Connect with us

SIYASA

Tiriliyan Shida PDP Ta Ciwo Bashi A Shekaru 16, Amma APC Ta Ci Bashin Tiriliyan 11 A Shekaru 3 –Melaye

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Abuja

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin birnin tarayya FCT Abuja, Dino Melaye (Sanata a karkashin APC daga Kogi) a makon da ya gabata ne ya bayyana wa Majalisar Dattawan cewa, a karkashin mulkin jam’iyyar APC ta ciwo bashin tsabar kudi har tiriyan goma sha daya a cikin shekaru uku kacal da suka yi a bisa karagar mulki, inda kuma PDP ta ci bashin tiriliyn shida kacal a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulkar kasar nan.

Dino Melaye, wanda ke jawabi kan kin amincewa da kudirin wanzuwar gami da amincewar hukumar ‘Peace Corps’ wanda shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi facakali da shi.

Melaye ya ce babu wani takamaiman tsari ko shirin da wannan gwamnatin ta kawo domin samar wa matasa ayyukan yi a kasar nan.

Ya bayyana cewar korafin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar na cewar a sakamakon rashin kudi ne ya sanya ba a amince da wanzuwar Peace Corps ba, da cewar wannan uzurin ba karbabbe bane, kuma bai gamsar ba.

Ya ke cewa, “Wani abu makamancin wannan ya faru a lokacin da ake kokarin amincewa da hukumar NSCDC, an samu korafe-korafen cewar babu kudi, babu kudi”.

“Amma a yau, ga shi muna ganin amfanin samar da Cibil Defence da yadda suke taimaka wa gwamnati wajen bayar da kariya,” A cewar Dino.

 

 


labarai