Connect with us

KIMIYYA

Tauraron Dan Adam Na NIGCOMSAT Zai Karfafa Harkar Intanet A Nijeriya

Published

on


Gwamnatin tarayya ta shirya amfani da tauraron danadam (Satellite) na NIGCOMSAT wajen cike gurbin kashi 9 da ake nema domin a kai kashi 30 a harka samar na intanet a shekara 2018.

Shugaban kanfanin sadarwa na “Nigeria Communications Satellite Company” Mista Sampson Osagie, ya ce kanfanin na kara fadada harkokin kasuwancin ta ta hanyar samar da ofishoshi da neman karin abokan hurdar kasuwanci a dukkan lungunan kasar nan tare da hadin gwuiwa da masu ruwa da tsaki a harkar intanet a kasar nan domin cimma wannan manufa.

Ya ce, kanfanin ya shirya kafa kafafen sadarwa na ICT da suka aka sawa suna “Knowledge and innobation serbices” a lungunan kasar nan domin fadakar da mutane aiyukan NIGCOMSAT tare da samar da intanet a wuraren da basu da shi a fadin kasar nan.

‘Hankoronmu a wannan shekara 2018 shi ne bayar da gudummawar cimma kashi 30 na karkafar intanet a kasar nan, mun shirya fadada harkar ta hanyar samar da ofis-ofis domin sauwaka wa abokanan hurdar mu dake a fadin Nijeriya”

‘‘Muna kuma shirin samar da cibiyoyin ICT da kuma sanar da mutane cewa zasu iya harkar su ta intanet ta hanyar amfani da Satellite dim mu na intanet fi ye da yadda suke yi a halin yanzu”

Hukumar sadarwa ta kasa “NCC” ta ce, tsarin samar da intanet a kasar nan ya kai kashi 21 ana da buwkatar saura kashi 9 ya kai kashi 30 da ake hankoron kai wa a shekarar 2018.

Shugaban NIGCOMSAT ya ce, dukan gudunmawar da kanfanin ke bayarwa na shiga ne ta hukumar “National Council for Broadband Plan” wanda NIGCOMSAT na daya daga cikin wadanda suka kafa, ya kuma kara da cewa, in har aka fara harkokin kasuwanci a kanfanin za a samu karuwar kudin shiga da kwarewa namusamman a harkokin na NIGCOMSAT.

“A saboda haka ne muke shirin fadada aiyukanmu na samar da intanet a kasar nan, wannan babban shiri ne da sai mun hada hannu da masu harkar ICT a ciki da wajen kasar nan wajen cimma.

‘‘Muna kokarin kyautata harkokin kasuwancinmu saboda rike abokan hurdar da muke dasu a halin yanzu wadanda muke hurda dasu shekara da shekaru.

‘‘Gwamnatin tarayya na taimaka wa kanfanin wajen tattaunawa da nufin samar da karin wani tauraron dan adam (Satellite) domin kowanne tauraon danadam na da rayuwar shekara 15 ne a halin yanzu namu satellite mai suna NigComSat-1R ya kai shekara 6 da kirkiro wa, yana da sauran shekara 9 kafin ya kammala zagayensa na sararrin samaniya” in ji shi.

Ya kuma bayyana dalilin rashin kyakyawar hurda da mutane basa yi da NIGCOMSAT, ‘‘Har yanzu mutane basu san cikakken aiyukan da zasu iya yi da tsarin NIGCOMSAT ba saboda basu da masaniya, ban ga laifinsu ba saboda nima haka nake kafin in shigo harkar samar da intanet” ‘‘Harkar sadarwa ta Satellite ba kamar harkokin kasuwanci na yau da kullum ba ne shi ya sa baka ganin kanfanonin sadarwa na satellite kamar yadda ake ganin kanfanonin ICT a kowanne lungu, a halin yanzu kanfanin  NIGCOMSAT ce kadai ke gudanar da harkar satellite a kasar nan. ‘‘Wannan babban kalubale ne gare mu saboda wasu mutane da dama basu fahinci aiyukan da zamu iya gudanarwa ba saboda hurdan da suke yi da kanfanonin kasashen waje, wasu na kuma ganin kamar baza mu iya samar musu da aiyukan da suke bukata ba, wasu kuma gaba daya sun raina duk wani abin da zai fito daga cikin Nijeriya ne sai su nufi abin da ke fito wa daga kasashen waje, wannan ne yasa muke kokarin fadakar da mutane irin aiyukan da muke yi da wadanda zamu iya yi domin karfafawa masu hurda damu gwuiwa da kuma wadanda suke kokarin fara hurda da mu” ‘‘Mutane sun fi son hurda da kanfanonin satelite na kasashen waje mai makon na NigComSat saboda suna tunanin bamu da kwarewar daya kamata amma a halin yanzu mutane sun fara samun kwarin gwuiwa da harkokin NigComSat-1R saboda kwanan nan muka kullla yarjejeniya tsakaninmu da kanfanin Belintersat na kasar Belarus haka kuma kanfanin kasar Chaina da ta taimaka wajen samar da satalite din na cikin yarjejeniya da aka sawa hannu an yi haka ne domin karfafa aiyukanmu da kuma gamsar da abokan hurdan mu na gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu”

‘‘Wannan shiri da muka yi har ya fara haifar mana da mai ido domin kuwa a halkin yanzu mun fara samun masu nuna sha’awar su a kan aiyukan mu daga kasashe irin su Botswana da Cote Boir da Jumhoriyar Benin da kuma kasar Garbon”

Shugaban kanfanin ya kuma kara bayayyana cewa, NIGCOMSAT na gudanar da aiyukan da doka ta tanadar mata ga dimbim jama’a sai dai wadanda basu san cewa satalite din ta na NigComSat-1R da kanfanin “NigComSat Nigeria limited” ke gudanarwa zai iya yi musu aiyukan da suka shafi samar da intanet da watsa bayanai irin na radio da sauran harkokin da suka shafi sadarwa ba.

a kan ko yarjeniyar da suka kulla da kanfanin Berlintasat ya kawo karshen bukatar karin wani satellite ke nan, sai ya yi bayanin cewa, ‘‘Ba haka bane abin da muke cewa shi ne da zaran satellite ya fara tsufa karfinsa zai rinka ragewa saboda haka in har kana da sabon satalle da zaran wanda kake amfani da shi ya fara rage karfi sai ka dawo da abokan hurdan ka kan sabon saboda samar da ingantacciyar aiki ga abokan hurdan ka”

‘‘Ba wai mun kure karfin NigComSat-1R bane har yanzu muna da saura kashi 60 da bamu riga mun yi amfani da shi ba, muna da sauran guraben da za mu iya bayar wa ga abokan hurda da mu masu bukata.

 


Advertisement
Click to comment

labarai