Connect with us

SIYASA

PDM Ta Shirya Karbe Kujerun Kananan Hukumomi A Jihar Neja –Nasko

Published

on


Daga Muhammad Auwal Umar Minna.

Jam’iyyar PDM ta kasa reshen jihar Neja ta kalubalanci gwamnatin kan kasa aiwatar da zaben kananan hukumomi. Ba wani dalili ga kasa rushe shugabannin kananan hukumomi saboda wa’adinsu ya cika shekaru biyu. Shugaban jam’iyyar PDM, Kwamared Musa Nasko ne ya bayyana hakan bayan kammala taron jam’iyyar na tantance ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi da kansuloli.

Kwamared Nasko ya cigaba da cewar ba mu san ko a wata doka ne shugabannin ke cigaba da mulkin ba tunda wa’adinsu na shekaru biyu ya cika, kan haka majalisar dokokin jiha ta jawo hankalin gwamnati kan rushe majalisar shugabannin kananan hukumomi amma har zuwa yanzu ba wani bayani.

Mu a matsayin jam’iyya mun tuntubi hukumar zabe ta jiha dan jin ranar da aka ware dan yin zaben kananan hukumomin amman ita ma cewa tai ba ta sani ba, wanda hakan ya sabawa dokar da aka yi zabe tare da rantsar da shugabannin.

Ba na kokwanto ko yanzu gwamnati ta cire tsoro indai za a gudanar da zabe a dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar muna da ‘yan takara. Don haka muna masu jawo hankalin gwamnati akan a rika aiki bisa dokokin da majalisa ta amince da shi amma yanzu ba mu san a wani matsayi ake akai ba.

Gwamnati na jin tsoro ne saboda shugabannin kananan hukumomin ba su tare da jama’a idan an yi zabe ta hango faduwa muraran, ba wani bambamci da gwamnatin da ta gabata har yanzu ba wani zababben shugaban karamar hukuma da zai iya kwashe kwanakin mako a karamar hukumarsa, saboda ba sa aikin komai duk da irin kudaden da suke samu.

Shugaban ya jawo hankalin shugabannin jam’iyyar a matakin kananan hukumomi da mazabu da su tashi haikan wajen wayar da kan magoya bayansu muhimmancin mallakar katin zabe, duk yadda ka ke son yin gyara muddin ba ka da katin zabe ba zai yiwu ba, Don haka kowa ya jure ya tabbatar ya mallaki katin zabe shi ne muhimmin abu.

Taron dai ya shafi duk masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, wanda shugabanta Kwamared Musa Nasko ya jagoranta, bisa goyon bayan sakataren jam’iyya na jiha da shugabar mata ta jiha, Hajiya Fatima Bida. Taron ya gudana a harabar sakatarinyar jam’iyyar ta jiha da ke Nateco cikin garin minna a lahadin makon nan.


Advertisement
Click to comment

labarai