Connect with us

WASANNI

Harry Kane Zai Yi Jinya Bayan Raunin Da Ya Ji A Kafarsa

Published

on


Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewa Sarkin kasar Katar, Tamim Bin Hammad ya umarci shugaban kungiyar kwallon kafa ta PSG cewa kada ya sake ya siyar da dan wasa Neymar ga kowacce kungiya a kakar wasa mai zuwa.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tana zawarcin dan wasa Neymar tun bayan komawarsa kungiyar daga Barcelona a watan agustan shekarar data gaba akan kudi fam miliyan 200 wanda hakan yasa yafi kowanne dan wasa tsada a duniya.

Tun bayan komawarsa kungiyar ta PSG rahotanni suka bayyana yadda yafara samun sabani da wasu daga cikin yan wasan kungiyar ciki har da Edinson Cabani wanda rigimarsu ta fito karara duniya tasani

Real Madrid dai tana ganin Neymar zai maye mata gurbin Cristiano Ronaldo wanda ake ganin zai bar kungiyar kowanne lokaci daga yanzu sai dai wata kila cinikin yayi wahala sakamkon saka baki da sarkin na Katar yayi.

Neymar dai yayi wasanni 20 inda kuma ya zura kwallaye 19 a gasar rukuni-rukuni ta kasar ta Faransa kuma bai buga wasa na biyu ba da kungiyarsa ta PSG ta sha kashi a hannun Real Madrid a gasar zakarun turai.

 


Advertisement
Click to comment

labarai