Connect with us

LABARAI

AYEM AKPATUMA: Masarautar Kagara Na Bukatar A Samar Da Barikin Soja

Published

on


Rundunar soja ta 31 da ke minna ta shirya taron masu ruwa da tsaki kan yadda za a samar da tsaro a yankunan Kagara, Munya da Shiroro dan dakile barazanar masu garkuwa da mutane da satar shanu. Rundunar ta shirya taron ne a karkashin yaki da ta ke da baragurbi mai taken farauatar mage da ya ke gudana yanzu haka a jahohi shida na kasar nan.

Shirin wanda aka fara shi sha biyar ga watan biyu ana sa ran kammala shi talatin da daya ga watan uku. Taron ya gudana ne a babban dakin taro na zamani na tunawa da Abu Lolo da ke cikin garin Kagara.

Tunda farko da yake bayani, wakilin shugaban rundunar soja ta kasa, Birigediya Janar A. M Adetayo shugaban  bataliya ta talatin da daya da ke minna, ya bayyana cewar wannan taron tattaunawa tsakanin fararen hula da soja an shirya shi dan samar da shawarwarin yadda za a iya bunkasa tsaro a yankunan da garkuwa da mutane da satar shanu yafi shafa, yace aikin na daga cikin kudurin aikinsu na kakkabe batagari a cikin al’umma.

Don haka jama’a su baiwa jama’a shawarar su baiwa rundunarsa da sauran jami’an tsaro hadin kai ta yadda za su samu nasarar kawo karshen batagari da ke kokarin hana zaman lafiya a wannan yankin.

Honorabul Gambo Tanko Kagara ( Bojo) shi ne shugaban karamar hukumar ta Rafi, ya bayyana cewar duk wani basaraken da aka samu da sauke wani bako ba tare da yin bincike ba kuma aka gano bakon nan mugu ne lallai bakin rawaninsa.

Yace sarakunan gargajiya wato hakimai da masu unguwanni na da rawar takawa a harkar tsaro, ya zama wajibi inda duk aka samu wani bako da yake bukatar zama kasar Kagara, lallai da masu unguwanni su kyautata bincikensu akan shi kafin amincewa dan kai shi gaban hakimi ta haka ne zamu hana dama ga mutanen da ba su dace ba zama cikin mu.

Karamar hukuma ta yabawa maigirma gwamna kan hadin kai da ya bayar da samar da zaman lafiya a wannan yankin, su kansu jami’an soja da aka turo dan yin wannan aikin sun nuna dattijantaka wajen gudanar da ayyukansu, domin yadda suke gudanar da aikin ba dare ba rana kuma ba tare da samun tangarda ba abin a yaba ne.

Da yake gabatar da kasida a taron shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) reshen jihar Neja. Kwamared Muhammed Muhammed ( Sa’in Gunna) ya jawo hankalin mazauna bangarorin da suka fi fuskantar wannan barazanar na satar jama’a yadda zasu baiwa rundunar soja hadin kai ta yadda za a bunkasa tsaro a yankin. Haka ya bayyana cewar haduwar fararen hula yau ya tabbatarwa jama’a cewar soja na kowa ne kuma yana aiki ne dan kare muradun kasa da samar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Kwamared Muhammed yace ya zama wajibi mu taimakawa jami’an tsaro da shwarwari da kuma tsegunta duk wani matsugunni da muka san akwai mugu zaune domin kawar da shi a cikin mu, yace rundunar tana kokarin nunuwa jama’a cewar ba ta iya samun nasara a dukkanin aikinta dole sai tare da hadin kansu, Don haka ina jawo hankalin ‘yan uwana mazauna karkara da duk wani tsari da rundunar ta AYEM AKPATUMA ta zo da shi da su bi shi sau da kafa har su kawo karshen wa’adin aikinsu a wannan yankin.

Shugaban na NUJ ya jawo hankalin karamar hukumar Rafi da ta cigaba da baiwa rundunar hadin kai da goyon baya dan samun nasarar wannan aikin.

Masarautar dai tana da gundumomi goma tana daya daga cikin yankunan da suka fi fama da satar mutane dan yin garkuwa da kuma samar da mafaka ga barayin shanu wanda zuwa yanzu ana gab da kakkabe su a wannan yankin.

Da yake jawabi, mai martaba sarkin kagara, Alhaji Salihu Tanko da ya samu wakilcin Hakimin Kwangwama, Alhaji Idris Jibrin ya bayyana cewar idan ka taso daga kasa Kontagora inda ke da barikin soja, ka shi kasar Kagara zuwa Birnin Gwari akwai manyan dazuka guda uku da suka kunshi dajin Kwangwama da ke masarautar Kagara sai Alawa da ke masarautar Minna wadda iyaka ce da masarautar Kagara sai dajin Birnin Gwari wanda ke cikin masarautar Birnin Gwari a jihar Kaduna, ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da barikin soja dan inganta tsaro a wannan yankin.

Masarautar tayi alkawarin cigaba da baiwa jami’an tsaro hadin kai dan ceto rayukan jama’a da dukiyoyinsu daga hannun bata gari.

A ‘yan watannin baya muna kwana ne da Ido daya saboda fargaba akan garkuwa da mutane da ya yawaita a wannan yankin, yau dan kankanin lokaci da zuwan soja kuma abin ya kusa zuwa karshe. Don haka ina kira amadadin masarauta ga duk wani mai rike da rawani da ya kara zage dantse wajen ganin ba sa ke mayar da hannu agogo baya ba.

Duk wata damuwa mu gaggauta sanar da masarauta ita kuma ina da tabbacin za ta mika rahoton ta ga karamar hukuma dan daukar mataki kan kari.

Taron dai ya samu halartar dukkanin bangarorin tsaro da kuma sarakunan iyayen al’umma daga kan hakimai, dagattai da masu unguwanni da shugabanni manoma da makiyaya da ke yankin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai