Connect with us

LABARAI

Sama Da ‘Yan APC 2,000 Suka Canza Jam’iyya Zuwa PDP A Kano

Published

on


Kimanin sama da mutum 2,000 ‘yan jam’iyyar APC suka canza sheka daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar adawa ta  PDP a karamar hukumar Sumaila dake jihar Kano.

Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da Ambasada Aminu Wali da Gambo Salau tare da wasu kusoshin jam’iyyar PDP ne suka karbi tawagar masu canza jam’iyyar.

Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar sun bayyana ra’ayoyinsu na cewa, sun fice daga jam’iyyar APC ne sakamakon rashin gudanar da jagorancin ‘yan jam’iyyar kamar yadda ya dace, musamman wurin hadin kan ‘yan jam’iyyar, rashin gaskiya da uma bin ka’idojin jam’iyyar kamar yadda dokokin jam’iyyar ta tanadar.

 

 

 


labarai