Connect with us

MAKALAR YAU

MUKALAR LITININ: Kashe Buharin Daji: Wane Ne Dogo Gide, Kuma Ina Yake?

Published

on


Sulaiman Bala Idris 0703 666 6850

A makon da ya gabata dai, cikin ikon Allah da nufinsa, an kawo karshen shafin hatsabibin makashin nan, wanda aka fi sani da Buharin Daji. Buharin Daji, asalin sunan da aka fi saninsa da shi, kafin ya gawurta, ya fara keta mutuncin al’umma, an fi kiransa da Buhari Tsoho.

Da yawan wadanda suka yi mishi farin sani, har yanzun Buhari Tsoho suke kiranshi da shi. Wasu ma ba su sanya ‘Buharin’ a sunan, sai dai su ce Tsoho kawai.

Hatsabibi ne na gaske, wanda ke ji da kansa a harkar rashin mutunci. tsagera na wanda kansa ke hayaki. Irin mutanen nan ne masu mugun ji da kansu, wadanda kuma ji – ji da kai din ke kai su ga ajali.

Tsoho – Buharin Daji a wani faife da na saurara, kafin ya hadu da ajalinsa, cikin Gadara ya ke magana, yana cewa ‘Sai Zamfara ta koma tamkar Maiduguri’. Wai kuma fa a wurin Buharin Daji, gaskiya yake fadi, domin ya ce, ba barazana yake yi ba.

Tsabar raina gwamnatin Jihar Zamfara da Buharin Daji yayi ne, ya sa yake jin kansa kamar wani Sarki, wanda ya fi Fir’auna iko da karfi. Kuma ba wai hasashe ko ga dukkan alamu ba, a’a, a kashin gaskiya yana da nashi dalilan na raina Mahukuntan Jihar Zamfara.

Banda Zamfara, a ina ne za a sakarwa Makashi kamar Buharin Daji mara yayi ta tsula tsiyarsa? Kuma wai irin wadannan maganganun ne idan aka fadi ko aka tanka a kai, sai ciwo ya zama kari.

Saboda tsabar rainin hankali irin na Buharin Daji, ba Zamfara ba ce kawai iyakarsa, yak an tsallaka zuwa wasu sassan Katsina da Kaduna a inda yake aikata ayyukan ta’addanci da keta haddi. Mafakarsa dai ita ce, Jihar Zamfara.

Tsoho ya hadu da ajalisansa ne a ranar Larabar makon da ya gabata, an kuma tsinto gawarsa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun tabbatar da cewa, wannan hatsabibin makashi, Buharin Daji dan asalin Garin Dangulbi ne, wani kauye dake Makwabtaka da garin Dansadau dake Karamar hukumar Maru, a Jihar Zamfara.

Yaronsa, wanda a wani rahoton ake nuni da cewa, yana daga cikin na hannun daman Buharin Dajin, wato Dogo Gide shi ne ya samu nasarar halaka shugaban ‘yan ta’addan. Kisan na Tsoho, ya biyo bayan sace Shanu da yi wa mata fyade da yayi a gidan surukan Dogo Gide.

Dogo Gide yayi iyaka iyawarsa wurin ganin Buharin Daji ya sako Shanu da matan da ya sace musu, amma hakan ta ci tura. Wannan lamari ne ya hargitsa Dogo (wanda wata majiyar ke nuni da cewa ya tuba, har ma yana taimakon jam’ian tsaro wurin dakile barayin Shanu a yankin).

Daga karshe, sai Buharin Daji ya aminta da su hadu da Dogo Gide a Dajin Nabango a gundumar Goron Dutse ta Karamar Hukumar Birnin Gwari dake Jihar Kaduna, domin a yi zaman sulhu kan batun.

Ko da lokacin haduwarsu yayi a ranar Larabar da ta gabata, yayin da Buharin Daji suka iso wurin shi da ‘yan tawagarsa, sai Dogo Gide ya bude musu wuta. Inda a wata ruwayar aka ce, a take ya kashe Buharin Daji da kwamandoji Shida daga cikin manyan hatsabiban yaransa barayin Shanu.

Wata Majiya mai tushe ta nakalto cewa, Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauki nauyin Dogo Gide domin ya halarci kasa mai tsarki don yin aikin Hajji a wannan shekara mai zuwa. Amma kuma, inji majiyar, sai Dogo Gide ya yi tutsu, zuwa yanzu ma an neme shi an rasa, saboda ya raina tukuicin da gwamnatin ta bashi.

Kuma Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa; Dogo Gide ne ya sanar da Jami’an tsaro wurin da za su je su dauki gawar Buharin Daji tare da makusantansa shida wadanda ya kashe.

Ko da Sojoji suka shiga Dajin tare da taimakon ‘yan sa kai, sun tarad da gawarwakin kamar yadda Dogo Gide ya sanar da su, sai dai bisa umurnin da suka samu, gawar Buharin Daji kawai za su dauko, kuma ita din suka dauko suka kai ta Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara.

Akwai wasu tambayoyi da gwamnatin Jihar Zamfara ya kamata ta amsa su. Na farko dai, wane ne Dogo Gide? na biyu, shin tuntuni me ya hana shi ya dirkawa Buharin Daji harsasai har sai bayan da ya sace Shanu da matan Surukansa?

Kafin mu je ga tambayoyi na gaba. Na fara wani tunani, kuma ya kamata kowa ma yayi wannan tunanin. Daga labaran da suka fito na yadda Dogo Gide ya samu nasarar kashe Buharin Daji, za mu iya fahimtar wani abu daya; wannan abin kuwa shi ne; Dogo fa ya fi Buhari wayo, dabara da zafin nama. Kuma ga dukkan alamu ba don Allah Dogo ya kashe Buhari ba, tunda har ya raina tukuicin kujarar Makka!

Idan Dogo Gide ya rikide, labarin zai canza. Don haka tun da wuri, tun kafin a yi latti, ana bukatar a nemo Dogo Gide a duk inda yake. Ba kawai ido za a sa mishi ba, domin shi ma barazana ne ga rayukan al’umma da zaman lafiya. Wane ne Dogo, kuma ina yake? Gwamnatin Jihar Zamfara ce za ta bamu amsa.

 

 

 

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai