Connect with us

RAHOTANNI

Matan Chibok Da Dapchi:  Ana Ci Gaba Da Musayar Yawu Tsakanin APC Da PDP

Published

on


A ranar Asabar din data gabata ce, jigajigan jam’iyyar APC suka yi kakkausar suka akan sace ‘yan matan makarantar Chibok da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi a shekarar 2014, inda kuma irin wannan lamarin ya maimaita kansa bayan ‘yan kungiyar sun sake sace wasu ‘yan mata ‘yan makarantar Dapchi a watan da ya gabata daga makarantar su dake cikin

jihar Yobe.

Dukkannin jam’iyyun biyu, suna sukar junan su akan sace ‘yan matan a matsayin gangamin na siyasa don cimma wata manufa ta siyasa.

A bangaren jam’iyyar PDP, ta suki APC akan gazawar jami’an tsaro, inda hakan ya janyo aka sace ‘yan matan ‘yan makarantar Dapchi da kuma yin siyasa da ruyuwar ‘yan matan.

Wannan sukar da PDP ta yiwa gwamnatin APC mai mulki, ya janyo ita APC ta mayar da martani a bisa zargin PDP wadda tana kan karagar mulki a shekarar  2014, wajen yin amfani da siyasa akan jinkirin kwato ‘yan matan makarantar Chibok.

Jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewar, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dauki matakin gaggawa a ranar sha tara ga watan Fabirairu akan sace ‘yan mata ‘yan makarantar Dapchi su 110 da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi daga makarantar su.

APC ta ce, sabanin sace ‘yan matan makarantar Chibok su 276 da ‘yan kungiyar ‘yan Boko Haram suka yi a ranar sha hudu ga watan Afirilun shekarar 2014 a jihar Borno a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, gwamnatin ta Jonathan ta dinga yin amfani da siyasa da karyatawa har ‘yan ta’addar suka samu sukunin sace ‘yan matan da kuma boye su a mafakar su.

Shugaban kasa Buhari kuwa, a sanarwar da ya fitar a ranar ashirin da uku na watan Fabirairu, kwana hudu da sace ‘yan matan ‘yan makarantar Dapchi bayan da labarin sace ‘yan matan ya riske shi ya bayar da umarnin gaggawa wajen tura tawaga ta musamman don zuwa garin su ganewa idon su.

Ya kuma kara bayar da umarni” da a tura hukumomin jami’an tsaro zuwa yankin don tabbatar da an gaggauta gano ‘yan matan ‘yan makarantar Dapchi da kuma cafko ‘yan ta’addar don su fiskanci hukunci.”

Bugu da kari, Shugaba Buhari ya sanar da cewar,“Gwamnatin sa ta kara tura dakarun sojji da jiragen yaki masu saukar Angulu don sanya ido akan dukkan wani motsin ‘yan ta’addar a yankin har na zuwa tawon awa ashirin da hudu a kullum da fatan gano ‘yan matan”.

Amma a martanin da jam’iyyar PDP ta yi akan ikirarin na APC ta ce, APC bata yi adalci akan maganar sace ‘yan mata ‘yan makarantar Dapchi ba.

Sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar PDP Mista Kola Ologbondiyan ya shedawa majiyar  mu a ranar Asabar data ganata cewar,  “ni da ku kunsan basu mayar da wani  a cikin gaggawa akan abinda ya auku a makarantar Dapchi ba domin da farko, sun karyata cewar an sace

‘yan matan”.

Ya yi nuni da cewar, maganar da ake yi a yanzu ita ce, basu mayar da martani akan tambayar mu ba ta akan wane dalili ne yasa suka kwashe jami’an tsaro da aka girke a makarantar?“

Kola ya kara da cewa, har yanzu basu mayar da martani gamsasshe ba da ‘yan  Nijeriya zasu gamsu ba.

Ya bayyana cewar, a bisa magana ta gaskiya, tambaya akan janye jami’an tsaro kafin sace ‘yan matan kwata-kwata baiyi kama da zargin da ake yiwa PDP akan rashin duba bukataun ‘yan mata ‘yan makarantar ba.”

Kola ya kara da cewa, akan ikirarin APC,“shin basu dauki nauyin ragamar shugabancin kasar nan a shekarar 2015, ‘yan matan Chibok nawa ne suka kubutar dasu? Kuma me yasa suke yin siyasa da rayukan ‘ya’yan mu mata? Kuma me yasa suke yin amfani da rayukan ‘yan Nijeriya? Shin wannan shine alkawuran da suka yiwa ‘yan Nijeriya a lokacin yakin neman zabe na shekarar 2015?”

Shima tsohon Mataimakin Shugaban kasa  Atiku Abubakar, wanda ada dan jam’iyyar APC ne wanda daga baya ya canza sheka zuwa jam’iyyar sa ta da PDP a ranar uku ga watan Disambar  shekarar 2017 bayan da ya taimaka aka kafa APC, ya yi tsokaci akan sace ‘yan makarantar ta Dapchi.

Atiku a ranar Asabar data gabata ya soki  APC, akan sukar data yi na sace ‘yan matan Chibok da kuma yadda gwamnatin APC ta yi sakaci aka sace ‘yan makarantar Dapchi don biyan bukatar ta na siyasa da kuma kushen da APC ta yi akan sace ‘yan matan Chibok duk da kokarin da gwamnatin PDP ta yi a wancan lolacin wajen kubutar da ‘yan matan Chibok.

Ya yi nuni da cewar nuna halin ko in kula da gwamnatin APC ta yi shine ya janyo sace ‘yan matan na Dapchi.

A cewar Atiku, “ bari inyi amfani da wannan karin magar rasa sace ‘yan matan da ‘yan Boko Haram suka yi kamar kara  sake rasa rukuni daya ne na ‘yan matan saboda irin sakaci na gwamnatin APC.

Ya ci gaba da cewa, a baya lokacin APC tana jam’iyyar adawa, tana akan gaba wajen yin suka akan sace ‘yan matan Chibok.“

Ya ce, APC ta yi suka sosai akan tsohuwar gwamnatin Jonathan,inda suka hana gwamnatin Jonathan sakat, duk da kokarin da take yi akan kubutar da ‘yan matan Chibok.

Ya yi nuni da cewa, abin mamaki ne ace mutanen da suke ta faman yin suka akan gwamnatin data gabata akan sace ‘yan matan Chibok sai gashi suma a karshin gwamnatin su, sun bari an sace ‘yan matan Dapchi guda 110.”

A cewar sa, “tuni ina sane cewar ‘yan  Boko Haram suna da wata kulalliya a boye don durkusar da neman ilimin Boko a kasar nan.”

Ya ce, wanne dali ne yasa aka bar makarantar ba tare da an girke jam’ain tsaro ba?.

A martanin da Sakataren yada labarai na kasa na  APC Mallam Bolaji Abdullahi ya yi kuwa, ya danganta zage-zargen Atiku akan marasa makama balle wani tushe, inda ya ce, mai makon tsohuwar gwamnatin PDP ta Jonathan ta kubutar da ‘yan matan Chibok, sai da buge da yin wasa da rayuwar su ta siyasa.

Abdullahi ya ci gaba da cewa, akan maganar sace ‘yan matan Chibok “bana tsammanin cewar APC tana wasa da rayukan su domin wannan maganar ba gaskiya bace.”

Ya ci gaba da cewa na biyu kuma, a bisa maganar gaskiya sace ‘yan matan Dapchi, lamari ne da ya ciwa ‘yan kasar nan fuska, amma akwai banbanci a tsakanin sace ‘yan matan Dapchi dana sace ‘yan matan Chibok, musamman akan martanin da gwamnatin APC ta yi.

“In za’a iya tunawa, a lokacin da aka sace ‘yan matan Chibok gwamnatin PDP ta wancan lokacin ta karya hakan.

Abdullahi ya ce, saida ta kai Gwamnatin PDP sati biyu kafin ta amince da an sace ‘yan matan Chibok din.

Ya ce, amma ita wannan gwamnatin ta mayar da martani a cikin gaggawa ta hanyar tura tawaga ta musamman da tura manyan jami’an tsaro da kuma kafa kwamitin bincike.

A cewar sa, “idan kana neman jam’iyyar da take yin wasa da rayukan ‘yan matan wanda wannan abune da ya shafi harkar tsaro ta ko wanne dan Nijeriya, Atiku ya zargi PDP wadda a wancan lokacin ta dinga zargin gwamnan jihar Borno  Kashim Shettima, da  APC mai makon PDP ta mayar da hankalin ta wajen kubutar da ‘yan matan Chibok.

Abdullahi ya yi nuni da cewa, ko Atiku yana ganin kafa kwamitin da gwamnatin APC ta yi da kuma daukar matakan gaggawa da gwamnatin APC ta yi tana yin siyasa ne da rayukan ‘yan matan na Dapchi?”

Ya bayyana cewar, daga cikin ‘yan matan Chibok su 276 da aka sace guda hamsin da bakwai sun samu arcewa, an kuma kuma gano hudu, inda kuma aka sako guda dari da uku kuma har yanzu ana neman guda dari da sha biyu.

Mahukunta sun yi ikirarin cewar, an kubutar da wasu ‘yan matan Dapchi, amma daga baya aka gano maganar ba haka take ba.

Har ila yau, a ranar Asabar data gabata rundunar shakwatar Soji ta kasa ta sanar da cewar, rundunar Soji ta kasa da kasa dake a gefen tekun  Chadi tana daya daga cikin jami’an Soji da suka himmatu wajen neman ‘yan matan na Dapchi.

Shalkwatar ta kuma sanar cewar, ta dauki dabarun yaki wajen ganin ta kubutar da ‘yan matan na Dapchi.

Daraktan yada labarai na shalkwatar Birgediya Janar John Agim ya shaida wa majiyar mu akan hadin kan da suke samu daga sojojin hadaka na kasashen kamar na kasar Nijar da Chadi wajen neman ‘yan matan na Dapchi.

A cewar sa,“muna gudanar da aiki kada da kada da sauran jami’an soji na kasa da kasa kuma suma dukkan su suna cikin tawagar ceto ‘yan matan wanda Nijeriya ke jagoranta.

Agim ya ce, ”akan yanayin neman ‘yan matan a yanzu koda yake alummar gari suna son su san sakamakon Sojojin suna yin dukkan mai yuwa don a kubutar dasu.“

A cewar sa, har yanzu muna kan neman ‘yan matan don mu kubutar dasu ta hanyar daukar dabarun yaki.”

Gwamnatin tarayya ta yi shela a satittukan da suka gabata cewar, an fadada neman ‘yan matan zuwa sauran kasashe dake makwabtaka da Nijeriya don a kubutar dasu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai