Connect with us

MANYAN LABARAI

Sauya Jadawalin Zabe: Buhari Ya Taka Wa Majalisa Birki

Published

on


A jiya ne ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taka wa Majalisar Tarayya birki, sakamakon kin rattaba hannu ga sauye-sauyen da suka gabatar a jadawalin dokar zabe ta shekarar 2018 wanda majalisar ta gabatar a kwanakin baya.

Dokan jadawalin zaben ya ayyana zuwan zaben shugaban kasa daga karshe, bayan an gudanar da zabukan majalisar tarayya da na gwamnoni.

Shugaba Buhari ya taka wa majalisar dattawan burki ne a wasikar da ya aika mata mai dauke da kwanan wata 3 ga Maris din 2018.

Wanda kuma a jiya Shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki ya karanta wa ‘yan majalisar wasikar a zaman a yayin gudanar da zaman majalisa.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa ya ki sa hannu a kan sauye-sauyen ne saboda yin haka zai yi karo da tanade-tanaden dake cikin sashi na 25 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, hakan kuma na iya zama tamkar wani katsalandan ga ‘yancin cin gashin kan hukumar zabe mai zaman kanta ‘INEC’.

Ya ce, sashen ya yarje wa hukumar zabe ta INEC shirya wa da gudanarwa da kuma kula da dukkan zaben da za a gudanar da zabe kamar dai yadda yake a sashi na 15 (a) bangare na uku na kundin tsarin mulkin kasar nan.

“Gyaran da aka yi wa sashi na 138 in da aka jinginar da muhimman ginshikin dalilan da za a iya kalubalantar zabe, yin haka na iya takaita ‘yancin dantakara na bukatar a gudanar da zabe na gaskiya ba tare da wani magudi ba.

“Gyaran da aka yi wa sashi na 152 (325) na dokar zabe zai iya tayar da batun hurumin majalisar tarayya na gudanar da zabe da kuma ikon da ta ke na kula da gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar nan.

“Ina sanar da shugaban majalisar dattijai da cewa, ina cikakken mutunta majalisar” inji shugaba Buhari.


Advertisement
Click to comment

labarai