Connect with us

BIDIYO

AREWA HIP-HOP: Gadon Sana’a Na Yi A Wurin Mahaifina -Nomisgee

Published

on


Shahararren mawakin Hausa na hiphop, AMINU ABBA RINGIM wanda a ka fi sani da NOMISGEE, fitataccen mawaki ne wanda ya yi shuhura a gabatar da shirinsa na Hiphop a gidan talabijin na Arewa24. Wakilinmu, UMAR MUHSIN CIROMA ya samu tattaunawa da shi. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

 

Da farko dai masu karatun mu zasu so susan cikkaken sunanka?

To, assalamu alaikum da farko dai cikkaken sunana Aminu Abba Umar Ringim, don ma haifina dan Jigawa ne a garin Ringim, maihaifiyata kuma ’yar Rano da ke jihar Kano ce. Ka ga kenan Ina Kano kuma Ina Jigawa.

 

Ko za mu iya sanin kadan daga cikin tarihin rayuwar ka?

Toh zan ce kadan daga cikin tarihi na dai na farko ni haifaffen Kano ne kuma girman Kano a Kano kuma na yi makarantar sakandare, daga nan na tafi jami’ar Bayero da ke Kano a nan nayi digiri a Mass Communication. Na zo na fara hidimar kasa a garin Fatakwal. Na dawo Kano, amma saboda harkoki na irin na entertainment na zo na karasa hidimar kasar a garin Kano. Ka ga kadan kenan da cikin tarihina.

Sannan kuma Ina cikin harkoki irin na entertainment akalla yanzu na kai shekara 17, don sanda na fara waka Ina ga a Kano Studio daya ne don ba zan manta ba na fara yin wasu abubuwa a Zoo Road, kuma a lokacin na kan yi waka ne da Turanci. Kenan so ka ga yadda tafiyata ta taso kenan.

Sai kuma lokacin da muka fara muna ta dan dai yawace-yawace, saboda kasan dai nomisgee mutun ne mai tafiye tafiye, saboda kasan ance tafiya mabudin ilmi ba ma a arewacin Najeriya ba kadai na zauna a kudu na zauna Lagas Porthacout na zauna agaruruwa da dama, sai yasa mutane da dama suke gani kamar niba bahaushe bane, saboda suna ganin yanayin shiga na da waye wana, lallai na samu nayi yawace yawace, haka ma kasashen duniya da dama, kuma dukkansu ana zuwa dan neman na kai da kara sanin wasu abubuwa da suka shafi entertainment, wani lokutan kuma waka ke kaini da in je in yi wasa in dawo.

Sai kuma daga baya Ina gani shekara 18 da su ka wuce, da ba a arewa 24 na fara aikin tb ba, na farko dai ita kanta aikin jarida gadanta nayi saboda mahaifina dan jarida ne kuma sananne danko kaima ina ganin zaka san Abba Umar Ringim, kusan su ne mutane na farko da suka fara aiki a gidan rediyo na Kaduna kuma ya yi yawace-yawace gidajen rediyo Katsina da dai sauran garuruwa har kuma ya dawo Kano garinsa sai da aka ba Jigawa jaha sannan ya koma can, dan kaga ringim a cikin jigawa take so kaga na fara aiki ne a Dstb, dan wajen shekara takwas da suka wuce na fara H Hip Hop a dstb amma a can ana kiranshi da Africa Hip hop magic Hausa, akalla na kai shekara daya ina bada aikina ana kallo, sai daga baya arewa 24 tazo, suka dauke ni aiki, daga nan kuma na fara shege da fece don in zakulo mawakan Arewa da su ke da talent in nuna su idon duniya a san su a gan su a duniya.

 

To, me yaja hankalinka ka tsinduma harkan waka?

Shi komai da ka gani baiwa ne dan tin ina karami yaro nake da wannan abun kuma yayyena dikansu na koyi wasu abubuwa daga wajensu, sanan akwai wadansu mutane dana zauna dasu sunyi nisa a harkan rediyo a Kano, na farko akwai su Muhammad Tahir MC wanda ya rike dala fm sannan kuma akwai irinsu Muhammad Jolie, irin su Ahmed don tin ina karami na koyi abubuwa da dama a wajensu so kaga akwai ra’ayi kenan.

 

Kawo yanzu ka na da wakoki kamar nawa?

Gaskiya yanzu ban san yawan wakokin da na ke da suba domin su na da yawa don akwai na Turanci zalla amma yanzu na Hausa sun fi yawa wato na Hausa hip hop, tunda mu na jan hankalin mutane su dawo shi ne, kwanan nan ma Ina da sabon aiki, amma sanannun cikin su da su ka yi fice su ka karbi ‘award’ akwai kamar su duniya ina zamu je tasamu lambar yabo da dama har da kasashen waje akwai su feeling, da su geto, akwai kuma an cukule, an cukule ta nuna cewa Nijeriya gaskiya fuskar kuwa a cukule take ba’a jindadi, sannan akwai young Alhaji wanda bidiyon ta zai fito kwanan nan da kuma subani 2 fingers da dai sauransu.

 

Kuma ka ce a shekarun baya ka kan yi waka ne da Turanci kawai, ko za mu iya sanin mai ya ja hankalinka ka koma Hausa hiphop?

Haka ne a shekarun baya na kanyi waka ne kawai da Turanci, dalili kuwa kowa a lokacin yana kokarin yaga yayi koyi ne da irinsu ingila amerika da dai sauransu, daga baya kuma munzo mun fahimci cewa yanzu ko ina a duniya kowa da yaranshi yakeyi, in kace Saudiya da Larabci su ke yi Faransawa da faranshi su ke yi dai sauransu, haka kuma ko lagos abun dayasa suma suka zama jag aba a Nijeriya saboda suma suna saka yare suna saka pingin, sai yasa mu muka dawo muka dage sai ansan Hausa hip hop, mu ta daga matasa, yanzu gashi ta fashe ko ina maganar Hausa hip hop ake.

 

Wasu irin darussa wakarka duniya ina za mu je ta ke koyarwa?

Darussan da duniya in zamuje take koyarwa suna da dama musamman in ka lli halin da duniya take ciki a yanzu ana jubar jinni mara misali ana ta kashe kashe ta ko ina, wasu mugayan abubuwa suna ta bulluwa wa’inda bamu san ta ina suke ba, amm kuma in ka zauna da idon basira zaka ga wasu ne a can gefe suke haddasa fitinu burinsu kawai suka a zubar da jini, to abinda wakar take koyar shine sai mun ajiye maganar addini mun bar batun cewa kai musulmine koko kai kirista ne mun hada kai to sannan ne zamu zauna lafiya, sanin kuma ina kara wayar da kan ‘yan arewa mu dai na ganin da kawo mana kowani kalan al’adu mu dauka, dan wasu zaka ga sun saka riga mai rubutu sunyi gayu dashi basu san me rubutu yake nufi ba, sai ka duba zaka ga baa bun daya dace ka dinga adune dashi ba, kaga sai yasa ita wakar duniya ina zamuje kaga har America a Washington Dc an zauna ana tattaunawa akan wakar kenan, sannan in ka kalli bidiyo zaka ga al’majiri ne da wasu abu buwan ana nuna fa cewa a tashe hankalin duniya yake, da kudin daza mu dinga kasha wa a banza mu taimaka ma almajiran nan, in ba haka sune suke girma su zama ‘yan ta’adda su futine Duniya.

Kuma a dalilin duniya ina zamuje naje gurare da dama, na samu lambar yabo akan wakar akalla kamar guda biyar kuma kwanan nan a dalilin wannan wakar aka mun PEACE Ambassador wanda akayi a yobe NGO da dama sun halarci wannan taron, YEF wani Entertainment kamfani da hadin gwiwar NGO da sauransu suka bani wani lambar yabon PEACE ambassador.

 

Ko za ka iya gaya ma na wasu daga cikin lambobin yabon da ka samu daga lokacin da ka fara waka zuwa yanzu?

Lambar yabo da na samu su na da yawa gaskiya da kusan ko wata shekara za ka ga na samu best Hip Hop artist a arewacin Nijieriya wanda Kamfanin MTN suke shiryawa AMMA kannywood Award na kuma ci best rapper Album of the Year, haka kuma zalika na karbi kyautar lambar yabo a nijar na amsa Best program Of Year wanda ni nake gabatarwa na biciken masu fasaha a duniya, na kuma zo na karbi Talent Hunter, Alhamdulillah na karbi kyaututtuka da dama, ko a karshen shekaran da muka fita na karbi best rapper of the wanda Sarauniya Beauty Pergent ta kaddamar a Kaduna.

 

Wakarka da kayi a Ghetto Area wakace da ta samu karbuwa soasai a idon duniya, musamman a nan yankin area. ko itama zaka iya gaya mana darussan da take koyarwa?

Darussan da wakar Ghetto Area take koyarwa, kasan ghetto unguwa ne da talakawa suke zaune da yare da mutane iri iri ba aiki ga dai sunan, rayuwar ta fita daban, amma fa cikin wannan unguwar ta ghetto akwai masu basira akwai masu ilmi suna bukatar gudun mawa ne kawai suma su daga su zama wani abu a duniya, so abun da ita wakar ghetto star take nuna wa kenan a taimaki ‘yan ghetto sai yasa zaka ji ina cewa a kwai masu zaman bakinciki, a ghetto mata suke ta bamu lobing a ghetto police suke ta bamu hating, sai dai in ka saurarin wakar zaka gane gaskiya gayu suna jin jiki, gashi suna da ilmi ga kwakwalwa amma basu samun taimako.

 

Sananne ne kai a harkar waka kuma ka na aiki a gidan talabijin na Arewa 24. Ya ka ke iya hada aikinka da harkar waka?

Kowanne aikinsa daban lokacin da ake aikin gidan tb daban lokacin da ake waka daban, amma kuma wakar ita ke kara haskaka gidan tbn asanshi a duniya saboda haka dik inda ka sani mutun yana da baiwar waka kuma yana aikin gida tb rikeshi ake hannu biyu saboda yan bawa gidan tbn gudunmawa ta wannan hanyoyin inda yake saida gidan tb da sauransu da hakan lokacin kowanne daban in naje weekend ina samun hutu, ko kuma dik garin dana je aiki kamar legas da jos in inaso nayi wakana nakanje studio ko da daddare in wakana shi yasa kaga lokacina kankani ne.

 

Wani irin kalubale ka fuskanta daga lokacin da ka fara waka?

Toh gaskiya ni ban samu wani kalubale ba, saboda kalubale babba shine in kana yin abun da iyayenka basa so da haka kaga wannan akwai damuwa, toni ban samu ba a wannan bangaren saboda haka ina kalubalen kawai da na samuina makaranta ina waka wannan kaga kalubale ne, sai kuma bangaren kudi saboda ni tun farko ina aiki, don a wannan lokacin nayi aiki da AA Rano a gidan manshi na farko, don dan uwane a guna, na zauna a matsayin mataimakin manaja nike kula da fannin kudin, to kaga tun alokacin ina da kudi ina zuwa makaranta.

 

Wane irin kokari ka ke yi don ganin ka faranta ma masoyanka rai?

Ta inda nake faranta ma magoya baya rai irin su facebook instagram twiiter da dai sauransu akwai fans Page dina na duba musamman da daddare in amsa masu tambayoyin da zan iya amsawa masu bukata in biya wanda zan iya wanda ban iya ban a basu hakuri,wani lokutan in kabi ta irin masoya ma sai ranka ya baci kalan tambayan da zai ma sai ya bata ma rai, amma haka muke lallaba a rabu lafiya, amma ina iya bakin kokarina na faran ta ma masoya rai a hanyar zada zumunta.

Tin kaga masoya a fain duniya sub a wai kano ba nijeriya tin inda kasani, gasu nandai indiya ne amerika jamani da dai sauransu, haka kuma a tb ina mika godiyana ga masoyan da suke nuna mun kauna.

 

Daga yanzu zuwa nan da shekara biyar wane hidima ka ke shirin yima Arewa Hiphop?

Daga zuwa nan da shekara ashirin kana tinanin wani irin hidima zamu ba hip hop, toh zan iya cewa ko yazu ma Alhamdulillah, dan bana jin jama’a sun san da Hausa hip hop sai da nomisgee ya fara haska Hausa hip hop a idon duniya baki daya san nan aka santa, kuma anan ne muke kokarin a san bahaushe da Hausa ita kanta aduniya, akwai kalubale dana samu da dama Alhamdulillah saboda in kana da stardom sai ka zama wani abu ake maganarka amma in baka wani wa baza ayi maganarka ba, amma kalubalen da na samu musamman a gurin malamai sun cewa nomisgee yana canja al’umma, amma ni a tinanina basu da sani ne akan wannan abun shine yasa, kuma in ana haka a hankula zaka ga sun gane fa’idar wannan abun, amma fa daga nan zuwa nan da shekara biyar inaso in sa kana gida kana wurin sana’ar ka a matsayin mawaki kana samun kudi a account dinka da ta online, san kuma a ta hanyar waka ne muke so muwayar da kan al’umma a samu zama lafiya matasa su samu aikin yi to kaga abun da muke so mu samar ma hip hop nan da shekara biyar.

Zamu Cigaba A Mako Mai Zuwa..


Advertisement
Click to comment

labarai