Connect with us

WASANNI

Ozil Ya Kafa Sabon Tarihi A Gasar Firimiya

Published

on


Kwallon da Mesut Ozil ya taimaka Shkrodan Mustaphi ya zura a ragar Watford tasa zuwa yanzu dan wasan ya taimaka an zura kwallo 50 a gasar firimiya tun zuwansa kungiyar Arsenal.

Arsenal ta doke Watford da ci 3-0 a wasan mako na 30 a gasar cin kofin firimiya da suka kara a ranar Lahadi a filin wasa na Fly Emirates dake birnin Landan.

Arsenal ta ci kwallo ne ta hannun Shkodran Mustafi kuma kwallo ta dubu daya (1,000) da kungiyar ta zura a raga a firimiya a filin wasanta, bayan da aka dawo daga hutu Pierre-Emerick Aubameyang ya ci na biyu.

Saura minti 14 a tashi daga fafatawar Arsenal ta kara kwallo ta uku ta hannun Henrikh Mkhitaryan wanda yakoma kungiyar a watan Janairu daga kungiyar Manchester United

Watford ta barar da bugun fenariti, bayan da Petr Cech ya buge kwallon da Troy Deeney ya buga kuma shine karo na farko da mai tsaron ragar ya buge bugun fanareti a kungiyar tun bayan shigarsa daga Chelsea

A karawar farko da kungiyoyin biyu suka yi a gasar a ranar 14 ga watan Oktoban 2017, Watford ce ta yi nasarar cin Arsenal 2-1.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta shida a kan teburin firimiya da maki 48.

Watford za ta karbi bakuncin kungiyar Bournemouth a ranar 31 ga watan Maris, yayin da Arsenal da Stoke City za su kece-raini a ranar 1 ga watan Afirilun wannan shekarar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai