Connect with us

LABARAI

Shugaban PDP Ya Bukaci Mata Da Su Rika Shiga Siyasa

Published

on


Ranar Alhamis ce ta makon daya wuce  shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus , ya yi kira da mata cewar su rika fitowa takara, samun shiga wani ofishi, wannan a cewar shi za a samu daidaituwar al’amura.

Secondus ya bada wannnan shawaarr ne a Abuja lokacin da yake gabatar da jawabi awani taro mai taken, ‘Pressing for Progress’ wanda ofishin shugabar mata ta kasa ya shirya,  a matsayin wani abu daga cikin bukukuwan da aka yi domin tunawa da  ranar mata da duniya ta shekarar 2018.

Ya ce, mata sun dade suna ganin laifin gazawa na maza a dalilin rashin aikata wani katabus wanda matan ba suyi ba.

Kamar yadda ya jaddada sai idan har su matan su taka wata muhimmiyar rawa a wajen shugabancin kasa, kasar Nijeriya ba zata samu wani ci gaban da zai burge ba.

Mista Secondus ya bayyana cewar duk wata kasa wadda ta nuna bata damu da mata ba, ba wani ci gaban da zata gani, don haka bai kamata ba mata su bari a ci gaba da yaudararsu.

‘’Na ga wata kasa da mata ke taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa, tunda mu maza mun kasa, a shekaru masu yawa da suka wuce, watarana zamu iya samun shugabar kasa mace’’.

‘’Ina mai8 ba mata hakuri a madadin maza wadanda suna suka rika tafiyar da kasar a shekarun da suka wuce,muka kuma kasa yin wani abin a zo a gani.

‘’Dole ne a ci gaba da nemar wa mata ‘yancin kansu, muna kira da mata da cewar su yi amfani da damar da tsarin mulkin  jam’iyyar PDP ya bayar akan mata, wadanda suke da sha’awa ta tsayawa takara neman mukamin wani ofis’’.

‘’Mata ya dace su kasance ba cikin wani tsoro ba, su tsaya takarar neman ko wane irin ofishi, wanda ya fara da na kansila zuwa na shugaban kasa’’.

Shugaban ya yi kira ga mata da su tabbatar da cewar sai gwamnatin da jama’a suke so it ace aka ba, mulki a shekara 2019 bayan an kammala zabe.

Ya kara kira ga mata kar su ji tsoron wani abu, amma su fito kwansu da wkarwkata su jefa kuri’a su kuma, tabbatar da cewar an yi amfani da kuri’ar da suka sa, an yi amfani da ita.

Mista Secondus y ace, sakamakon zabubbukan shekara ta 2019 ya danganta ne akan rawar da mata suka taka.

Ita ma a tata gudunmawar shugabar mata ta jam’iyyar PDP Hajiya Mariya Waziri, akwai ranar da ka ware musamman, domin a yi wa mata jawabi akan matsalolin mata da kuma ci gabansu, a fadin duniya.

Waziri ta kara bayyana kusan mata bilyan daya basu da aikin yi, yayin da kuma akwai su da yawa wadanda suke fama da matsaloli da yawa, da cin mutuncinsu ta hanyoyin daban daban.

‘’Dole ne mu fara daukar matakai na daukaka mata da kuma tabbatar da sun taka rawa ta hanyar zaben mace da kuma nada ta.

‘’Sai mu ci gaba mu yi watsi da duk wasu tunanin da akan yin a rashin adalci a shekarun baya, bayan nan kuma a shiga wani sabon babi’’.

‘’A zabubbuka masu zuwa ya dace mata su klasance a gaba gaba a mulkin damukluradiyya, wanda za a fara da da bangaren jam’iyya, da kuma taka muhimmiyar rawa.’’


Advertisement
Click to comment

labarai