Connect with us

LABARAI

PDP Reshen Katsina Ta Dirar Wa Kalaman Oyegun

Published

on


Jam’iyyar PDP ta nuna rashin jin dadinta dalilin maganar da shugaban jam’iyyar mai mulki John Oyegun saboda kiran jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta ‘’mutu’’.

Oyegun ya ce dalilin da ya sa ya bayyana hakan saboda manyan jami’an da suka bar jam’iyya, suka koma jam’iyyar APC wannan ya nuna karshen jam’iyyar ke nan da sauran wasu.

Da yake magana lokacin da ake taro a Katsina Oyegun ya tabbata cewar APC ita ce jam’iyyar da take numfashi, sauran kuma sun mutu a Katsina.

Ya kara bayyana cewar yadda wasu mutane ke fita daga jam’iyyar suna komawa  gwamnatin APC , da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shugabanta, ga shi kuma yana aiki tukuru. Abin da kuma shi ke ke jawo hankalin mutanen su koma APC.

Amma kuma shugaban jam’iyyar na jihar Katsina a wata ganawa da ya yi da manema Labarai a Katsina, cewa ya yi, bayanan da Oyegun ya fada, babu kanshin gaskiya, saboda PDP tana da karfinta a jihar Katsina.

Abin da Oyegun ya gani ai ba wani abu bane illa ‘yuan tsirarrun mutanen da aka gaiyato bayan an biya su kudi, daga Zamfara da kuma wasu Jihohi na kusa, ya kara da cewar ba wani abu ne illa bugun kura da gwado wanda ake yi.

‘’Ta yaya za ayi jihar data fitar da shugaban kasa daga jam’iyyar PDP ace ta mutu, wannan ai ba gaskiya bane, ba kuma za a yadda da hakan ba’’.

Majigiri yana nufin maganar da Oyegun ya yi bayan da aka yi zaben  cike gurbi, wanda ita jam’iyyar PDP take kalubalanta, daga sakamakon da Hukumar zabe ta bayyana, ba ta yadda za a ce wannan jam’iyya ta mutu, ai ko ma yawan kuri’un da muka samu aka gani ba mai iya cewar PDP ta mutu a jihar Katsina.

 


Advertisement
Click to comment

labarai