Connect with us

SIYASA

Yadda Za A Bunkasa Nijeriya –Farfesa Moghalu

Published

on


Fassarar Mahdi Garba

 

Wannan shi ne jawabin bayyana ra’ayin zama dan takarar shugaban kasa a 2019 wanda Farfesa Kingsley Moghalu, OON ya gabatar a lokacin wani taron ’yan jarida na duniya. Wanda kuma aka gudanar a dakin taron Shehu Musa Yar’adua dake Babban Birnin Tarayya Abuja, Abuja a ranar 28 ga watan Fabrairun 2018.

Sakamakon matukar kaunar da mu ke yiwa kasarmu da kuma yadda mu ke son ci gabanta da fatan a ce yan kasa sama da Miliyan 180 sun samu ci gaba  mai amfani ba tare da bata lokaci ba  , ina da buri na zama shugaban kasar tarayyar Nijeriya daga ranar 29 ga watan Mayun 2019. Wannan ya kasance bayan bayan samun shawarwari masu yawa daga dukkan bangarori na kasar nan har ma da kasashen ketare.

Da wannan nake bayyana shaawata da bukatata na zama dan takarar shugaban kasa a shekarar 2019. Ina so a bani wannan damar domin samarwa da kasarmu fata mai kyau, kyakkyawan hangen nesa da kuma shugabanci na gari domin bunkasa gabanmu.

Shekaru 60 da suka wuce, Iyayenmu wadanda suka samar da wannan kasar irin su Dk. Nnamdi Azikiwe, Sir Ahmadu Bello da Cif Obafemi Awolowo, sun tsaya tsayin daka domin tabbatar da samar da babbar kasa wacce za a yi alfahari da ita cikin kasashen duniya saboda hazakar yan kasarta da kuma tsarin mulki wanda zai tabbatar da adalci, daidaito da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.

Har yanzu hangen nesan su da fatansu bai kai ga cimma gaci ba, domin katsalandan din mulkin sojoji da kuma samun man fetur da yadda ake almubazzaranci da dukiyar alumma, da kuma rashin samun shugabanci na gari daga yan siyasa a tsarin mulkin farar hula, duk sun hadu sun dagula alamura wanda yasa komai ya rikice bayan samun yancin kai.

Ina tsaye a gabanku a yau, ina mai tabbatar muku da cewa yanzu lokaci ya yi da zamu kawo karshen wadannan abubuwa da ba za su kaimu ga gaci ba.

Gani a yau, ina mai nuna damuwata da bacewar yan matan Dapchi 110 tare da taya Iyayensu alhini, da kuma yan matan Chibok da aka lalata rayuwarsu wadanda suke tare damu da wadanda har yanzu ake tsare da su.

A yau ina mai tsayawa gaban yan Nijeriya fiye da Miliyan 180, tare kuma da dubban yan kasuwar da suke fafutikar amfani da wutar lantarki megawat 4000.

A yau ina tare da yan Nijeriya fiye da Miliyan 100 wadanda suke fama da talauci, suke kuma rayuwa da samun da bai fice kasa da Naira 300 a kowacce rana ba.

A yau, akalla mutane Miliyan 33 ne Mazanmu da Matanmu ba su da aikin yi ko kuma wani abin dogaro da kai, kuma Yara Miliyan 15 ne ba sa zuwa makaranta, sannan kashi 60 ne kawai cikin yan Nijeriya masu ilimi.

A yau, asibitocinmu babu maaikata kuma tsofaffin kayan aikin da asibitocin suke da shi ba sa samun kulawa, har wala yau mata na fuskantar barazana, kuma rayuwarsu tana tagayyara.

Ina mai daukar wannan matakin a nan kuma yanzun nan, saboda Nijeriya a yau ta samu rarrabuwar kai na kabilanci, da kuma rigingimu na addini, wadanda kuma suke faruwa sakamakon hauhawar cin hanci da rashawa. Wannan gwamnatin ta gaza ta fuskacin samar da tsaro ga yan kasa, mun rasa matsuguni a cikin wannan duniyar. Lokaci ya yi da zamu gyara wannan.

Bakidayanmu an gajiyar damu daga yan siyasarmu wadanda suke ci gaba da hada kansu a kowanne lokaci amma ba su damu da dan kasa ba musamman talaka. Suna kara tsananta tsoronmu da kuma samun fatan ci gaba da zama daram akan mulki duk da ba su tsinana mana wani abu sabo.

Yanzu lokaci ne na samun sauyi daga tushe a siyasar shugabancin Nijeriya. Yanzu lokaci ne na hangen nesa, shugabanci ingantacce wanda ya damu da kasarmu. Yanzu lokaci ne da shugabanci yake bukatar basira, hazaka da kuma nagarta domin yakar talauci da rashin aikin yi. Yanzu lokaci ya yi a Nijeriya da za a samu matasa wadanda za su cimma nasarori a rayuwarsu, kuma lokaci ne da yayanmu mata za a dama da su. Yanzu lokaci ne da za a samu shugaba a karni na 21 wand zai jagorance mu zuwa sabuwar rayuwa mai amfani.

Abin da muke bukata a yanzu shi ne hakikanin tafiyar da take son ci gaban alummarmu, daga ita alummar, kuma abu mafi muhimmanci shi ne saboda alummar Nijeriya domin ci gaban kasarmu da kawo karshen matsalolinmu. Ina mika kaina a matsayin daya daga cikin wannan tafiyar.

Muna wata kasa da take dauke da mutane muhimmai. Idan muka yi laakari da yadda yan Nijeriya a kasashen waje suke samun nasarori. Muna jin labarai iri-iri na wadanda suka bar kasarnan da abu kalilan a hannunsu, amma dauke da fata da kuma adduoi kuma suka kawo sauyi a kasashen duniya.

’Yan Nijeriya suna da fikira da basira tare da hanyoyin ci gaba da kuma kwazo da jajircewa da hangen nesa da zuciyar gudanar da aiki. Ya zama wajibi a garemu mu karfafa wannan halayensa na su domin su yi amfani da su wajen gudanar da ayyukansu a cikin gida.

Ya ku yan uwana yan Nijeriya, tsohon shugaban kasar Amurka a kalmominsa Marigayi John F. Kennedy yana cewa siyasa yana da muhimmanci a bar wa yan siyasa.

Dole ne mu rika tambayar gwamnatinmu tsauraran tambayoyi akan alkawuran da ta yi mana dangane da samar da tsaro, akan gudanar da mulki, akan abin da ya shafi fararen hula, akan lafiya, da kuma akan yancin mata.

Duniya tana sauyawa, lokaci da yanayi ya saka a kasashe daban-daban tuni suka yi fatali da tsofaffin dokoki suka kawo sabbi, wadanda suma suna iya samun sauyi. Nijeriya bai kamata a ce ta zama an barta a baya ba. A don haka Mu, Kai, da Ni, zamu iya samar da haka ga kasarmu.

Muna bukatar mu tafi a zamanance kuma cikin sauri. Misali, mun san cewa mata a shugabanci a cikin gwamnati suna bunkasa kowanne irin tattalin arzikin kasa cikin sauri, amma duk da haka, kashi 6 ne kawai cikin masu dokokinmu suke mata. Akwai mata da yawa, wadanda suka cancanta, mata masu basira wadanda suke zaune cikin shiri domin su ba da gudummawarsu wajen yanto kasarmu. Dole ne mu fito da su mu ba su dama mu tabbatar da an ji muryoyinsu.

Dole ne mu daina canje-canjen yan siyasar da suka durkusar da kasarmu, mu samar da matasa maza da mata wadanda suka cancanta masu karsashi kuma masu basira. Matasa kuma wadanda suka shirya suke da damar su shiga a fafata da su, dole ne su shiga domin a kwaci shugabanci daga wannan fafutikar da ake yi, domin ana maganar fatan kasarmu ne ba ana maganar abin da ya shude bane.

Fafutikar samar da sauyi mai kyau a Nijeriya zuwa ga kasa mai karfi, yana bukatar nagarta, dabi’a mai kyau da kuma karfin yin aiki. Kuma a matsayina na dan kasa wanda nake son zama shugaban kasa, ina da dukkanin wadannan halayya.

Idan ana maganar nagarta ne, aiki na a matsayin mataimakin babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda na gudanar da shugabanci na kuma bada gudummawa wajen yanto da daidaita tsarin bankin Nijeriya bayan an fuskanci matsalolin shaanin kudi a duniya.

Idan ana maganar karfin yin aiki ne, aikin da na gudanar a majalisar dinkin duniya wajen sauya tsarin aiki a kasashen da suka fuskanci rigingimun cikin gida abu ne wanda kowa zai iya gani a zahiri a duniya.

Idan kuma ana maganar dabi’a ce, sai na ce ka yi magana da wadanda na yi aiki da su, manyana. abokanaina, da kuma Iyalaina, ka saurari abin da za su ce. Jajircewa tare da Ilimi da kuma goyon baya shi Nijeriya ta rasa, ina mai mika bukatata akan na yi wannan aikin, kuma a hanya a bude take a binciki yadda na yi shugabanci.

Ba ina nan bane na sanar da ku cewa akwai hanyoyi masu sauki wajen kawo karshen matsalolin kasarmu. Wannan ya wuce nan, an kwashe lokaci mai tsawo ana barna ta fuskacin tattalin arzikin kasa da shugabanci, ba za a iya gyara wannan a cikin makonni ba ko kuma cikin watanni ba. Abubuwa za su tsananta, kuma dole ne a dauki matakan da ka iya tsanantawa, wanda suke bukatar hannu da yawa. Abin da nake son sanar daku shi ne; a tare da ku, zamu samar da sabuwar hanya mai kyau.

A tare da ku, zamu iya samar da manufofi masu kyau.

A tare da ku, zamu iya samarwa da kanmu wata natija mai kyau.

Nijeriya zata samu ci gaba kyakkyawa.

A yau ban bayyana jamiiyyar da zan tsaya dan takarar zama shugaban kasa. Yanzu hange na shi ne yan Nijeriya ba wai wata Jamiyya ba, wanda a baya suke zame tamkar wani abin hawa da ake amfani da shi domin a samu mulkin siyasa.

Ina ta samun gayyata daga wadansu Jamiyyun siyasa, tafiyar da nake tare da ita, sune za su yanke shawarar kowacce jamiyya zan shiga cikinta. Wannan yanke shawarar kuma zai danganta ne da daidaiton fata na da hangen nesa ta, da kuma tsarin shugabanci. Kuma zan ayyana wannan a cikin makonni masu zuwa.

Akan wannan shawarar, zamu samar da hadakar Jamiyyu saboda zaben shugabancin kasa wanda a tare zai wakilci bayyananne kuma nagartaccen hanya wanda zai kawar da shugabancin yan siyasar da suka karkatar damu suka samar mana da cin hanci da rashawa, da kuma rashin iya shugabanci a kasarmu.

Yana da muhimmanci, a yanzu mu fara maida hankali ga masu tsayawa takara a kasarmu, mu rika laakari da zurfin karatunsu da basirarsu tare da nagartarsu, dabi’arsu, da kuma karfin yin aikinsu da binciken tarihinsu.

A aladance, muna hangen Jamiyyar da mutum ya fito ne, duk daya daga cikinn hanyoyin dimukradiya, amma basirar da muka samu a kasarnan a koyaushe ana zabar wadanda ba su dace ba. A dabi’ance, wadannan da ake zaba suna zama shuwagabannin da suke karkatar damu. Ba su iya cimma nasara. Dan takara nagari shi ne wanda zai samar da Jamiyyar siyasa. Domin Jamiyyar da ba ta da fata ba za ta iya samar da nagartaccen dan takara ba.

MANUFATA

Manufata ga kasarmu yana cikin sabon littafina mai suna BIG (Build, Innobatibe, Grow). Wato Ginawa, Kirkira, Ci gaba wanda aka fitar kwana biyu da suka wuce. A takaice, har wala yau, manufar gwamnati a karkashin shugabancina, sun hada da wadannan:

SHUGABANCI DA JAGORANCI

Samar da sabuwar duniya, sha dayan farko” na hadaka wanda zai yi laakari da cancanta tare da jagoranci domin cimma hadafin gwamnati. Dole mu kasance cikin shiri a rana ta farko. Zabar sunayen manya-manya wadanda za su taya gwamnati aiki za a bayyana sunayensu cikin Awanni 48. Gwamnatina zata samar da hujjoji da yanayi mai kyau domin alumma, da kuma samar da hanyoyin rage matsaloli a matsayin hanya na shugabancin zamani.

Samarwa da bunkasawa ta hanyar bin tsarin Ilimi da bin falsafar duniya a Nijeriya, wanda zai bai wa yan Nijeriya damar hadin kansu a manufa guda.

BUNKASA KASA

Jagorantar hanyar tuntuba a siyasance tare da hadin guiwar yan Majalisun kasa domin cimma sauye-sauye a tsarin mulkin Nijeriya da kuma dawo da kasarmu akan hanyar kishin yan kasa domin daidaiton wadata zuwa 2021.

Zamu samar da daidaito wato 50:50 wajen raba mukaman siyasa. Wannan zai rubanya tsarin National Gender Policy na 2008.

Samarwa da kuma aiwatar da da sabon tsarin hulda da muamala da kasashen ketare, tare da bin hanyoyin wajen samar da ci gaba da nasara a kasarmu kamar yadda aka yi a kasashen China, Indiya da kuma Israila. Gwamnatina zata yi bunkasa wannan.

Hukumar majalisin kasa za su amince da ita ta kuma fara aiki wacce zata samar da hanyoyin cimma nasarori ga wadannan manufofi nawa.

Zan samar da kuma inganta Jami’an tsaron yan Sandan Nijeriya, tare da inganta su ta hanyoyin ba su horo na musamman da kayan aiki tare da karfafa su  wajen ba su damar daukar maaikata akalla Miliyan 1.5 na jami’an tsaron yan Sanda Maza da mata domin bunkasa adadin da ake da su na 350, 000.

TATTALIN ARZIKIN KASA

Samarwa da kirkirar sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arziki wajen amfani da kayayyaki daban-daban na kasa da hanyoyin bunkasa wasu a matsayin hanyar bunkasa tattalin arziki.

Samar da Kamfani mai dauke da akalla Naira Biliyan 500 domin alumma da kuma masu zaman kansu, domin saka hannun jari wajen kirkirar sabbin kasuwanci bisa laakari da rashin aikin yi da matasa suke fama da shi a Nijeriya, sabbin kasuwancin da za a samar daga wadannan kudade zai samar da ayyukan yi. Kamfanunnuka masu zaman kansu ne za su rika kula da kudaden a inda gwamnatin tarayyar Nijeriya za su zama masu goyon baya da kula da shi.

Kawo sauye-sauyen a tsarin wutar lantarki domin samar da ingantaccen muhalli a tsakanin gidajen yan Nijeriya, a inda kuma bangaren kamfanunnuka za su rika amfani da iskar gas da kuma samar da karfin wutar lantarki daga ruwa.

Kawo sauye-sauye a tsarin samar da lafiya a asibitocinmu, domin tabbatar da an samu nagartaccen wuraren neman lafiya ga yan kasa. Da kuma cire tsarin fita kasashen waje  domin neman lafiya. Bangaren lafiya zai samu kashi 15 daga cikin kasafin kudin Nijeriya, wanda zai yi daidai da shelar Abuja ta kungiyar Afrika a 2001. Samar da manya-manyan asibitoci a dukkanin shiyyoyi shida da muke da su a asibitocin koyarwa na Jamia na gwamnatin tarayya.

Kawo sauye-sauye a tsarin Ilimin Nijeriya wajen kirkira da basira da kuma kuma Jari da zai taimakawa ci gaban maaikatu da ayyukan yi. Za a rika bai wa bangaren Ilimin kashi 20 daga kasafin kudi na gwamnatin tarayya, tare da bunkasa shi zuwa kashi 30 sama da shekaru 8.

KAMMALAWA

Ina nan ne a yau domin ina son ci gaban kasa ta. Bamu da wasu Iyayen gida. Mu kawai yan Nijeriya ne da muke da kishin kasarmu da ci gabanta. Mu gaba muke yiwa kasarmu kallo, hangen mu daban yake da na wadanda suke karya alkawuransu, da kuma cin cika alkawuran ci gaban kasa ga yan kasa wanda aka dade ana yi musu.

Duk da haka mun san cewa, da goyon bayanku ne zamu iya kawo dukkanin wadannan ci gaba da sauye-sauye a kasarmu. Domin cimma wannan, har wala yau, kowanne dan kasa da ya kai shekaru 18 zuwa sama ya zama yana da katin dindindin na zabe domin gudanar da zabe a 2019.

Ya ku yan uwana yan Nijeriya, wannan tafiyar tawa, tafiya ce ingantatta da take bukatar gamayyar kowa da kowa ba wadansu kebantattun mutane ba, wanda suke tare da kai. Saboda wannan tafiyar tabbas ta kowa ce, kuma zata biya bukatun kowa da kuma alumma baki daya. Akan wannan dalili, muna bukatar alumma, basirarmu da kuma kudi domin ci gabantar da kasarmu zuwa gaba. Idan kana son goyon bayan wannan tafiyar shiga shafin www.tobuildanation.com

Dole ne mu ki yadda da yan siyasa su ci gaba da kuntata mana da fikirar ba wanda zai iya sauya su. Har dukan kirji da jiji da kansu suke yi akan za su ci gaba da mulkarmu.

Muna cewa gare su; yan Nijeriya ba za a sake daukar su haka ba. Lokacin zama a bakin katangar ya wuce, ya yan uwana maza da mata.

Ina so na karkare Jawabina wajen nuna godiyata ga Iyalaina. Masoyiyata wacce take goyon bayana a gare ni a koyaushe, a koyaushe kuma take kalubalanta ta domin zama namiji wanda za a yi alfahari da shi. Ina mai godiya ya masoyiyata a bar kaunata. Ga Yayana Maza da mata, ku ci gaba da zama abin alfahari da kasancewa Yara masu basira. Ina alfahari da ku.

Nijeriya, zamu iya kai ta gaba idan muka yi aiki tare.

 


Advertisement
Click to comment

labarai