Connect with us

SIYASA

Majalisar Katsina Ta Jaddada Kudurin Goyon Bayan Gwamnati

Published

on


Daga Sagir Abubakar, Katsina

Majalisar dokoki ta jihar Katsina ta kara jaddada kudurinta na bayar da goyon baya ga manufofi da shirye-shiryen gwamnati mai ci a yanzu.

Shugaban majalisar Alhaji Abubakar Yahaya Kusada ya bada tabbacin hakan ne a lokacin da ya amshi bakuncin manyan jami’an kungiyar hadin kan Kafur watau Kafur Unity Forum da suka kai ma shi ziyara.

Ya bayyana Gwamna Aminu Bello Masari a matsayin shugaban abin koyi wanda manufarsa ta bunkasa rayuwar al’umma ta wuce bukatunsu ta kashin kansa.

Ya bayyana cewa majalisar tana alfahari da gwamna Aminu Bello Masari akan halayensa na nuna da’a da rashin sanya iyalensa a cikin harkokin gwamnati.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa tsawon zaman da majalisar tayi tare da wannan gwamnati mai ci a yanzu babu wani lokaci inda gwamnan ya aikata ba daidai ba a kasafin kudi sai dai wurin da majalisar ta bada shawarwari na yin gyara.

Alhaji Yahaya Kusada ya bayyana cewa demokoradiyya ba za ta tafi lafiya lau ba har sai in akwai ja in ja tsakanin bangaren zartaswa da na majalisa.

Shugaban kungiyar hadin kan ta Kafur  mai suna Kafur Unity Forum Alhaji Abubakar Magaji ya bayyana cewa sun je majalisar dokoki ta jiha ne domin sun jindadin al’ummar karamar hukumar ta kafur ga me da goyon bayan da majalisar ta ke ba Gwamna Aminu Bello Masari a jihar nan.

Kamar yadda yace irin wannan hadin kan tsakanin bangaren zartaswa da na majalisa ya taimaka wajen kawo cigaba mai ma’ana a jihar nan.

Ya bayyana kiwon lafiya, ilimi, aikin gona da samar da kayayyakin more rayuwa a matsayin bangarorinda gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari ta ke ba muhimmanci.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa daga darajar manyan asibitocin Katsina, Baure da Funtua da gwamnatin jiha mai ci a yanzu ta yi ya taimaka wajen inganta samar da kiwon lafiya ga mutane.

A jawabin shi wani Dattijo na kungiyar Alh. Abubakar Dogo ya bayyana bangaren majalisa a matsayin wanda ya ke taka muhimmiyar rawa wajen cigaban demokoradiyya da gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari ta ke ba muhimmanci.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa daga darajar manyan asibitocin Katsina, Baure da Funtua da gwamnatin jiha mai ci a yanzu ta yi ya taimaka wajen inganta samar da kiwon lafiya ga mutane.

A jawabin shi wani Dattijo na kungiyar Alh. Abubakar Dogo ya bayyana bangaren majalisa a matsayin wanda ya ke taka muhimmiyar rawa wajen cigaban demokoradiyya.


Advertisement
Click to comment

labarai