Connect with us

LABARAI

Limamin Babban Masallacin Kasa Ya Bukaci Kungiyoyin Addini Su Yi Rajista Da CAC

Published

on


Limamin Babban massallacin kasa da ke Abuja, Dakta Kabir Muhammad, ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da su tabbatar da yin rijinta da hukumar da ke da alhakin yin rijista wa kungiyoti wato ‘Corporate Affairs Commission (CAC)’.

Imam Muhammad ya bayyana cewar babu yadda za a yi ake tafiyar da al’amura ba tare da bin doka da oda ba.

Ya bayar da wannan shawarar ce a lokacin da ke rufe gasar karatun Alkur’ani karo na biyu wadda ‘Islamic Promotion Initiatibe of Nigeria da hadin guiwar ‘Turkiye Diyanet Foundation of Republic of Turkey’ suka shirya a birnin tarayya Abuja.

Ya ce, ya kamata a ce ya zuwa yanzu kowace kungiyar addini ta yi rijista da hukumar ta Corporate Affairs, hukumar da ke kula da harkokarin kungiyoyi a Nijeriya domin su samu zarafin gudanar da dukkanin harkokinsu a bisa doka da kuma yadda ya dace, ya kara da cewa yin hakan zai bayar da dama wa shuwagabanin addini su ke kaucewa wa kuskure.

Imam Kabir ya ke cewa, “Ina shawartar kungiyoyin addini da sauran kungiyoyi da su tabbatar da yi rijista da hukumar da ke kula da wannan na gwamnati domin su samu zarafin gudanr da shirye-shiryensu ba tare da shan wahala ba,”

Ya ce, “Kungiyoyinmu ta yi rijista da CAC a 2014, mun samu takardar shaidarmu ne a 2015, don haka; muke samun zarafin gudanar da harkokinmu da tsare-tsarenmu ba tare da wata matsala ba,” A cewar Muhammad.

Da ya juya kan gasar karatun na Alkur’ani kuma, Imam Muhammad, ya nuna gamsuwarsa sosai da yadda mahalarta gasar karatun suka hallara, da kuma yadda gasar ta samu karbuwa cikin nasara.

Ya kuma yi bayanin cewar, wadanda suka samu gagarumar nasarar s biyu, za su wakilci birnin FCT a kasar karatun kur’ani na kasa na mata wadda zai gudana a garin Sokoto, bayan nan kuma su ne za su sake wakitar Nijeriya a gasar karatun na kasa da kasa wadda ke ci gaba da gudanuwa a kasar Turkey, Tanzania da kuma Egypt.

Ko’odineta na shirin, Dr Abdulkadir Muhammad, ya sanar da cewar Suraiya Mohammed, daga yankin Gwagwalada, itace ta lashe kambun gasar na bana 2018 a sashin gasar na mata baki daya, inda kuma Nuhu Ibrahim, wadda ya fito daga jihar Kogi, ya lashe gasar a bangaren mazan.

Ko’odineta Muhammad, ya bayyana cewar biyu daga cikin wadanda suka samu gagarumar nasarar da kuma wasu su ne za su wakilci kungiyar a gasar kur’ani wadda za a yi na duniya wanda zai hada kasashe da dama a sassan duniya.

Haka kuma, ya jero sauran wadanda suka taka gagarumar rawa a wannan gasar da aka fafatan, yana mai cewa Abdulrahaman Bunu daga Borno; Suleiman Lawal daga Katsina; Mohammed Suleman; Khadija Suleman daga Abuja yankin Municipal, har-ila-yau,  Hassana Umar daga yankin Abaji, Maryam Suleman, Fauzia Shehu da kuma Huraira Mohammed sune suka samu gagarumar nasara a gasar da aka fafatan na wannan shekarar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai