Connect with us

KASUWANCI

Jihar Legas Za Ta Gina Gidaje Dubu 20 Nan Da Shekarar 2020

Published

on


Gwamnatin jihar Legas na shirin gina gidaje 20,000 nan da shekarar 2020 domin cika gurbin gidaje Miliyan uku da ake bukata a fadin jihar, kwamishinan gidaje na jihar Mista Gbolahan Lawal, ne ya bayyana haka a yayin da yake zagaya aikin gina gidaje na Odo-Onosa/Odo Ayandelu a Agbowa na karamar hukumar Ikorodu ranar Lahadi.

Kwamishinan ya ce, binciken da aka gudanar kwanan nan a jihar ya nuna cewa, kashi 65 na al’ummar jihar matasa ne saboda haka gwamnati ke kokarin gaggauta samar da gidajen da zai amfani wadannan matasan masu tasowa.

“Hankoronmu shi ne cika gurbin da muke da shi na gidaje a jihar tare da hadin hannu da kanfanoni masu zaman kansu, mun tsara shirin ne a karkashin tsarin “Lagos Affordable Public Housing” muna son samar da gidaje 20,000 kafin shekarar 2020 da hadin hannun kanfanoni masu zaman kansu” inji shi.

Mista Lawal ya ce, gwamnati ta shirya samar da yanayin aiki da kuma filaye a matsayin nata gudummawar domin cima wannan hankoron.

“A halin yanzu muna aiki tare da kanfanoni masu zaman kansu guda 10 mun fara da gidaje 4,404, muna sa ran shigowar wasu kanfanonin nan gaba domin fadada aiyukan”

“Fatan mu shi ne cike gibin gidaje miliyan uku da muke da shi ta hanyar samar da gidajen tare da la’akari da kuma lura tsarin gwamnati na samar kudaden gine-gine”.

“Muna aiki a kan samfurin gudaje da dama, wadanda da zasu zaburar da ‘yan jihar Legas su nemi mallakar gidaje na kansu” inji kwamishinan.

A cewar sa, rukunin gudaje na Odo-Onosa/Odo da ke da gidaje 660 an tsara duk wanda ya karba haya zai iya mallakar gidan daga karshe an kuma kai kashi 65 na kammala aikin ginin.

Ya kuma bayyana cewa, kashi 70 na kayan aikin da ake gudanar da aikin ginin an samo ne daga cikin gida kuma ‘yan kwangila na cikin gida 34 ke gudanar aikin ginin”

“Muna fatan ‘yan kwangilan za su gudanar da aiyukansu yadda ya kamata, mu kuma zamu tabbatar da ana biyasu kudaden su cikin lokaci domin karfafaf su domin mu samu cimma wa’adin kamala aikin”

“A halin yanzu an kammala kashi 60 zuwa 65 na aiyukan gidajen, muna fatan nan da zango na hudu wato tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba na 2018 za a kammla aiyyukan gaba daya”

Inji shi.

Daga nan ya umurci jami’an ma’aikatansa dasu gaggauta biyan ‘yan kwagilan da suka nuna kwazo a aikinsu domin a karfafa musu.

Gwamnatin jhar Legas dai ta kirkiro da shirin ne in da mai haya zai iya mallkar gidan da yake haya a ranar 8 ga watan Disamba 2016, shirin ya kunshi mutane masu karamin karfi daga bangaren kanfanoni masu zaman kansu da ma’aikatan gwamnati, in da mai haya a cikin wadannan gidajen zai ci gaba da biyan kudin gidan a cikin shekara 10.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai