Connect with us

WASANNI

Babu Tabbas Ko Pogba Zai Iya Buga Wasan Mu Na Yau, Inji Mourinho

Published

on


Mai koyar da tawagar yan wasan Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa bashi tabbas din cewa ko dan wasan kungiyar Paul Pogba zai iya buga wasan da kungiyar za ta karbi bakuncin Sebilla a filin wasa na Old Trafford a wasan zakarun turai a yau.

Mourinho ya bayyana hakane a wata hira da manema labarai inda yace har yanzu bashi da masaniya akan ciwon dan wasan saboda likitocin kungiyar sune suke kula da ciwon saboda  ba aikinsa bane.

Sai dai yace zai tattauna da dan wasan yaji ko zai iya buga fafatawar ko kuma bazai buga ba inda kuma ya kara da cewa ba abun damuwa bane idan bai gama murmurewa ba saboda bazai yi amfani dashi ba idan bai murmure ba sosai.

Manchester United dai za ta karbi bakuncin Sebilla kwanaki hudu bayan ta doke Liberpool a wasan firimiya kuma a satin daya wuce ta doke Chelsea da Crystal Palace a wasannin firimiya wanda hakan yake nufin kungiyar tana kan ganiyarta kawo yanzu.

Mourinho yaci gaba da cewa wasan Liberpool  da suka buga bai kai wasan da zasu buga da Sebilla da kuma Brighton Albion ba a wasan cin kofin kalubale na FA zagaye na kusa dana kusa dana karshe.

Yaci gaba da cewa wasan Liberpool wasa ne kamar na kowanne sati banbancinsa kawai shine wasan adawa ne amma koda ace sunyi rashin nasara zasu iya cigaba da buga gasar amma wasan Sebilla idan sukayi rashin nasara sun fita daga gasar sai shekara mai zuwa sannan shima wasan Brighton Albion idan sukayi rashin nasara shike nan.

Sai dai yace duka wasannin zasuyi iya kokarinsu wajen ganin sun samu nasara inda kuma yace yan wasansa a shirye suke dasu fafata domin samun nasara.

A yau ne dai Sebilla za tayi tattaki har filin wasa na Old Trafford domin fafatawa da Manchester United a wasan zagaye na biyu na cin kofin gasar zakarun turai bayan sun buga 0-0 a wasan farko da suka buga a kasar sipaniya sati biyu da suka gabata.

 


Advertisement
Click to comment

labarai