Connect with us

KIWON LAFIYA

Hatsurran Yin Amfani Da Man Girki Ba Tare Da Lura Ba

Published

on


Man kwantirola ana amfani dashi wajen dafa dukkan nau’in abinci a duniya. Yana dauke da sanadarin da ake afani dashi wajen sarrafa shi.

Yana da kyau mai amfani dashi ya kiyeye akan irin hanyar da ake ake sarrafa shi da kuma irin sanadarin da ake sanyawa wajen sarrafa shi.

Irin dandanon sakamakon saboda sanadarin dake cikin sa, musamman a kasar nan, ya tabbatar da cewar ana sanya sanadarin  (hedane) wajen sarrafa man.

Mun yanke shawarar bayani don fadakar da alumma akan don su kiyeye mun kuma samar da tsare-tsare ga masana’antun da suke sarrafa irin wannan man don su zabi kayan da ya dace wajen sarrafa man, musamman don kare lafiyar mutane masu yin amfani dashi dake dauke da sanadarin (hedane), domin yin amafani da man ba’a bisa ka’ida ba, zai janyo matsala ga lafiyar mutane.

Wannan man da muke amfani dashi a kullum wajen girka abinci, yana dauke da sanadarai.

Ya zama wajibi mu ke yaye akan irin sanadaran da ake amfani dashi wajen sarrafa shi.

Sanadarai da ake amfani dashi wajen sarrafa man, zai iya shafar lafiyar mu kuma ya kamata alumma su alumma su masu amfani dashi, suka jajirce wajen sayen man na gari.

Muna amfani da man daga kashi sha hudu zuwa ashirin bisa dari a kullum a cikin abincin mu.

Akwai irin wannan man da ban-da-ban  da ake sayarwa, wadanda suka hada da, mai na waken soya dana (canola) da man gyada da suran su.

Kasar nan, ta kasance a gaba wajen samar da manja kuma mai sauki haka ya samu karbuwa a fadin duniya.

Man da ake sarrafawa yana dauke da sanadarai masu karfi wajen fitar da mai daga cikin iri ana kuma tattara iri sannan a goge dattin dake jinsa sai kuma gurje shi.

Irin da aka gurje ana tafasa shi akan yanayi tsakanin 110˚ zuwa 180˚kafin a fara tatsar sa.

Ana gasa irin daga kwabsar da aka fitar daga man sannan a matsa man daga irin.

Anan kuma ake hada irin da man sannan a sanya su hade da sanadarin (phosphate) sai kuma a fara raba man da irin.

Idan an gama tsane man kuma sai a ware in ya gama dafuwa.

Daga baya kuma ana yin amfani da irin wajen sarrafa abincin dabbobi.

Ana kuma sarrafa man ta hanyar wasu kamar canza launin fatar jiki da sauran su.

Sanyawa man ruwa:

A wannan hanyar ana sanyawa man ruwa har zuwa wani lokaci sannan kuma a ware shi.

A yayin wannan sarrafawar, ana fitar da wasu sanadarai da dama.

Mayar dashi yadda yakamata:

Duk wani maiko da sauran sanadarai ana fitar dasu daga cikin man. Man da aka sarrafa shi kalar sa bata da nauyi.

Canza launi:

Babban dalilin da yasa ake canza launi shine, don a cire wasu sanadarai dake cikin man.

Man da aka dafa ana gyara shi wajen cire wasu sanadarai da ba’a bukatar su.

Man da aka sarrafa shi ana kiran sa mai da aka sarrafa shi kuma ana yin amfani dashi a koda yaushe.

Mafi yawancin man girki a kasar nan da ya shiga kasuwa, ana samar da shi ne daga manja.

Babbar matsalar dake shafar lafiyar mutane, an lura aka kuma ji shi ne na yin amfani da sanadarin (gasoline) wanda wani sanadari ne na man fetur da aka sarrafa shi.

Ana amfani da sanadarin (SRG) mai makon yin amfani da sanadarin (Hedane) saboda saukin da yake dashi.

Sanadarin (SRG) yana dauke da sanadarin(isomers) da sanadarin (butane) da kuma sanadarin (sulphur). Duk wadannan sanadaran suna da illa ga lafiyar mutum.

Sai dai, saboda matsatsin tattalin arziki, ana amfani dashi wajen sarrafa man.

Magance sanadaran da ake sanyawa a cikin man, nauyi ne akan gwamnati da hukumomi.

Muna kira ga gwamnati data sanya ido sosai akan irin wadannan sanadarai da kamfanoni ke sanyawa a cikin man da suke sarrafawa don kare lafiyar alumma.

A ko wanne lokaci idan zaka sayi man girki, ka tabbatar da ka sayi man da zai kara maka lafiya.

Man baida wata takamai-man ka’ida da aka sanya masa a jikin galan, kuma zai yi wuya ga mai amfani dashi su fahimci sanadarin da yake cikin sa.

A saboda haka, yana da mahimmanci kamfanonin da suke sarrafa irin wannan man, su magance wannan matsalar.

Kuma dole ne mahukunta su sanya a dinga bincikar kamfanonin da suke sanya irin wadanan sanadaran.

Maduagwu Kulkarni shine shugaban masana’antun Andra dake kasar nan kuma kwararren injiniya ne bugu da kari, yana aiki a sashen sayar da kaya da rarraba su a wani kamfani dake a Houston  kasar Amurka.

Shi kuwa Meshram yana da babban digiri na M.Sc kuma shine shugaba a. Sashen sanadarai na kamfanin TATA dake jihar Legas.


Advertisement
Click to comment

labarai