Connect with us

RA'AYI

Abdulrazak Danfulani: Murucin Kan Dutse…

Published

on


Wani abin takaici ba kasafai al’umma ke fahimtar mutanen kirki masu taimakawa saboda Allah ba, illa nadiran. Irin wadannan mutane sun a da na a boye, sai a wasu lokutta ake saninsu. Kuma masu iya magana na cewa, ‘Babban abin da ya fi muhimmanci a rayuwa shi ne gudumuwar da mutum ya bayar, ba wai yawan shekarun da ya yi a duniya ba.’

Shi ya sanya mutane irinsu Alhaji Abdulrazak Abdulsalam Danfulani, wanda aka fi san da Danfulani & Sons a garin Kaduna suka ciri tuta, kuma su ka kafa tarihin da ba kasafai ake kafa irinsa ba, musamman a wannan lokacin da rashin gaskiya da tausayi da kishin al’umma suka mamaye rayuwar yau da kullum.

Danfulani & Sons mutum ne matashi mai matsakaitan shekaru, domin yana da shekaru 44 da haihuwa, dan asalin jihar Kano. Bayan karatun muhammadiyya mai zurfi, ya fara aiki da wani mutumin Kasar Labanan, a wani kamfanin gine-gine. Da Ubangidan na sa ya aminta da gaskiyarsa da rikon amanarsa, sai ya tafi da shi zuwa Kasar Labanan a lokacin da zai koma Kasarsa bayan ya gama ayyuka, inda ya ci gaba da ayyuka da shi a can har na shekaru uku 3.

A can ne ya koyi harshen larabci bakin gwargwado da kuma haduwa da mutanen arziki daban-daban.

Yana can ne, sai mahaifansa suka bukaci da ya dawo gida, domin a tunanin tsaffi suna ganin ya yi musu nisa, hakan ya sanya ya dawo gida, cikin rufin asiri na ban mamaki. Da yake shi mutum ne mai ladabi da biyayya ga na-gaba da shi, ba ma kamar iyayensa ba, wannan biyayya da ya yi ta dawowa gida, kusan ana iya cewa ita ce tushen nasarar sa.

Da ya dawo gida ne sai ya koma garin Kaduna da zama ya ci gaba da sana’ar zirga-zirgar ababen hawa, watau sufuri da Babura da kananan motocin haya.

A zamansa Kaduna, ya fuskanci ibtila’o’in da yawa, wadanda cikin ikon Allah da tawakkali da shi, ya ga bayansu daya bayan daya. Wannan ya yi daidai da fadar Khalifa Imam Ali Bin Abi Talib (AS) cewa, ‘Kada ka ga mutum mai yin alheri da tausayin jama’a ya shiga cikin matsayi, ka tsammaci cewa, karshensa ke nan. A’a, zai sake farfadowa har ma ya wuce yadda yake a da.’

Da yake Allah ba ya rufe kofa ga bawa, ya kuma sanya sakata, sai Allah cikin ikonsa ya hada shi da wata mata, wadda ta ba shi amanar baburanta na haya, wadanda su ne tushen farfadowarsa da arzikinsa a halin yanzu.

Da ma can bayan ya dawo garin Kaduna yana yin sana’ar hayar Babura ne. Wannan amanar da yake rike da ita ta sanya a yau din nan , shi ne babban mai kamfanin zirga-zirgar ababen hawa dangin Keke NAPEP mafi girma da daukaka a duk fadin jihar Kaduna. A halin yanzu, ya yi rijistar kamfaninsa Danfulani & Sons da Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Kasa, watau Corporate Affairs Commission CAC. Bayan harajin da yake ba gwamnatin jiha, a halin yanzu ya samarwa matasa akalla dubu 1000 ayyukan yi a duk fadin Kaduna da masauran jhohin Kano da Katsina da Abuja.

Bugu da kari, saboda ficen da yadda ya tsunduma a harkar sufuri da Keke NAPEP ka’in da na’in, hatta Kamfani Bajaj na Kasar Indiya ya san da zamansa, da sanya shi cikin manyan dillalan sa a Kasar nan. A duk fadin Arewacin kasar nan, Danfulani & Sons shi ne akan gaba wajen sayeda sayarwar Keke NAPEP a wurin kamfanin Bajaj na Kasar Indiya. Sau biyu a jere, Kamfanin yana aiko injiniyoyi da kanikawan Keke NAPEP sun a zowa garin Kaduna inda suke koyar da kanikancin Keke NAPEP, yadda ake gyara da hada shi kyauta, ba tare da ko sisin kobo ba.

A shekarar 2016 da 2017 sun zo yadinsa dake NDA Bus stop kusa da Gombe Jewel Hotel, inda suke bayar da horon. “Wannan gagarumar nasara ce ga Kasar nan. Don haka, yana da kyau gwamnati ta tallafa wa wannan dan taliki, don ya ci gaba da samar da ayyukan da kwarewa ga matasanmu, a harkar sufurin Keke NAPEP da harhada shi da gyaransa. Ida har aka samu hakan, to anan gaba, na tabbata Abdulrazak Danfulani zai bunkasa al’amarin ta yadda zamu rika hada shi kamar yadda Kamfanin Peugeot na Kasar Faransa suka kafa kamfani a Kakuri suna hada motoci a cikin kasar nan, to haka matasanmu za su rika hada Keke NAPEP a cikin wannan jihar,” in ji wani Babban dan kasuwa, Alhaji Salihu Maijam’a a zantawa da manema labarai.

Da na zanta da wani mai aiki da Keke NAPEP dinsa, Jabiru Musa dan shekaru 33, ya shaida ma ni cewa, “Tsakani na da Danfulani & Sons sai godiya da girmamawa da addu’ar fatan alheri. A dalilin Keke NAPEP din da y aba ni, na y i aure, na sai filin da zan gida gidana, ina ciyar da kai na da iyalina da mahaifiyata. Ya kamata gwamnati ta jawo irin wadannan mutane a jiki, ta tallafa musu domin suna dauke ma ta nauyin samar da ayyuka ga matasa,” in ji shi. Akan haka ne wani kuma, Malam Salisu Dan’asibi wani magidanci, cewa ya yi,”A  gaskiya, Alhaji Danfulani & Sons mutumin arziki ne sannan ga tausayi da kishin al’umma matuka. Allah ya saka masa da alherinsa amin. Yana da kyau al’umma su fahimci ayyukan wannan dan taliki da kuma jinjina masa.”

Abin sani ne duk wata gwamnati wadda ta san abin da ya dace, wajibi ne ta godewa mutanen dake ke taimaka ma ta ta fita hakkin al’ummarta.

Akan haka ne, Shugaban Hukumar Tabbatar da Bin Dokokin Hanya da hadurra ta jihar Kaduna, watau KASTELEA, ya y aba Danfulani & Sons, ya kuma bayar da tabbacin Hukumar na tallafa masa, a harkar zirga-zirgar ababen hawa a cikin jihar ta Kaduna, a yayin da ya ga wani labarinsa wanda wannan jaridar ta wallafa a satin da ya shude.

A kokarinsa na kulla kyakkyawar alaka da gwamnatocin Arewacin Kasar nan, musamman jihar Kaduna, Danfulani & Sons zai kai ziyarar ban girma ga huumomin da wasu ma’aikatun gwamnati, cikin har da jami’an tsaro da kafofin yada labarai a nan gaba. “Wannan ayyukan da muke yi, muna yi ne saboda Allah da kishin al’umma da kuma jihar Kaduna da kasa baki daya.

Don haka, babban al’amari shi ne a tsare gaskiya da rikon amana da cika alkawali, sannan da yin ladabi da biyayya ga na-gaba. Wannan shi ne sirrin nasarar da al’umma ke ganin mun samu.”

A karshe, ayyukan Abdulrazak Danfulani & Sons abin koyi ne da jinjinar ban girma, domin mutum ne wanda ya faro yanayi na gaskiya da rikon amana da biyayya, sannan ga tausayi da kishin al’umma. Sana’ar haya da Babura wadda daga baya ta rikide zuwa Keke NAPEP ta fitar da kyawawan halayensa a fili, inda bayan samun karbuwa daga Kamfanin Bajaj na Kasar Indiya, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa sama da 1000 a jihar Kaduna da makwabtan jihohi, a halin yanzu Danfulani ya zama rimi kere itace, da babban mai Kamfanin zirga-zirga a jihar Kaduna, wanda gwamnati ya dace ta tallafa ma wa. Ko gwamnatin za ta tallafa masa,

lokaci ne kadai zai nuna hakan.


Advertisement
Click to comment

labarai