Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnan Gombe Ya Ba Dalibai 51 Da Suka Yi Zarra Aiki

Published

on


Daga Khalid Idris Doya

A shekaran jiya ne Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayar da damar daukan aiki kai tsaye ga daliban da suka yi zarra cikin wadanda suka kammala jami’ar jihar Gombe.

Su dai daliban sun kamala ne da sakamakon kwazo mafi kololuwa na ‘First Class’, wadanda suka samu wannan zarafin adadinsu ya kai mutum 51.

Gwamnan Gombe, Dankwambo, ya sanar da kudirinsa na daukansu aiki kaitsaye ne a yayin bikin yaye daliban da suka kammala jami’ar na rukuni na 6, 7, 8 da na tara wadanda suka samu takardar shaidar jami’ar a matakin farko har zuwa aji hudu.

Har-ila-yau, gwamnan ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar Gombe ta amince da daukan su aiki kai tsaye ga duk mai bukatar hakan a cikinsu, hade kuma da basu tallafin naira dubu dari-dari ga kowanne daya daga cikin dalibai 51 da suka yi zarran.

Dankwambo ya bayyana cewa a karkashin gwamnatinsa ta iya samar da cikakken amincewa wa ASUU da kuma yarjejeniya da gwamnatin tarayya, ya kuma kara da cewa tallafin karatu ma gwamatinsa ya na kokari wajen bayarwa.

A nashi jawabin, mukaddashin shugaban jami’ar jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Musa Umar, ya ce, adadin dalibai dubu uku da dari tara da hamsin da uku 3,958 ne suka samu kammala jami’ar a wannan lokacin.

Ya ce, dalibai da suka yi zarra suka kammala da lambar kwazo na daya su 51 ne, adadin dalibai 864 ne suka fita da lambar sakamako na biyu mai daraja, a yayin da kuma dalibai 1,945 suka fita da sakamako na biyu marar daraja ‘second class lower’, su kuma dalibai 1,038 suka kammala jami’ar da mataki na uku.

Da yake jawabi a madadin NUC, Dr Bello Gidado Kumo, ya ce, hukumarsu za su amince da tsangayar ilimin lauya da wasu fannoni guda biyu a rukinin karatu na gaba na jami’ar.

Wakilinmu ya labarto cewar jami’ar ta kuma karrama shugaban jami’ar kuma sarkin Gome Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III da kyautar Digirin girmamawa, sauran wadanda suka samu kyautar Digiri din su ne Sakatariyar majalisar dinkin duniya Hajiya Amina J. Mohammed, Cif Christopher Kolade da kuma babban manajin darakto na bankin Access Bank PLC, Mr Herbert Wigwe.

 


Advertisement
Click to comment

labarai