Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Nijeriya Za Ta Samar Da Matatun Mai Biyu A Neja Delta

Published

on


Daga Abubakar Abba

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewar tana kokari wajen kafa matatar mai guda biyu na zamani a yankin Neja Delta. Gwamantin ta sanar da hakan ne bayan data shigo da kayan aikin cikin kasar nan bayan hukumar hana fasa kauri ta kasa ta tantance kayan.

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a Abuja a taron da kwamitin yankin  Delta wanda Osinbajon ya jagoranta, inda ya sanar da mahalarta taron cewar, za a kafa matatun man ne a yankin na Neja Delta.

Furucin na Farfesa Yemi Osinbajo yana kunshe ne a cikin sanarwar da mai taimaka masa na musamman akan harkar yada Labarai, Laolu Akande ya sanyawa hannu, inda sanarwar ta nuna cewar, kuma ana tsimayin sauran kayan da za su iso kasar a cikin watan Afirilu da za a kafa su a jihar Ribas.

Osinbajo ya ci gaba da cewa, aikin ya hada da samarwa da al’ummar dake kusa da matatar mai aikin yi.

A cewar sa Osinbajo, al’ummar dake zaune a inda za a kafa matatun man za a tabbatar da sun samu ayyukan yi kai tsaye da kuma samarwa da matasan dake yankin ayyukan yi.

Idan dai ba a manata ba, a cikin watan Disambar shekarar 2017, kwamitin ya karbi rahoto akan lasisi talatin da takwas na ‘yan kasuwa masu zaman kansu da suma suka nuna sha’awar su ta zuba jari akan kananan matatun mai a yankin.

A lokacin taron, akalla masu zuba jari goma da suka samu lasisi tuni sun yi nisa wajen shirye-shiryen kafa kananan matatun mai.

Bugu da kari, rahoton hukumar NDDC, a taron ya nuna yadda aka yi nisa wajen kaddamar da aikin a yankin. Sanarwar ta kara da cewa, a shekarar 2017, jimlar ayyuka da suka hada da aikin hanyoyi 372 da gada da samar da wutar lantarki da ruwan sha da sauran su hukumar ta kammala. Aikin ya kuma hada da akin hanya ta Nembe-Ogbia ma tsawon kilo mita 25.7 wadda nan bada dade wa za a kaddamar da hanyar.

Akwai kuma aikin hanyoyi na Otueke dake cikin karamar hukumar Ogbia a cikin jihar Bayelsa data Kira Dere Mogho da aikin gada a karamar hukumar   Gokana cikin jihar Ribas. Bugu da kari, akwai kuma aikin hanyar Iselu-Okaigben-Idung-Boko-Onicha Ugbo a jihohin Edo da yankin Delta da aikin hanya na Orie Ukwu Amaoji a cikin karamar hukumar Isiala Ngwa ta Arewa a jihar Abia da aikin hanyar Ashikem-Ufono-Betwaswan a garin Obudu cikin jihar Koros Ribas. Hukumar tana kuma kan aiki tare da ko wanne bangare harda AMCON, don a tabbatar da an kaddar da samar da gangar mai 6,000 a kullum a karamar matatar mai dake Amakpe da za a kafa a garin Eket cikin jihar Akwa Ibom. Hukumar NDDC ta bayyana cewar, ta kafa cibiyoyin samar da ayyukan yi da ake sa ran za a samarwa da kimanin matsa 208,000 dake yankin Neja Delta ayyukan yi.

Manufar a cewar hukumar ita ce, don a rage ywan matasa masu zaman kashe wando a yankin kuma cibiyoyin za su yi daidai da samar da ayyukan da ake dasu ta hanyar koya masu sana’oin dogaro da kai a yankin.

Akan nasarar da aka samu wajen share dagwalon mai a Ogoni aikin wanda yake a karkashin ma’aikatar muhalli ta kasa kuwa, zata fara neman kwararru don kammala share dagwalon na mai a Ogoni. In an kammala aikin, zai bai wa kamfanin dake kasashen waje za su samar da ayyukan da za su inganta rayuwar mazauna yankin. Takardar ta karshe ta kaddamar da aikin na (SIWP), an gabatarwa da kwamitin.

A wata sabuwa kuwa, jami’ar  Maritime dake Okerenkoko a cikin yankin Delta, ta shirya tsafa, wajen daukar sababbin dalibai na shakarar karatu ta 2017/2018 kuma za a fara koyar da darussa a cikin watan Afirilu. Kimanin jimlar dalibai 196 jami’ar ta samnce zata dauka,inda kuma fam 76 din dalibai na neman gurbin karatau suke ajiye.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tuni ya amince da  karin naira biliyan biyar daga naira biliyan biyu da a baya aka amince. Wannan kudin an sanya su a cikin kasafin kudi na shekarar 2018 da aka gabatarwa da majalisar kasa a cikin watan Nuwambar shekarar 2017.

Haka kuma, shugaban kasa ya kara amincewa da naira biliyan daya don tallafawa ayyuka na musamman dana daukar ma’aikata a jami’ar a cikin watan Nuwambar shekarar 2017 2017. Gwamnatin jihar  Delta ta bai wa jami’ar gudunmwar Janareto guda biyu.

A cikin watan Janairu ne hukumar jami’oi ta kasa (NUC) ta amice jami’ar, ta fara yaye dalibai da suka karanta Digiri a sassa uku na jami’ar, da suka hadada; darasin sufuri da da kere-kere da kula da muhalli da za a fara sassa sha uku na jami’ar daga shekarar karatu ta 2017/2018. Wasu daga cikin jami’an gwamnati da suka halarci taron sun hada; Ministan yankin Neja Delta Usani Usani da karamin Ministan na muhalli Ibrahim Jubril da Manajin  Darakta kuma babban jami’I na hukumar NDDC Nsima Ekere.

Sauran sune, Darakta Janar na hukumar (NIMASA) Dakuku Peterside da mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman akan shirin afuwa na gwamnatin tarayya Paul Boroh da babban sakatare na (NUC) Adamu Rasheed da shugaban jami’ar Maritime Ongoebi Etebu da wakilan sauran hukumomin gwamnatin tarayya.


Advertisement
Click to comment

labarai