Connect with us

KASUWANCI

An Samu Tangarda A Noman  Masara A Jigawa

Published

on


Manoman rani na bana a jihar Jigawa ya fuskanci koma bawa sakamakon karancin manfetur,inda hakan ya janyowa manoman rani a jihar da suke yin amfani da injinin ban ruwa suka rage yawan noman na rani da suke yi.

A saboda hakan ne aka yi kirdadon cewar yawan amfanin gonakai da ake san ran za’a samu in anyi girbi, zai sauka kasa matuka saboda tashin gwaron Zabo da manfetur ya yi a jihar saboda rashin issasun kudi a gun manoman don sayen man.

Mafi yawancin manoman ranin suna zaune ne a karkara, saboda basu cika shige cikin birane ba don sayen man a farashin da gwamnati ta yanke ba.

Manoman sun dogara ne kacokam akan man da suke saye a gun ‘yan bunburutu, inda kuma ‘yan bunburutun suke sayar da man akan rfarashi daga naira 250 zuwa naira 300 ya kuma danganta akan inda suka je sayo man.

Bugu da kari, manama wadanda ke  zaune a yankuna masu nesan gaske, suna sayen man ne a farashin da aka tsawalla saboda kai man irin wadannan yankuna, farshin na man ana kara rubanya shi.

Sai dai, a wani bincike da aka gudanar a wasu gonakan a kauyen Miga da karamara hukumar Birnin Kudu, ya nuna cewar duk da karin na farashin man bai sanya manoman ranin sun sun rage fadin ginakan su ba, amma, amma wasu manoman ranin tsadar ta man ta sanya su jingine aikin noman ranin dingurungun.

Mafi yawancin wasu manoman ranin sun tsunduma sana’ar yin Achaba don kare mutuncin su dana iyalan su da kuma ware wani dan kasafi don zubawa gonakan su.

Saboda dinbin tsadar kula da noman ranin tunma kaffin karancin man, wasu manoman basa noma manyan gonakan su saboda yadda gonakan suke da girma haka kuma ya kamata a nome su.

Duk da cewar manoman suna shukawa da kuma girbe amfanin gona iri-iri, a gonakan su da ban-da-ban, manoman suna noma a kalla gonakai  biyu ko hudu akan ko wanne amfanin gona yadda zasu iya kula dasu.

A bisa noma kadada biyu ko uku, abinda manomi yake bukata itace lita uku ta mai kuma a wani lokacin manoman suna dogaro ne akan injinan ban ruwa masu inganci.

Yin amfani da injinan ban ruwa na tsohon ya yi, suna shan litar mai hudu akan ko wacce kadada.

Yawan nauyin yanayin noman ranin ya danganta ne akan karfin kasar noma na rike danshi saboda yadda ake yin ban ruwa sau biyu ko sau uku a sati, ya kuma danganta akan yadda kasar noman zata iya rake ruwan.

Daya daga cikin manoman mai suna Malam Sani, wanda ada yake noma kadada hudu ta Masara ,a yanzu baya iya kula da koda kadada daya a noman rani na bana, inda ya danganta hakan akan tsadar mai da kuma ci gabada kula da ginar sa.

Sani ya ci gaba da cewa, a baya yana kashe naira 12,000 wajen sayen mai wajen yin shuka da kuma yin girbi, wanda yake kai shi tsawon watanni uku.

Malam Sani ya kara da cewa, hakan ya sanya dole ya jingine noman ranin a gefe bayan da ya kirba yawan kudin da yake kashewa akan sayen mai kawai.

A cewar sa, yanada gonakai biyu, masu girma daya, inda a daya yake noma Shinkafa dayar kuma yake noma Masara,inda ya ce dole ta sanya a jingine noma gonar Masara ya mayar da hankali ga gonar Shinkafa.

Ya bayyana cewar,  eben the rice farm, harda ita gonar ta Shinkafa indan wasu abubuwa na halin rayuwar yau suka bijjiro masa, zai iya jingine noman na Shikafa.

Sani ya ce,” idan ta faru a hakan zan jingine gonar ta noman Shinkafa kamar yadda na jinge noman ginar Masara, ganin yadda suma makwabtana manoman Shinkafa suke yanke shawarar jingine gonakan su na noman Shinkafa, akan saboda nima bazan iya noma ginata ta Shinkafa ba.”

Akan dalilin da yasa ba zai iya yin noman ba kuwa, Sani ya yi nuni da cewa, idan kana yin noman rani a cikin manoma da yawa, gonar ka shan ruwa kadan ne da kuma rike danshi har zuwa tsawon lokaci domin duk ranar da baka yi noman ranin ba, makwabcin dake kusa da gonar ka danshin ginar ka zai gangara ko ina.

Shi ma wani manomin  mai Abdulhadi Isa dake kauyen Maiganjara a cikin karamar hukumar Miga an ruwaito yana cewa, a baya yana noma kadada biyu ta Masara a gonar, amma a yanzu ya zamar masa dole ya rage kadada daya da rabi saboda tsadar mai.

Ya ce koda yake bai yi lisafin ko nawa yake kashewa ba kafin ya yi girbi ba, amma ya san a wannan karon komai ba zai samu a yadda yake ba, inda hakan ya sanya ya yanke shawarar rage fadin gonar sa.

Ya ci gaba da cewa, yana yin noman rani ne sau biyu a sati kuma yana sayen lita biyu har zuwa uku na mai ya danganta da bukatar ban ruwan kuma tsadar man da yake zubawa injinan na ban ruwa, yana shafar ‘yan kudin da yake ajiyewa.

A cewar sa, shekara mai zuwa ba zai koma yin noman ranin ba koda farashin mai ya sauka in har farashi amfanin noman bai daidai ta a wannan shekarar ba, inda sai idan farashin ya daidaita ne, manoman zasu iya riba mai amfani.

Isa ya ce, shekarar data wuce, ya samu amfanin noma kimanin buhu sha biyar, amma saboda rage fadin gonar sa da ya yi a yanzu, baifi ya samu buhu shida zuwa bakwai ba.

Ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa dasu kawo masu dauki ta hanyar taimaka masu da mai.

“A shekarar da ta gabata kimanin  mutane dari 300 mazuna kauyen mu na Maiganjara, suka tunduma a cikin noman rani na Masara amma a wannan shekarar, saboda tsafar mai da ya kai kimanin kashi saba’in bisa dari, ba za su iya yin noman na rani ba”.


Advertisement
Click to comment

labarai