Connect with us

RAHOTANNI

PDP Ta So Ta Siye Mu Don Mu Yi Wa APC Zagon Kasa –Ma’ajin APC na kasa

Published

on


Daga Mustapha Ibrahim, Kano

Kishin ci gaban al’ummar kasar mu da jama’armu ne ya sa muka sadaukar da rayuwarmu gabadaya domin mu ga jam’iyyarmu ta APC ta yi nasara tun a 2015 domin mu shugabannin wannan jam’iyya ta APC amma na ta yi biliyan kimanin 25 inda za a ba kowanne mu biliyan daya da alkawarin gidaje gare mu da kuma mukamai ministoci idan PDP ta yi nasara amma muka ki yarda da a yi wa jam’iyyarmu ta APC zagon kasa da hadin bakin mu domin kishin kasar mu ta fita daga halin da PDP ta jefa kasar a baya.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin ma’ajin jam’iyyar APC na kasa Honarabul Bala Muhammad Gwagwarwa a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a gaban wasu daga cikin magoya bayan Jam’iyyar ta APC a Kano.

Ya ce, don haka duk wani abu na shirme da wasu za su fada akansu to ba zai zama gaskiya ba dominAllah ka dai ya san irin gwagwarmayar da suka yi kuma suke yi na ganin ba a wargaza jam’iyyar APC ba.

Haka kuma ma’ajin jam’iyyar, Honorabul Bala Gwagwarwa ya ce, su a matsayinsu na shugabannin Jam’iyyar APC har yanzu su na ci gaba da hikimomi da nuna kwarewa a siyasance na a ga ba a samu Nasara da zata kawo wa APC matsala ba inda y ace kuma har yanzu akwai hakkokin su da ya Kamata jam’iyya ta ba su amma ba a basu kuma hakan bai hana su su ga sun tsaya tsayin Daka domin APC ta yi Nasara ba, ga kuma irin jajircewar da su kayi na hana biyan bukatar wasu masu yiwa APC zagon kasa musamman a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba yi da lafiya su kadai su ka san wacce siyasa su ka yi don ceton Najeriya daga biyan bukatar masu son zuciya a jam’iyyar da kasa baki daya.

Danga ne da karin lokaci da akayi wa shugabannin APC kuwa ya ce abu ne da ya ke kan ka’ida kuma wata Hikima ce babba a siyasance wacce APC ce za ta fi kowa cin amfanin wannan karin lokaci ga shugabbanin jam’iyyar da akayi a wannan lokaci wanda kuma wannan ya samu Amincewar kasha 99 cikin 100 na shugabannin zartarwa da ake kira NEC na APC dan wasu kalilan sun so ki lamarin ai bazai yi wani tasiri ba tun da siyasa akeyi kuma siyasa kullum masu rinjaye sune ke da nasara a siyasance.

Haka kuma ya bayyana cewa shi a matsayin sa na Dan Kwankwasiyya ba wani abu da za a ba shi domin ya bar Kwankwasiyya domin su Kwankwasiyya akida ce amana ce domin kula da hakkin al’umma musamman raunana na a ga sun sami ilimi da sauran ci gaba domin al’umma ta zama mai Daraja a ko ina kuma a ko da yaushe kuma irin jajircewa da sadaukar wa da sukayi wajen ganin ba ayi wa APC zagon kasa ba wannan akida ta rikon amana bas a duniya a gaba ba shi ne akidar Kwankwasiyya a cewar Honorabul Bala Muhammad Gwagwarwa Kano Ma’ajin Jam’iyyar APC na kasa inda kuma ya bukaci al’ummarmu musamman ta arewa da su tsaya wajen koyi da magabata ta hanyar rike sana’o’i da kuma mutunta kan su kamar ya kamata.


Advertisement
Click to comment

labarai