Connect with us

TATTAUNAWA

Kwankwaso Jagora Ne Mai Kwatanta Adalci -Hajiya Balaraba

Published

on


HAJIYA BALARABA IBRAHIM ita ce shugabar kungiyar Siyasa da wayar da kai ta Kwankwaso Tsohuwar mai ba da shawara ce a kan harkokin ma’adinai a Gwamnatin Kwankwaso ta dora a kan ta Ganduje wanda daga bisani aka ba wani mukamin nata. A wannan hirar da ta yi da IBRAHIM MUHAMMAD a Kano, ta bayyana mana shigarta siyasa da abubuwanda suka biyo baya zuwa wannan lokaci. Ga yadda hirar ta kasance.

Hajiya Balaraba Ibrahim kina daga shugabanni a mata masu biyayya ga manufofin Sanata Dokta Rabiu Musa Kwankwaso, za mu so mu ji, ta yaya ma kika shiga harkokin siyasa?

Bismillahi Rahmanir Rahim. To ya aka yi na shiga siyasa yau dai ina da shekara 14 tun a 2003 na fara siyasa da yake na yi zaman Saudiyya to tunanin da zai sa in dawo gida in zauna in daina zaman Saudiyya shi ya sa na shiga siyasa, sai kuma na duba a lokacin siyasar da ake siyasa ce ta dabbanci ana bai wa yara kwaya da makamai saboda biyan bukatar ’yan siyasa, to wannan lokaci sai muka tashi kungiya “Kano political awareness group”Muna wayar wa da matasa kai a kan su daina yarda ana amfani da su ana biyan bukata. Saboda idan ka duba matasan nan su ne jigon tafiyar siyasa wanda su za a yi amfani idan bukata ta biya, mutumin da ka amfana wa gaisuwa ma ta gagara. Shi ne sai muka kirkiri wannan kungiya ana nan daga baya aka buga gangar siyasa sai muka dauki Aminu Dabo a matsayin dan takara saboda karko da muka ga yana da shi na wajen taimaka wa al’umma, sannan a wannan lokacin mun sami labarin cewa hatta da mai wankin takalma da mai fura da suke zaune a kofar ma’aikatar filayen sai da aka ba su kyautar filaye. Sai muka ga cewa, to me zai hana mu tallata shi saboda ya zo ya zama Gwamna a wannan lokacin tunda Allah shi ke ba da mulki, sai Allah ya kaddara ba shi ba ne.

Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya tsaya ya zama gwarzo ya ci takara sai aka ce shi yana da gutsiri tsoma a je a dawo aka tsai da Ahmad Garba Bici muka zo muka fadi wannan zabe sai da aka zo kuma 2011. A 2018 kungiya ta yi tunanin cewa ya kamata ta jajirce ta tsaya da kafarta wajen Dokta Rabiu Musa Kwankwaso shi ne muka dauki kungiyar muka mayar ta koma “Kwankwasiyya”Political Awareness Group” Saboda ya yarda da ita ya tabbatar da cewa, wannan kungiya tasa ce kuma babu rawa a cikinta, wannan shi ne kadan daga yadda na zo na shiga siyasa har muka ci kuma Gwamnati 2011. Shi mai girma Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya ba ni mai ba shi shawara a kan ma’adinai wanda aka tafi Alhamdu lillahi an yi nasara an yi tafiya an gama lafiya.

Wace jam’iyyar siyasa kenan kika soma siyasarki?

Da PDP na fara siyasa kuma ban taba fita na bar ta ba, har sai da jagora ya ce a fita a bar ta, tunda ni biyayya nake kuma ina da akida da ra’ayi duk abin da nake ina jajircewa a kansa.

To kasancewar kin taho a waccan Gwamnati ta Kwankwaso har zuwa wannan Gwamnati ta Ganduje kwatsam sai aka daina jin duriyarki a Gwamnatin wane dalili ne ya jawo hakan?

E, to dalilan sunada yawa, a gaskiya wanda yake ko lokacin ma da shi Ganduje ya ba ni aiki sai da na je na sanar wa da shi jagora cewa, to mai girma Gwamna na yanzu ya mai da ni ofis din da ka fara saka ni, saboda ya ga amanata a wajen, kuma yana da sha’awar ya ci gaba da aiki da ni. Ya ce da kyau ai duk daya ne. Allah ya ba da sa’a. Allah ya yi jagora, ki je ki kai takardunki kamar yadda suka bukata kuma haka aka yi da kuma aka mai da ni ofis na sake komawa na sanar da jagora cewa ga shi-ga shim, ya ce to ba komai duk daya ne, maganarsa dai guda daya ne, duk daya ne, Allah ya ba da sa’a , ban taba zuwa mishi da wata magana ya kawo min sabanin haka ba, sai dai ya ba ni hakuri ya rarrashe ni. To har aka zo ana ta gutsiri- tsoma tun ba mu fahimci akwai matsala ba, har muka gane cewa akwai matsala, amma tsakani da Allah Gwamna Ganduje da ya dawo da ni ofis ya ba ni ba ni da matsala da shi, na kuma gode mishi, saboda kauna ce ta sa shi ya yi haka. To amma kuma da tafiya ta yi tafiya, sai ya zamana cewa akwai matsalolin da shi ya kasa ya tunkare ni ya yi magana da ni, shi mai girma Gwamna Ganduje sai ya kasance ana min cune, sai dai a cuna wannan ya taba ni, a cuno wannan ya taba ni, ni da shi in mun hadu babu wannan maganar.

To ni kuma a tunanina kai da ka kira ni ni da kai ka ba ni aiki, idan akwai matsala ni da kai ya kamata ka kira ni mu tattauna ta ko meye in kana so za a iya yi maka. To amma in da ya zamana cewa an sami wani shiri wanda bai ma san me ake yi ba, to ka san akwai matsala. To a wannan lokaci koda Ganduje ya ba ni aiki ban bar Kwankwaso ba, zai wahala na yi sati biyu ban je na gaishe shi ba. In ka ga ban je ba, to ko banda lafiya ko aiki ne ya rike ni. Kuma a cikin wannan sabgar yana raina zan je ko gaishe shi ne in yi, takan kama in tashi daga Kano har Abuja in je, wallahi ina wuni ina gajiya ba za ta samu tsakanina da shi ba, saboda sabga amma dai ya gan ni na gan shi ni bukatata ta biya, saboda na gan shi lafiya. To karamar sallah sai na je na gaishe shi sai ya kasance abu ne da ake yi mishi buki, kowa da kowa yana tura sako, in ka hana naka ya yi, ba za ka hana na wani ya yi ba. To su nan din sai suka gan ni. To ni dama ban cire jan mayafina ba, dan ba dalili kuma ni dama ko Kwamkwaso da jana ya same ni, ya yi kara kalar ne a kai kuma ya kara min son jan. amma ni dama tun ina karama, launin da na fi so shi ja, tunda suka nuna ba sa son jan mayafi, to ni shi karan kansa Gwamnan a wannan lokacin da ja a kansa kuma har yanzu jar hula tana kansa, to mene ne illar jan mayafina tunda inai maka aiki tsakanina da Allah ba na cin dunduniyarka kuma ba abin da zan cewa Allah sai godiya saboda har na yi aiki da Kwamkwaso na gama, na yi aiki da Ganduje na gama bangaren da ya shafi aikina ba a taba zanga-zanga ba ko korafi ba, duk sanda korafi zai zo Allah zai taimaka za mu je mu yi maganinsa. To amma yau sai ga shi an wayi gari ina barin ofis ko wata uku ba a yi ba sai da ’yan yashi suka yi zanga-zanga. To saboda haka ka ga me za mu ce wa Allah? sai godiya.

To ganina a wajen Kwankwaso sai aka ce dan me ina nan ina can? Sai na ce a’a nan aiki nake yi kuma tsakanina da Allah nake. Can kuma fa? Na ce ra’ayina ne, wanda ba ni da Gwamna aka yi wannan ba. Ni da Abdullahi Abbas muka yi wannan. “To idan can ne ra’ayinki mu nan ne ra’ayinmu”. Na ce bambancin ra’ayi shi ya sa Allah ya bambanta tsakanin dan’adam, addini ma kowa nasa yake, kuma Allah bai kashe Kirista ba dan ba ya Musulunci. Akwai ma kwata-kwata wanda bai damu da samuwar Ubangiji ba, amma Allah ne ya halicce shi. To sai na ga cewa ai ra’ayi ne, ’yancina ne, idan za ka ce ga abin da zan yi maka ba da rarrashi ba, da karfa-karfa to wallahi ba ka isa ba. Shi ya sa sai na ce ba zai yiwu ba. To a wannan lokacin kai da ka ba ni aiki ya kamata ka kira ni in ka ji nan ka ji can, to tunda ba ka ji ba, sai aka tafi a haka. Ni ban rubuta takarda na bar aiki ba, shi bai rubuta ya sallame ni ba, ya dai dauki ofis ya bayar da shi, to har yanzu a cikin haka ake.

Wannan ya nuna ke nan misali, da tun farko an yi kiran ki an yi maslaha da ke za ki ci gaba da bin Gwamnati?

Ai, rai dangin goro ne, shi komai dan rarrashi ne, ko danka ne yau in za ka yi masa hawan kawara, gobe ka yi, jibi ka yi, sai ya ba ka kunya wata ran. To ko mene ne, koda ba zan bi Gwamnati ba, hakki ne nashi, tunda ni da shi ya kira ni a wayata ya ba ni aikin, ya kamata ya fita hakkina ya zo ya ji mene ne ya faru daga bakina, amma hakan ni alhamdu lillahi ya zame min alheri saboda yanzu abubuwa da suke faruwa, koda ma hakan bai farun ba, ni a yanzu na bar su dan ni zuciyata ba za ta dauka ba, cin amana da jagwalgwalo da yadda abubuwan da suke faruwa ba su dace ba, alakar mutuncina yau da gobe da kake tare da mutum, ko guga ba ta ci tsirar komai ba, ta ci na igiya. Idan yau ban raga maka ba, ai yau shekara 16 kana tare da mutum ai ya kamata ku raga wa juna. Kuma me yake nema ne? Gandujen ba Gwamna ba ne? Kuma bai samu ba? Kwankwaso ya isa ya yi mishi ne? Bai isa ya yi mishi ba. Allah ne ya yi mishi, komai za a yi a rayuwa ta duniya Allah ne yake yi, yana abubuwansa da lokaci ne. Lokacin da Ganduje yake ganin ya kamata ya zama Gwamna bai zama ba. Kwankwaso ya zama Allah ne ya yi zai zama, yanzu Allah ya kaddara yake so ya zama kuma ya zama. To me kake nema? Babu wani abin da kake nema. Irin wadannan abubuwa suna taba zuciyata shi ya sa alakarka ma ta mutum da mutum, ka ga idan dai da Kwankwaso da Ganduje a ce za a wayi gari a cikin wannan karni to babu wani dan’adam da yake da wata alaka da ba za a wayi gari a ce an gaji ba.

To yaya kike gani za a iya sulhunta wannan lamari da yake akwai manya da suke kai komo dan ganin an sami sasanci?

Manya daga sama da suke kokarin a sasantawa wai in har akwai su din, ai ta gaba ta rago ce, ta baya ta malalaci, ihu ne bayan hari. Tunda an riga an bar abin ya lalace ya jagwalgwale tunda in kana ganin bakin zaren ga inda za ka jawo to yanzu gaba daya ya zama nema babu abin da za ka iya gani. In ka ce in za ka yanka ta nan tsinkewa za ta yi, saboda haka ina ganin abin nan dama imma da sama ko yadda kake cewa, manya ka ce sun shigo ko?To da saninsu aka yi, kuma ba su san za ta kazance haka ba, to yanzu ta kazance. To yanzu ai fadan ba na Kwankwaso da Ganduje ba ne, saboda kasa ta dauka, kuma kasa ta fi sama yawa. Wallahi to muma mun dauka muna nan muna zura ido mu gani Kwankwaso zai shirya da Ganduje shi shi kadai su biyu su yi harkarsu ko kuwa a’a muma muna da hakki? Muma muna da hakki saboda duk wanda ya taba masoyinka ya taba ka, mu duk abin da Kwankwaso yake so muna son shi, duk abin da yake ki mana kin sa, wannan zance haka yake. Kai! Ba ka jin ma maganganun da Ganduje yake fada? Yau ake maganar za a yi sulhu tun maganar ba ta kai hakan ba. Yau idan ka zo ka yi maganar sulhu gobe sai ka ji wata.

Kamar yau fa aka kwashi Gwamnoni guda shida ko bakwai aka je har da Ganduje aka sami Kwankwaso a gidansa na Maitama da maganar cewa a yi sulhu, kamar yau da dare washe gari fa da safe Ganduje bayan duk wani mai mukaminsa na Kano ya sa ya shiga Abuja, bayan an je an ce wannan abu ba daidai ba ne muna ’yan’uwan juna abokan juna wane ne-wane ne kawai washe gari sai Ganduje ya ja mu muka tafi ofishin jam’iyya ya je ya ce ga Abdullahi Abbas shi ne shugaban jam’iyya ya kuma sake kawo karar Kwankwaso. To kararsa name? A duk duniya ban taba tunanin cewa wai ai Ganduje ba yaro ba ne, idan an gaya mishi ko an ce ya kamata ya yi amfani da hankalinsa ya kamata ya duba alakarsu. Wai mahaifiyar Ganduje ta rasu wai Kwankwaso ya debo ’yan iska maimakon su je su yi mishi ta’aziyya wai sun je suna ta zazzagin shi. Wane irin tunani ne zai dauki wannan. Na gindinsa dama suna nan wadanda suke so haka ta faru, idan ba haka aka yi ba su ba za su ci abinci ba, su suka yi amfani da wannan dama na shigowarsa. Tunda shi ya tafi ya sa kafarsa ya tafi shi bai shigo garin nan ba, sai da aka yi mutuwa da aka yi mutuwar ma da yaya ya shigo?

Zan yi amfani da wannan dama in fada wa Kwankwaso daga yanzu babu wani da da zai yi Gwamna a jahar Kano da za ka tafi ka bar jahar Kano, ka ce ka ba shi dama ya yi Gwamnatinsa. Yin hakan ta kawo ga shi nan zai shiga ya ga al’ummarsa, ya ga iyayensa, ya yi zumunci, ya yi siyasa, suka yi ta kulle-kulle aka hana shi shigowa shi kadai ne sanata? Ko shi kadai ne ya taba Gwamna a Kano. Kabiru Gaya ba ya yi Gwamna ba, yanzu ba sanata ba ne, ba ya shigowa? Saboda mene ne saboda cin amana. To babu wani da da zai kara zama Gwamna a Kano da Kwankwaso zai ba shi iska ya ce ya ki shigowa cikin jahar Kano wannan daga kan Ganduje ta kare.

Mene ne shawararki ga ’yan siyasa musamman ma magoya bayan Kwankwaso?

To shawarata ita ce, duk mai kaunar Sanata Kwankwaso ya zama wajibi ya je ya yi rijistar zabe, domin duk irin kauna da kake wa Kwankwaso, to idan ba ka da katin zabe soyayyarka ba za ta zama mai amfani ba, domin da wannan katin ne za ka zabe shi a duk wani matsayi na ya fito, saboda haka ya zama wajibi masu kaunar ci gaban kasar nan su yi katin zabe da za su zabi mutane masu kishi da son ci gaban al’umma irin sanata Kwankwaso.

Ina kuma shawararki ga sauran ’yan siyasa a kasar nan?

Shawara da zan ba ’yan siyasa sama da kasa ita ce su ji tsoron Allah, su kuma dubi Allah, su kuma tunada cewa duk wata kujera da suke hawa kai su zauna. al’umma ne suke kai su, wadannan al’ummun kuma wallahi hakkinsu ne in mutun daya ya kwana da yunwa Allah sai ya tambaye su, tunda hakkinsu ne, amma ba su damu da wannan ba, kuma tun daga Duniya Allah zai fara tambayar su, ba sai sun je lahira ba. Ai ga shi nan muna gani nan aka ce ’ya’yan da Kwankwaso ya kai karatu kasar waje aka ce ’ya’yan iska ne ’yan’wiwi. Malamai sun ce idan ka ga dan wani yana lalacewa to yi masa addu’a ba ka kara tagayyara shi ba, sai ka gani a cikin gidanka.

Kuma abin da ya zo ya fada sai Allah ya bayyana shi a aure rawar da amarya za ta fito fili ta tsaya sai an zo kawayenta suna jajjawo ta ta ki yi, amma ke kadai kike fiye da kowa ana kallon ki Duniya duk ta gan ki. To wallahi wannan kalubale ne ga shugabanni, idan ’ya’yanmu suna lalacewa ku tattara su ku killaces u ku nemar musu shiriya da abin yi. Shi ya sa Kwankwaso sai ya yi makarantar Kiru banda wannan ma akwai wasu guda uku da aka yi cibiyar gyara hali. Inda ake gyara yara masu shaye-shaye saboda kusan gidan kowa da shi. Gama-gari ne, amma kai a matsayinka na shugaba, wanda yake kowa a karkashinka yake, amma ka zagi ’ya’yan talakawa da su suka zabe ka, ka zama abin da ka zama. Ba ka musu addu’a ba ma, ka ce wai ’yan wiwi ne. To ina ’yan wiwin suke? An gan su. To ina ranar wannan abu. Yan siyasa ku yi wa Allah da Annabinsa kar ku ci amanar al’ummar da kuka dauka. Idan kuma ba ku rike ba g aku nan ga Ubangiji. Kuma shi ya sa Kwankwaso ya fita daban da su ko ba komai yana kwatanta adalci.


Advertisement
Click to comment

labarai