Connect with us

WASANNI

Na Shirya Zama Mai Koyar Da Arsenal –ALLEGRI

Published

on


Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Madimiliano Allegri ya bayyana cewa yagama shiryawa domin karbar aikin koyar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a karshen kaka.

Allegri, mai shekara 52 ya bayyana hakane inda yace tuni yafara koyan yaren turanci kuma yafara tunanin rayuwa a birnin Landan a shekara mai kamawa.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai ana tunanin zata nemi sabon mai koyarwa domin cigaba da koyar da kungiyar bayan da ake tunanin mai koyar da kungiyar, Mista Arsene Wenger zai ajiye aikin koyar da kungiyar sakamakon matsin lamba dayake fuskanta.

A kwanakin baya ma dai an danganta mai koyarwar, dan kasar Italiya, da karbar aikin koyar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea inda zai karbi koyarwar a hannun dan uwansa dan kasar italiya, Antonio Conte.

Arsene Wenger dai yana fuskantar matsin lamba daga bangaren magoya bayan kungiyar sakamakon kungiyar tasha kashi sau 4 jere a wasan firimiya dana Europa da kuma rashin nasara a hannun Manchester City a wasan karshe na cin kofin Karabawo.

Wenger dai ya shafe shekara 22 yana koyar da Arsenal bayan daya jagorancin kungiyar ta lashe kofuna daba-daban ciki har da kofin firimiya guda uku sannan kuma yakawowa kungiyar shahararrun yan wasa a lokutan baya.

Har yanzu dai mahukuntan kungiyar basu ce komai ba game da makomar Wenger sai dai kamar yadda rahotanni suke fitowa abune mai wahala ya ci gaba da zama a kungiyar indai bai lashe kofin Europa ba da kungiyar take fafatawa a yanzu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai