Connect with us

SIYASA

Makarfi Ya Tallafa Wa Al’ummar Kasuwar Magani

Published

on


Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmed Kohammed Makarfi ya shawarci al’ummar karamar hukumar Kajuru, musamman na garin Kasuwar Magani da su rungumi zaman lafiya a tsakaninsu domin ci gaban wannan karamar hukumar, da kuma jihar Kaduna baki daya.

Alhaji Ahmed Makarfi ya bayyana haka ne a sakon tallafin kayayyakin abinci da ya aika ga al’ummomin Kasuwar Magani da wasu matsaloli suka faru a garin wanda har aka rasa rayukan al’ummomin da suke wannan karamar hukumar.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, wanda Shugabar mata ana jihohin arewa ma so yamma na jam’iyyar PDP Hajiya Halima Yunusa Kajuru ta wakilta ya ci gaba da cewar, babu al’ummar da za ta sami ci gaba sai al’ummar ta rungumi zaman lafiya tare da girmama ra’ayoyin juna, san nan, in ji shi, za a sami ci gaban da ake bukata.

A dai sakonsa Alhaji Ahmed Makarfi ya yaba wa shugannin addinin musulunci da kuma na kirista, na yadda suka hada hannu a lokaci guda,  suka dakile yaduwar wannan matsala da taso a garin Kasuwar Magani da kuma wasu kauyuka da suke makotaka da wannan gari da aka ambata.

Ya kuma shawarci shugabannin addinan musulunci da kuma na kirista da su kara tsayawa irin na maid aka, waje ci gaba da bin hanyoyin da suka dace , na ganin wannan matsala ba ta kara tasowa ba a wannan gari da kuma jihar Kaduna baki daya.

Hajiya Halima Yunusa Kajuru, a matsayinta ta ‘yar karamar hukumar Kajuru, ta ce, dole ta yaba wa Alhaji Ahmed Makarfi, na yadda ya tausaya wa wadanda wannan matsala ta rutsa da su, har kuma ya ba su wannan tallafin kayayyakin abinci.

A jawabansu daban-daban, shugabannin kungiyoyin Jama’atul Nasrul Isla da na Kungiyar kiristoci a Nijeriya, duk sun yaba wa Alhaji Ahmed Makarfi, na yadda ya tallafa wa al’ummar Kasuwar Magani da wasu garuruwa da wannan matsala ta shafa.

Shugabannin kungiyoyin biyu, sun kuma tabbatar wa wakiliyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Halima Yunusa Kajuru cewar, kwamitin da ke tattara gudunmuwar zai rike amanar da aka dora ma san a rabon kayayyakin tallafin bisa adalci a tsakanin wadanda matsalolin tashin-tashinar ta rutsa da su, kamar yadda suka saba laya a lokacin

da aka kaddamar da su, jim kadan bayan faruwar tashin-tashinar.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai