Connect with us

KASUWANCI

Dandamalin ‘Zero Hunger’ Ya Bukaci Gwanmoni Da Su Mayar Da Hankali Ga Noma Da Kiwo

Published

on


Daga Abubakar Abba

Kungiya mai suna ‘ Zero Hunger Forum’ ta jaddada cewar akai bukatar gwamnatocin  jihohin kasar nan su mayar da hankali wajen noma da kiwo don a habaka sana’oin biyu.

Ta kuma bukaci gwamnonin jihohin dasu bada mahimmanci wajen zabar amfanin noma uku da sana’ar kiwo.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin takardar bayan taro da shugaban kungiyar kuma tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo (PHD) da Gwamnan jihar Borno kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa Kashim Shettima suka rattabawa hannu a satin da ya gabata.

Taron kungiyar jaro na uku an gudanar da shi ne daga ranar takwas zuwa tara ga watan Maris na 2018 a garin Maiduguri cikin jihar Borno.

A cewar sanarwar, kungiyar ta gudanar da taron karo na uku ne da nufin sanya ido wajen kaddamar akan kokarin da jihar ta yi da kuma duba nasarorin da jihohin da aka fara kaddamar da shirin suka samar tun bayan taron karshe da aka gudanar a jihar Ebonyi a shekarar data gabata.

Wakilan jihohin biyar da aka fara kaddamar da shirin a jihohin su, suma sun harci taro. Jihohin sune; Benue da Borno da Ebonyi da Ogun d Sokoto da  Bauchi da Nasarawa da kuma Oyo.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hadada; kwararru da suka yi hadaka da kungiyar da cibiyar aikin noma ta kasa da kasa (IITA) da jami’an shirin samar da abinci(WFP) kungiyar noma da samar da abinci ta  (FAO) ‘yan kasuwa masu zaman kansu da kungiyoyin manoma da wakilan Masarautar Borno da kuma ma’aikatar noma da raya karkara.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hadada; na Borno Kashim Shettima da mataimakin Usman Mamman Durkwa da mataimakin gwamnan Ebonyi Kelechi Igwe da mataimakin gwamnan jihar Ogun  Yetunde Onanuga.

Shi kuwa gwamnan Jihar Biniwai Samueal Ortum, kwamishinan sa na noma Mista James Abuane ne ya wakilce shi. Ko wacce jihar da aka fara gudanar da shirin, ta gabatar da kasida a wurin taron akan nasarorin da suka samu don cimma burin shirin da kuma yadda taron da kungiyar ta gudanar a jihohin Biniwai da Ebonyi suka ja hankalin su.

Suma masana’antu masu zaman kansu, sun gabatar da bayanai, musamman akan noman waken Soya a jihar Biniwai  kamar yadda wani Titus Agbecha ya bayyana cewar, shirin na kungiyar yaja hankalin su sosai da kuma habaka aikin su na noma.

A wata ziyara da aka kai a cibiyar gona da rubanya irin noma  da kuma kai ziyara ga cibiyar (Machinery Shade),an kuma kai ziyara ga makarantar mata da jami’ar Borno domin duba yadda ayyukan noma da

gwamnatin jihar Borno ke gudanarwa don cimma burin shirin na kungiyar.

An kuma haska faifan Bidiyo mai tsawon mintuna ashirin dake kunshe da irin nasarorin da aka samu sakamakon rashin kai ziyara ga matsugunin ‘yan gudun hijira inda ake gudanar noman rani don samar da abinci da kiwo kaji da kifi da kuma sabon tsarin aikin noma don tallafawa matasa.

A bisa bayanai da aka samu, daga masu gabatar da kasida da ziyarar gani da idon da aka kai, wakilian kungiyar sun yabawa gwamnatin jihar Borno a bisa daukar nauyin taron bayan da kuma bayar da shawarwar.

Kungiyar ta kuma yabawa akan kasidun da aka gabatar akan nasarorin da jihohin suka samar wajen cimma nasarar shirin kungiyar da kuma matakan da jihar Ebonyi ta dauka da kungiyar ta gabatar a taron ta na baya.

Bugu da kari, manyan masana’antu sunada kyau wajen samar da wadataccen abincu. Kungyar ta kuma bayar da shawara da a mayar da hankali ga matsakaitan sana’oi na noma wadanda zasu zama hadaka a tsaknin kananan manoma da masana’antu.

Har ila yau, kungiyar ta jinjinawa kikarin gwamnatin tarayya ta hanyar Babban Bankin Kasa(CBN) da Bankin Manoma don samar wa manoma matsalar kudi da suke fuskanta.

A taron, an kuma yabawa CBN akan amasa gayyatar halartar taron. Kungiyar ta kuma jinjinawa CBN akan taimakon kudi data bayar da masana’antun dake jihar Biniwai, musamman taimakaon da aka baiwa manomi Titus Agbecha akan sarrafa waken soya tare da zuba jarin da gwamnatin

jihar  Borno ta yi wajen samar da kayan aikin noma na zamani.

Wakilan kungiyar sun kuma yi kira ga jihar ta Borno data kafa samar da kayan noma na zamani da yafi dacewa don manoman jihar su dinga samun su a cikin sauki.

Ta kuma bayar da shawara wajen kakkafa cibiyoyin noma ta hanyar yin amfani da masana’antu masu zaman kansu.

An kuma amince akan cewar akwai bikatar jihohi su horar da masu koyar da yadda ake yin amfani da kayan noma na zamani kamar Taraktoci da gyran  su da kuma kula da dasu.

An kuma yaba wa jihar Borno akan kirkiro da kayan na’urorin noman rani kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar data samar da kasuwar fasaha ga daukacin sauran jihohi dake kasar nan, musamman a yankin Arewa Maso Yamma.

Kungiyar ta kuma yi jinjina noman rogo, inda ta ce, hanya ce yin yaki da yunwa da da samar da ayyukan yi musamman ga mata da matasa. Ta kuma bukaci jihar ta Borno data zuba jari a noman rogo.

Don kara habaka ci gaba, kungiyar ta shawarci jihar da a cikin gaggawa data samar da yanayi wajen baiwa masana’antu masu zaman kansu dammar yin hadin gwaiwa da kananan masana’antu. Shirin zuba jari a fannin ilimi na jihar shima taron ya amince dashi musamman don tabbatar ko wane yaro na jihar ya samu ingantaccen ilimin Boko kyauta tun daga matakin sakafare.

Kungiyar ta kuma yabawa hukumar(IITA) akan jan jihohi a jiki wajen basu taimako don lura da aikin noma musamman noman rogo da doya da bayar da tallafin irin noma. Suma sauran masu ruwa da tsaki suma an jaba masu. An kuma yabawa kokarin da hadaka tskanin (FAO) da kungiyar. Kungiyar ta kuma amince ta taron da za ta gudanar a watan Yuli 2018 a jihar  Sokoto.

 


Advertisement
Click to comment

labarai