Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Mai Juna Biyu Ta Arce Daga Sansanin Matsafan Da Suka Sace Ta A Ogun

Published

on


Daga Abubakar Abba

Masu iya magana sun ce mai rabon ganin badi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.

Wannan karin maganar ya yi daidai da labarin wata mata mai suna Janet Oyewole, wadda aka yi zargin cewar, wasu matsafa ne suka sace ta daga jihar Osun suka kaita mabuyarsu dake yankin Ado Odo a cikin jihar Ogun.

Rahotanni sunce matsafan sun asirce, Janet suka kaita maboyar su.

Da kyar Janet ta iya samun sukunin yin bayani bayan ta samu ta arce daga hannun matsafan.

Wasu mutane da suka tausayawa Janet, sun  sun tara mata kudi da kuma bata suttura sun kuma yi kokarin gano ‘yan uwanta.

Wani mazaunin yankin mai suna Wale Hammed ya ce, ”munga matar ne tana ragaita akan titi, inda ta kuma tsaya a wata mahada har tsawon awowi kafin mutane su matsa kusa da ita su da ita su tambaye ko ina take nema.”

Ya ce, ”matar ta bayyana mana cewar, wasu da bata san su bane suka sato ta daga garin Oshogbo lokacin tana kan hayar ta zuwa gida, inda suka rufe mata ido da tsumma suka kuma kaita inda bata sani ba.”

Ya ci gaba da cewa, matar gaya mana Allah ne ya kubutar da ita daga mafakar matsafan bayan sun fita daga maboyar su.

A karshe ya ce, ”za mu yi iya kokarin mu don mu taimaka mata wajen kai ta wurin ‘yan uwanta ko mijinta da kuma sanar da ‘yan sanda don su mika ta ga ‘yan uwanta.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai