Connect with us

SIYASA

Rikicin Gidan APC: Al’amarin Da Ya Ki Ci Ya Ki Cinye Wa

Published

on


Daga  Muhammad Maitela

Rikita-rikitar cikin gidan jam’iyyar APC mai mulki a tarayyar Nijeriya, wadda ta fara kama manyan turakun da take tafiya a kai. Rikicin wadda ta fara ci bal-bal tun bayan ayyana nasarar APC a zaben 2015 rikicin da ya kama kowanne lungu da sakon ta.

Matsalar da ta jawo nada kwamitocin sulhu tare da sasanta ‘ya’yan jam’iyyar APC. Na baya bayan nan shi ne wanda fadar shugaban kasa ta kafa da damka ragamar sa zuwa ga Asiwajo Bola Ahmed Tinubu domin sasanta rikita-rikitar da ta kanannade yan jam’iyyar.

Haka zalika kuma, wannan kwamitin yana fuskantar babban kalubalen yadda kallon hadarin kaji ke dada zafafa tsakanin wadannan kusoshin guda biyu. Bugu da kari kuma da rikita-rikitar da ke hauhawa a jihohi; da matakan kananan hukumomi wanda ya dabaibaye yan jam’iyyar APC.

A jihar Ondo, Borrofice ke rikici da gwamna Rotimi Akeredolu, yayin da a jihar Kogi, Hon James Faleke yake takaddama tsakanin sa da gwamna Yahaya Bello; ga Sanata Dino Melaye hadi da shugabanin APC suna takon saka da Yahaya Bello. Inda a Bauchi kuma Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara yana karon battar karfe da Gwamna Mohammed Abubakar, baya ga yadda a Kaduna- Sanata Shehu Sani tare da Suleiman Hunkuyi suka ja daga tsakanin su da Gwamna El-Rufai.

Yanayin bai canja zani ba a jihar Oyo ba, wanda ake dambacewa tsakanin karamin ministan sadarwa, Adebayo Shittu da gwamna Abiola Ajimobi. A gefe guda kuma, a jihar Ogun zaman doya da manja ake yi tsakanin Sanata Adeola-Yayi da Gwamna Ibikunle Amosun. Karawa da karau kuma, sai a Kano inda tattaburzar da ke ci gaba da zafafa a tsakanin Sanata Rabiu Kwankwaso da gwamna mai ci-Abdullahi Ganduje.

Idan ka je jihar Zamfara kurar rikici ce ta muske a tsakanin sanata Marafa da Gwamna Abdul’aziz Yari, sannan da wutar rikicin jihar Ribers wadda ta kama hannun rigar Rotimi Amaechi da ta sanata Magnus Abe. Har wa yau, a Imo, babu ga maciji asakanin Gwamna Rochas Okorocha da Sanata Ifeanyi Ararume, kuma da kallon hadarin kaji dake gudana a tsakanin Oyegun da Adams Oshiomhole a jihar Edo.

Haka lamarin yake idan ka leka jihar Bayelsa, inda Timipre Sylba ya shelanta shaya dagar fito-na-foto tsakanin sa da shugabanin jam’iyyar APC a jihar, sai rikicin da ya kannanade kafafun tsuffin hannu a jam’iyyar jihar Abia da ministan kasuwanci, Okechukwu Enelama. A jihar Gombe kuma, Sanata Danjuma Goje ke kai ruwa rana dashi da shugabanin jam’iyar APC a jihar.

Har yanzu tsugunen bata kare ba a tsakanin Segun Oni da Kayode Fayemi a Ekiti, inda wata wutar ke ci a jihar Osun, a tsakanin Gwamna Rauf Aregbesola da Mista Lasun, sannan da rikicin cikin gida a jam’iyyar wanda ya kankama a jihar Lagos, inda ake nuna wa juna yatsa a tsakanin Gwamna Akiwunmi Ambode da lauyan APC na kasa, Muiz Banire.

Ita ma jihar Delta bata kubuta daga wannan rikita-rikitar ba, yayin da Mista Erue Jones-jigo a jam’iyyar ke takon saka da kusoshin jam’iyyar. A Adamawa kuma, Gwamna Jubrilla Bindow ne ke yar-tifa da tsohon gwamnan jihar- Murtala Nyako, kana da rashin jituwar da ke tsakanin Sanata Nyako da Nuhu Ribadu. Yayin da a jihar Cross Riber kuma, rikici ya barke tsakanin shugabanin jam’iyya a jihar da minista mai kula da lamurran Niger Delta, Pastor Usani Nguru.

Manazarta su bayyana cewa, bisa hakikanin gaskiya Tinubu ya shiga sahun wadanda ke hana ruwa gudu a jam’iyyar APC tun bayan sabanin da ya kaure tsakanin sa da Dakta Bukola Saraki da Dino Melaye- biyo bayan shatale kafar sa wajen kokarin sa na kafa yaran sa a majalisar dattijai.

Wanda kuma hakan ya jawo dangantakar sa tayi tsami da wasu kusoshin jam’iyyar a yankin kudu maso yamma, irin su gwamna Amosun da Akereduolu, tare da ministan makamashi da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da makamantan su. Bisa ga wannan kuma, babbar matsala ce ace mai bunu a gindi ya kai gudumawar kashe gobara.

 


Advertisement
Click to comment

labarai