Connect with us

RAHOTANNI

“Yadda Aka Tilasta Mana Kwana Da Maza Ko Da Muna Cikin Yin Al’ada”

Published

on


Daga Abubakar Abba

Daya daga cikin  ‘yan matan da aka yi safarar su daga jihar su ta haihuwa Edo zuwa kasar Rasha aka kuma tilasta masu yin karuwanci  har tsawon shekara biyu, ta bayyana yadda aka rika kwana dasu har a yayin da suke yin jinin al’ada.

Yarinyar wadda aka tafi dasu a lokacin tanada shekaru sha tara, ta bayyana hakan ne a gaban wasu manyan jami’an gwamnati har da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, a lokacin Majalisar Dattawa ta shirya taron tattaunawa da ‘yan matan a garin Benin cikin jihar Edo.

Bayanan yarinyar wadda aka sakaya sunanta, yana kunshe ne a cikin faifan bidiyo da kafar zumunta ta facebook na na Malisar data tada. Yarinyar wadda a yanzu ta yi aure har da juna biyu, taci gaba da cewa, “sun ce min zan je yin karuwanci ne har na tsawon wata shida zan samo kudi don in zurfafa neman ilimi na”.

“Mun kwana da maza iri-iri har a kan hanya muna tsayawa a kan tituna.” inji ta

Ta kara da cewa, “ ‘mafi yawanci ‘yan matan suna barin gida ne da karfe uku na dare su tsaya a titi neman abokan hulda kuma uwar dakin mu tana tilasta mana mu kwana da maza koda muna al’adan. Tana ce mana ba ta yadda aikin ta ya tsaya ba.

“Akwai wata adugar mata da take bamu tace mu tare jinin bata barin mu mu zauna a gida ciyar da ita da tufatar da ita da kudin hayar ta duk mu muke biya.

“Mu muke sayawa kan mu kororon Roba wani lokacin maza daga shida zuwa bakwai suna zuwa gu na suna ko wannen sai ya biya ni kudin Rasha 1,000 kafin su kwanta dani a kullum wani lokacin indan kasuwa ta bude har 10,000 zuwa 15,000.

“1,000 na kudin Rashnin ya kai kima bout dalar Amurka 17,inda kuama ya kai daidai da naira 6,120”.

Ta kuma bayyana yadda wataran wasu maza suka sukayi mata taron dangi suka yi mata fyade da wani lokaci da ‘yan sanda suka cafke ta suka kulle ta a office dinsu har tsawon kwanaki suka kuma yi mata duka da fyade.

Ta kara da cewa, “har fitsari suke yi akai na in kuma nace su biya ni kudi na sai suce min in kai karar su ga mahukuntan kasar in kuma fada cewar sun yi mini fade, ba zan iya kai karar ba domin bami da wata shedar d azan gabatar  kuma na san hukumar bazata saurare nib a tunda ni karuwa ce.

“A hankali na yanke shawarar daina yin karuwanci na samu na gudo na dawo Nijeriya ba tare da Fasgo, wani dan Nijeriya da ake kira Mista Ken”.

A karshe ta ce, “kafin na gudu ina biyan uwar daki na dalar Amurka 15,000 daga cikin dalar Amurka 50,000 da take sa ran zan rika bata don ta ;yanta ni na yi matukar dana sanin tafiya ta Rusha”.

 


Advertisement
Click to comment

labarai