Connect with us

KIWON LAFIYA

Kasafin Kudin 2018: An Bukaci Gwamnatin Filato Ta Muhimmanta Kiwon Lafiya

Published

on


Bayan ’yan awo’wi kalilan ya rage a yi ban kwana da shekarar 2017 a shiga sabuwar shekara ta 2018, inda tuni wadansu gwamnoni suka fara mika kasafin kudaden da za su kashe wajen yi wa al’ummominsu aiki ga majalisun dokokin Jihohinsu don amincewa. An bukaci gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin jihohi 36, dake cikin fadin kasar da su fi ba da fannin kiwon lafiya da ilmi, muhimmanci don taimaka wa masu karamin karfi daukar nauyin iyalansu.

Daya daga cikin Dattawan da ke da burin ganin mulkin Dimokradiyya ya dore a kasar nan kuma shugaba ’yan kasuwa reshen babbar kasuwar Bukur da ke jihar Filato, Alhaji Zubairu Shehu ne, ya yi wannan kira a lokacin da yake sharhi a kan kasafin kudi da gwamnonin ke mika wa ’yan majalisun dokokin jihohinsu don amincewa a yi wa al’umma aiki da su a shekara mai zauwa ta 2018.

Alhaji Shehu, a zantawarsa da wakilimmu a garin Bukur hedkwatar karamar hukumar Jos ta Kudu, a karshen wannan mako ya ce ya zama wajibun wa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su fi ba da mahimmanci a fannin kiwon lafiya da ilmi don saukake wa al’umma yin jinya da ilmantar da iyalansu. Ya ce, yanzu jinya ta fi karfin magidanta saboda a Asibitocin gwamanati, inda magidanta masu karamin karfi suke saran samun magunguna a cikin rahusa. Ya ce, a yanzu idan ka je wadansu Asibitocin gwamnati din za ka ga dan karamin kudin da suke bukata maras lafiya ya ajiye kafin a fara yi masa jinya shi ne N50,000.00, wanda wannan din ma ya ce ba zai isa ba idan ka zo sallamarsa.

Alhaji Shehu, ya ce, haka batun yake a wajen ilmi idan magidanci yana da yara fiye da uku, a makarantar Sakandare ba zai iya daukan nauyinsu duka ba, idan ya tashi biyan kudin makaranta musamman in yaran sun kai su rubuta jarrabawan fita makaranta.

 


Advertisement
Click to comment

labarai