Connect with us

LABARAI

Sauya Sheka: Muna Tabbacin Masari Mutumin Kirki Ne –Tsaffin ‘Yan PDP

Published

on


Wasu daga cikin manya kuka jiga-jigan jam’iyyar PDP ada, sun bayyana cewa daga cikin dalilan da suka sa suka kuma jam’iyyar APC sun hada da amincin da suke da shi na cewar gwamna Aminu Masari Mutumin kirkine.

Wadannan kalamai dai sun fito ne daga makin Kwamared Bilyaminu Mohammed Rimi tsohom mataimaki kakakin majalisar dokokin jihar Katsina da ya sauya sheka  daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Kwamared ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da wakilin Leadership Ayau a Katsina lokacin gagarumin bikin karbar wadanda suka sauya shekka daga PDP zuwa APC a wanda shugaban jam’iyyar APC na kasa John Oyegun ya halarci bikin da ya gudana a filin wasan Dawaki da ke Katsina.

Tsohon mataimakin kakakin majalisar ya ce yana mamakin yadda gwamna Aminu Bello Masari yake girgmama su, amma da ya yi dogon tunani sai kawai ya gano Masari haka Allah ya yi shi, yana son jama’a kuma yana ba su girma.

Kazalika ya ce duk mutumin da ya ke ganin  jama’a da kima babu dalilin da zai sa ba zai yi tafiyar sa ba ko wanene, akan haka ya shiryawa tarnakin makiya wanda  ya ce tuni suka fara bin shi na sharri da kage, amma acewarsa wannan ba zai hana ya taimaki gwamna Masari ba a siyasa.

Ya kuma kara da cewa idan aka duba yanayin yadda wannan siyasar take tafiya dole sai mutane irinsu sun kama an yi tafiyar da su, ba don komi ba,  sai domin al’ummar da suke tare da su.

Ya ce kafin ya dawo jam’iyyar APC yana da jama’a da dama, kuma sun ki tafiya ko’ina suna jiran su ji yana ra’ayinsa ina ya karkata, ya kara da cewa abisa la’akarin da jiga-jigan jam’iyyar APC a karamar hukumarsa ta Rimi suke yana da matukar mahimmanci su a gaza domin cimma nasarar da ake bukata a siyance.

‘’yanzu idan ka duba mutanen mu suna da bukatar hanyoyi da asibitoci da makarantu da sauran kayayyakin more rayuwa, wanda yanzu haka gwamnati na iyakar kokarinta, amma saboda an rasa wadanda za su tsaya masu wajan ganin an samar da wadannan kayayyaki yadda ya kamata  domin amfanin jama’a dole mu shiga saboda al’umma’’ in ji

Shi kuwa da yake tofa albarkacin bakins tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina honarabul Ya’u Umar Gwajo-Gwajo cewa ya yi dalilansa na komawa jam’iyyar APC sun fi karfi a rubuta a jarida daya saboda mahimmacin su.

Ya ce matsayinsa na dan siyasar da baya gudun jama’arsa dare da rana suna tare da mutane babu dalilin da zai sa ba zai bi gwamna Masari ba tunda shi ma haka yake, jama’a ce gabansa ba mulkin ba.

‘’Ni a ganina ana yin shugabanci ne saboda jama’a kuma idan ka duba bakin daya jama’a ne faban Masari, duk wani mai kishin al’umma dole ne ya bi tafiyar Masari domin samun nasara a gwamnatance, saboda haka Masari mutumin kirki ne.

 


Advertisement
Click to comment

labarai