna rayuwa bane cikin Zirin Gaza wanda ruwa kadai yake wahala ga mazauna yankin, a’ah muna rayuwa ne a kasar Nijeriya, kasar datake da arzikin man fetur, kasar dake cikin manyan kasashen duniya dake da arziki, kasar da ita ce ta farko a nahiyar afrika a arziki, kasar dake dauke da wasu shahararrun fitattun masu kudi a duniya hadda na daya a afrika, kasar da ‘yan kasuwar duniya ke zuwa suna tallata hajojinsu na kasuwanci, kasar da manyan kasashen duniya masu arziki ke alfaharin yin kasuwan ci a kasar.

Amma kuma sune kasar da rabin al’ummar kasar TALAKAWA ne, kasar da kaso tamanin cikin dari na talakawan kasar ke kasa sanya abinci sau uku acikinsu, ita ce kasar da talakawan ke gudun hijira zuwa wasu kasashen kawai don neman Sana’a.

Abin tambaya anan shi ne ya akai aka haihu a ragaya?  Amsa ce daya me saurin fada, me saukin ganewa, mara wahalar fahimta, kuma wacce kowa ya amince da ita, ita ce zalinci daga Shugabannin kasar, rashin tausayi daga masarautar kasar, rashin imani da tausayawa ga masu kudin kasar, handama da babakere daga ‘yan siyasar kasar, halin ko in kula daga Shugabannin yankuna, da kuma kwadayi daga Jagororin addinai na kasar, sannan rashin adalci daga jami’an tsaro da kuma karbar cin hanci daga alkalan kasar, shin ina talaka zai sa kansa ya ji dadi ? Ina talaka zai kai kukansa a share masa?

An dade ana musayar zance tsakanin ‘yan gwagwarmayar kasar nan da ‘yan MAJALISUN kasar akan albashin su, yanzu yafito afili cewar su kadai ne ke more dimokrdiyar kasar, ta nuna su kadai ne kudin kasar kewa amfani, su kadai ne ke cin gajiyar mulkin kasar, wannan shi ne fa zallar rashin imani da nuna halin ko in kula, bayan miliyoyin kudi amatsayin albashi, tare da tsare rayuwar su daga jami’an tsaro, bayan manyan gidaje da luntsuma-luntsuman motocin da suke hawa har kawo yau basu taba kallon talakawa amatsayin wadanda suke da alfanu gare su, basu aikata wani aiki don amfanar talakawan, babu wasu dokoki don kare tagaiyarar rayuwar talakawan kasar, wai ina talaka zai antaya kansa ya ji sanyi ne ? Koda kudin gareshi, kayan masarufi sunyi matukar tsadar da ba zai iya bukatar da iyalinsa yadda ya kamata ba, ba’a bawa ‘diyansa karatu kyauta ba, bai sha magani kyauta ba,  ruwa da wuta sai ya siya, bayan wahalar rayuwa datake tagayyara rayuwar sa. Rana zafi, inuwa kuna ga rayuwar talakan kasar nan.

Amfanin gwamnati shi ne lura da bukatun talakawa, dalilin Shugabanci shi ne don kare yau da kullum dinsu, darajar Shugaba shi ne wanda yake yi don ‘yan kasa, wanda ya ajjiye uzurinsa don karfin Uzurin al’ummarsa, wanda yake dagewa wajen kare bukatun su, yake tsayawa kai da fata don ganin dukiyar su taje gare su, sannan rayukan su dana dukiyoyin su an karesu, an kuma wadatar da rayuwar su. Amma wannan labarin sauran Shugabannine na kasashen wasu talakawan, a kasar mu ita ce kasar da Shugaba ke kyakyata dariya don ganin talaka na wahalar rayuwa. Shugaba shi ne wanda baisan ciwon kansa ba, ballantana yasan na al’ummar dayake wakilta, wannan shi ne zallar zalinci da rashin imani.

Idan har anason zaman lafiya ya dore kasar nan, dole ne acire wannan banbancin afili, dole ne rayuwa ta kyautata ga TALAKAWA, dole ne ilimi da sauran ababen more rayuwa su wadata, rashin hakan babbar matsala ce da take ruguza zaman lafiyar kasa ,dole ne TALAKA ya ji yanada mahimmanci a duniyar sa, dole ne ya ji an damu da damuwar sa, kuma ana farinciki da farincikin sa, wane talaka ne zai yadda da kalaman yaudara na nuna cewar an damu dashi bayan ana sace ‘yan’uwan sa, kannen sa kuma ‘yan kasar sa, amma anci gaba da bidiruruwa a kasar tamkar kiyasai kawai akayi awon gaba da su?  Wannan babbar barazana ce ga talakawan kasar nan, al’ummar kasar nan basu bukatar miliyan har sha uku a wata, amma suna bukatar miliyoyin hanyoyin dogaro da kai, talakawan kasa basa bukatar akaisu Jamus ko Ingila suyi karatu, sunason kadai a gyara tsarin Jami’o’insu a wadatasu da kayan bukatun dalibai,  wannan shi ne bukatuwar talakawan kasar nan.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai