Connect with us

WASANNI

Liverpool  Ta Ce Real Madrid Tabiya Fam Miliyan 142 Na Muhammad Salah

Published

on


Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta ce Real Madrid sai ta biya zunzurutun kudi har fam miliyan 142 idan har tana son ta dauke Muhammad Salah daga kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Salah dai yafara buga wasa a kungiyar Liberpool da kafar dama tun bayan komawarsa kungiyar daga Roma inda ya zura kwallaye 32 cikin wasannin daya bugawa kungiyar ciki kuwa akwai kwallaye 24 daya zura a gasar firimiya.

Kokarin dan wasan ne yaja hankalin manyan kungiyoyin nahiyar turai ciki har da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wadda bata kokari a gasar laliga kuma ake saran za tayi garambawul cikin yan wasanta na gaba.

Rahotan ya bayyana cewa Liberpool ta shirya karbar kudi fam miliyan 160 sama da yadda ta karba a hannun Barcelona a lokacin cinikin Coutinho watakila ma ta bukaci adadin kudin da PSG za ta biya Monaco wajen siyan Kylian Mbappe.

Sai dai watakila shugaban gudanarwar kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez ya canja shawara akan Salah din yakoma kan Mauro Icardi ko Robert Lewandowski ko kuma Edin Hazard da kungiyar ta dade tana nema.

Real Madrid dai ta kai wasan kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun turai sannan kuma tana mataki na uku akan teburin laliga na kasar sipnaiya.


Advertisement
Click to comment

labarai