Connect with us

RAHOTANNI

Jam’iyyar KOWA Mafita Ce Ga Kasar Nan –Bobboi

Published

on


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Jam’iyyar kowa ta fito ne dan kawo mafita ga kasar nan saboda kangi da aka saka al’umma domin rashin adalci da shugabanni suke. Shugaban jam’iyyar na kasa Alhaji Sa’idu Bobboi ya bayyana haka a wajen zaben shugabannin jam’iyyar na jahar Kano. Ya ce, jam’iyyar tun a 2009 aka yi mata rijista a kasar nan kuma ta tsai da ’yan takara a matakai daban-daban har da shugaban kasa ba tare da jingina ko hada kai da wata jam’iyya ba. Bobboi ya ce, Jam;iyyar ta soma da rarrafe ta yi ta-ta-ta kuma yanzu tana tafiya da kafafunta duk wanda bai gamsu da yadda abubuwa ke tafiya a kasar nan ba ya zo a hada kai a cikin wannan jam’iyyar a sami mafita yanzu haka akwai masu neman su tsaya wa jam’iyyar takarar shugaban kasa mutum hudu a kasar nan.

Alhaji Hamisu Bobboi ya ce, jam’iyya ce da take da manufa ta ci gaban talakawa wanda za ta sa matasa a gaba dan kaiwa ga nasara duba da duk shugabanni da suka sami kai kasar nan ga nasara suna matasa ne, dan haka muka zo da manufa ta kawo ’yanci ga matasa maza da mata dan sau da dama sukan yi zabe sai a tura mota a gudu a bar su da kura, sai zabe ya zo a watsa musu tsaba dan su sake zaba.

Shugaban jam’iyyar na kasa Saidou Bobboi ya ja hankalin sabbin shugabanin jam’iyyar da aka zaba yayin taron su rike amana da aiki tukuru wajen ciyar da jam’iyyar gaba. Ya ce, saboda kula da bai wa nakasassu muhimmanci shi ya sa suke tafiya tare da su a shugabancin jam’iyyar.

Shi ma jagoran jam’iyyar kowa a jahar Kano Malam Hamisu Magaji ya nuna rashin gamsuwa da mulkin APC na kusan shekaru uku da ba wani abu da ta kawo wa talaka ya amfana a kasa. Ya kara da cewa, hasali ma koma baya aka samu, an shiga kangin talauci da rashin kwanciyar hankali, masifu ana cikinsu a kasar nan ta kowane bangare, dan haka suka kawo wannan jam’iyya domin nema wa al’umma mafita.

Malam Hamisu Magaji ya ce, ko a zaben 2015 sun shiga zabe sun yi na uku a Kano, kuma sun tsai da ’yar takarar shugaban kasa Farfesa Uwargida Remi Shonaya da ita aka yi muhawara ma da tsohon shugaba Jonothan da Buhari kafin zabe ta zama ta daya a manufofin da ta kawo dan ci gaban kasa. Malam Hamisu Magaji ya ce, yanzu matasa na shiga jam’iyyar tasu wanda ita za ta zama mafita ga al’umma saboda kosawa da rashin adalci da ke wanzuwa a mulkin kasar nan.

Malam Hamisu ya ce, jam’iyyar KOWA ta kowane bangare ne na al’umma da suke son kawo sauyi a kasa .Ya yi kira ga ’yan jam’iyyar su ci gaba da ba shi hadin kai bisa zaben da suka yi masa dan kai jam’iyyar ga nasara. A lokaci taron dai an sake tabbatar da Malam Hamisu Magaji a matsayin zabbabben shugaban jam’iyyar KOWA a jahar Kano, kunshin zababbun shugabanin jam’iyyar a Kano guda 18 ne ciki har da


Advertisement
Click to comment

labarai