Connect with us

MANYAN LABARAI

Matan Dapchi: Amurka Za Ta Jagoranci Sulhu Da Boko Haram

Published

on


…Yau Iyayen Matan Chibok Za Su Ziyarci Garin

A jiya ne Sakataren Kasar Amurka, Rex Tillerson ya bayyana cewa, akwai fata na gari dangane da kokarin da ake yi na ceto dalibai matan garin Dapchi wadanda kungiyar Boko Haram ta sace su kwanakin baya.

Sakataren na Amurka ya ce, za a bi hanyoyin sulhu domin ganin an ceto daliban.

Mista Tillerson ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan sun kammala wata ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Sakataren Kasar ta Amurka ya jaddada cewa, suna matukar ba Nijeriya goyon baya da duk wani taimako da take bukata don ganin an ceto dalibai matan Dapchi da takwarorinsu na Chibok wadanda kungiyar Boko Haram ta sace. Ya ce, daga cikin tallafin na su ga Nijeriya akwai na bayar da horo, kayan aiki da sauransu.

Ya ce; “Da farko dai muna yabawa matakan da gwamnatin Nijeriya ke dauka dangane da lamarin. Mu ma kuma muna taimaka musu da duk wani taimako da ya dace don ganin an magance wannan matsala.

“Mu na sa ran za a ceto dalibai matan ta hanyar bin hanyoyin sulhu cikin ruwan sanyi ba da karfi ba. Wanda muke fatan a ceto su cikin gaggawa ba da jimawa ba.” inji shi

A wata sabuwa kuwa, iyayen dalibai matan makarantar Chibok, wadanda har ya zuwa yau din nan ba a ji duriyar su ba, tun bayan da ‘yan ta’adda suka sace su daga makarantar kwanan su ta Chibok, da ke Jihar Borno, sun shirya kai wata ziyarar jimami ta musamman a yau din nan, ga takwarorin su na garin Dapchi, wadanda su ma ‘yan ta’addan suka sace masu ‘yan mata 110 a watan da ya wuce.

A karshen makon nan ne iyayen yaran na Chibok suka shaida wa majiyarmu cewa, sun shirya ziyarar ne domin jajantawa iyayen yaran na Dapchi, kasantuwar sanin yanayin da suke a ciki a halin yanzun.

Mista Yakubu Nkeki, da Uwargida Yana Galang, Shugaba, da kuma Shugabar mata, na kungiyar yaran da aka sacen na Chibok, a yau din nan ne  za su jagoranci tawaga ta wasu daga cikin iyayen su talatin wadanda har ya zuwa yanzun ba a ga ‘ya’yan na su ba, domin su kai ziyarar ta jajantawa a garin na Dapchi.

“Shugaban mu, ya rigaya ya yi magana da Shugaban iyayen yaran na Dapchi, da kuma Shugaban Karamar Hukumar Bursari, inda ya sanar da su aniyar tamu ta kai masu ziyarar jajantawan na mu,” in ji Uwargida Galang.

Ta ce, za mu je ne mu zauna da su, mu saurare su, mu kuma tattauna da junanmu a kan yanda za mu tarbi juyayin kasantuwar har ya zuwa yanzun ‘ya’yan namu suna hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Amma ta ce, duk da haka, za su tafi da wasu daga cikin wadanda aka rigaya aka samo ‘ya’yayen na su, domin su karfafa masu gwiwa da sa ran kubutar ‘ya’yan na su watarana.

 


Advertisement
Click to comment

labarai