Connect with us

LABARAI

Matan Dapchi: Mun Amince Da Yin Sulhu – Iyayen Matan

Published

on


Iyayen dalibai matan garin Dapchi wadanda aka sace su kwanakin baya sun nuna matukar farincikinsu ganin yadda Shugaba Buhari yake gudanar hanyoyin da za a bi don yin nasarar ceto ‘yan matan tare da yin sulhu domin ganin an ceto daliban.

Wasu daga cikin iyayen sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai NAN yau a garin Damaturu cewa kokarin da shugaban kasar yake na ceto daliban ya kara masu kwari gwiwa kan kubuto daliban.

Shugaban kungiyar iyayen daliban makarantar Alhaji Bashir Manzo, ya nuna matukar goyon bayansa ga gwamnati na ceto daliban don bin hanyar sulhu ba wai kawai da karfin bindiga ba hakan zai sa a sako daliban cikin koshin lafiya.


labarai